← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 84

Sashe 76

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhamdilillah, Hafsa ta É—an farfaÉ—o ba kamar lokacin da aka kaita Asibiti ba, an samu jinin ya É—an sauka.
Likita yayi ta mata nasiha, da rarrashinta a kan ata kwantar da hankalinta, ta miƙa lamuranta ga Allah, sannan ya sallamesu.
Kusan duk kuɗin hannunsu ya ƙare, saboda zaman Asibiti, ga babu kayan Abinci. Hafsa ta ɗan ji daɗin jikinta, sai dai ta kasa mantawa da batun Khalil, babu abin da ya canza daga soyayyar da take yiwa Khalil ɗin.
Kayan da Khalil ya bata ta tattara ta bashi bai karɓa ba,  a soron gidansu ya bar mata, dama tunu ta cire layin wayarta daga wayar da ya bata zuwa tsohuwar tata.
Da suka dawo gida ta duba wayar, sai ta ga missed calls É—in Khalil rututu a ciki, da tarin messages, ba dan ta so ba haka ta saka lambar Khalil a blacklist, tana jin kamar da zuciyarta ta haÉ—a ta saka a black list É—in.

Bayan Amina ta gama koke kokenta, kuma sai ta fara tunanin akan abin da ta yiwa Daddy, sai taga kamar bata kyauta ba, saboda ya kyautata mata har ƙarawa Baba albashi yayi ba tare da ko matar gidan ta sani ba, ita ma Baba da ya gaya mata ya gargaɗeta a kan kar wanda ta gayawa, dan Alhaji Ahmad ya ce masa ko Aminan kar ya gayawa, banda kyautatawa da yake mata a kai a kai da ƙoƙarin bata kariya a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin cin mutuncinta, gaba ɗaya kuma sai jikinta yayi sanyi.

Da magariba Hafsa na zaune, ta saka tuwon da Mama ta zuba mata, amma ta kasa ci, Mama sai hira take yi mata dan ta É—ebe mata kewa.
Wayar Hafsa ce ta kawo haske alamar kira ya shigo, kasancewar wayar a silent take, Mama ta ɗauko wayar ta miƙawa Hafsa.
Hafsa ta girgiza kai ta ce "Mama ƙyale wayar nan kawai"

"A'a ai ba a yi haka ba" Mama ta É—aga wayar tare da yin sallama.

"Wa'alaikum salam, Mama ina wuni?"
Mama ta kalli Hafsa jin muryar Khalil.

"Lafiya lau Khalil, ya aiki?" Waro ido Hafsa ta yi jin Mama ta ambaci Khalil.

"Aiki lafiya lau Mama, ina ta kiran Hafsa a waya bata É—agawa, daga baya ma wayar bata shiga"

Mama ta ce "Ai da yake ta É—an yi rashin lafiya ne, É—azu muka dawo daga Asibiti"

Cikin damuwa Khalil ya ce "Subhanallah, ya jikin nata?"

"Taji sauƙi Alhamdilillah, bari in bata wayar" Mama ta miƙawa Hafsa wayar, ta tashi ta bar ɗakin.

Hafsa ta kalli sabuwar lambar, sannan ta saka wayar a kunnenta.

"Assalamu alaikum, Hafsat"

"Na'am" ta amsa a sanyaye.

"Hafsa why? Meyasa laifin Mummy zai shafeni, ko mun rabu ai bai kamata ki yanke duk wata alaƙa da ni ba" Hafsa tayi shiri ba ta ce masa komai ba, sai ma jin kewarsa na damunta.

"Hafsa kiyi magana mana"

"To me zance?"

"Shikenan, Yanzu ya jikin naki?"

"Naji sauƙi"

"Allah ya baki lafiya, gaba ɗaya ina cikin damuwa ko aiki na kasa yi, na kira ba kya ɗagawa daga baya ta daina shiga, sai sabon layi na saya na saka na kira sannan kika ɗaga, dan Allah Hafsa kiyi haƙuri abin da Mummy ta yi miki ya wuce, ina ta ƙoƙarin saita komai, in Allah ya yarda za mu yi Aure"

Hafsa ta lumshe idanunta sannan ta buÉ—esu ta ce "Khalil"

"Na'am Hafsa"

"Duk abin da iyaye ba sa so aka aikata shi baya albarka, baya zuwa ko ina, dan Allah Khalil kayi haƙuri ka ƙyaleni, dole mu haƙura da juna"

Khalil ya maraice ya ce "Dan Allah Hafsa...

"Shhhhhh" ta katse shi.

"Ko Mama ce ta ce na rabu da kai, idan har bata son alƙarmu zan rabu da kai har abada, Yakamata mu yiwa Mummy biyayya, dan Allah Khalil kar ka sake kirana, kayi haƙuri"

"To ki tsaya kiji" ba ta jira mai zaice ba, ta kashea wayar, ta cire layin gaba É—aya daga kan wayar.

Ta haɗe kai da gwiwa tana ta ƙoƙarin mayar da hawaywnta amma ta kasa.

Mama tayi sallama ta shigo É—akin, ta zauna ta ce "Yaya kiran me yake miki?"

"Haƙuri yake bani, wai mu koma kamar da"

Mama ta girgiza kai ta ce "Ai hakan ba zai yiwu ba, tun da mahaifiyarsa bata so, Allah ya haÉ—a kowa da rabonsa na alkhairi"

"Ameen" Hafsa ta amsa jiki a sanyaye.

Khalil kuwa sakin wayar yayi a ƙasa, sai a Yanzu yaji wasu irin lafiyayyun hawaye suna zubo masa, bai taɓa zaton zai iya kuka a kan mace ba, babban abin da yasa yake jin zai iya taking kowane risk saboda Hafsa shi ne ya sani ba kowane namiji ne zai iya karɓar Hafsa da ƙaddararta ba, gashi so yake mata na fisabilillahi, ji yake a duniya banda uwar da ta haifeta babu wanda ya kai shi ya sonta da ƙaunarta.

Daddare Amina zata kwanta bacci, ta dinga kallon wayarta, da sukan yi chatting da Daddy da daddare kafin tayi bacci, tayi ta masa shirme da shirirta yana biyeta. Sai dai yau ko saƙo ɗaya bai turo mata ba, ta duba what's app taga yana online.
Sallama tayi masa, sai dai ya buÉ—e ya gani amma ya share, ga zauna shiru shiru amma bai mata reply ba.
Ajiye wayar tayi cike da damuwa, tana sake ganin rashin kyautuwar abin da ta aikata wa Daddyn.

Kwanaki biyu kenan, babu wanda ya nemi wani tsakanin Fadila da Yazid, a kwana na uku kuwa bai zo makarantar ba gaba É—aya, gashi ana ta shirye shirye na fara exams, ana fa teses baya nan, abu kamar wasa har aka tafi kwana na uku baya zuwa makaranta, gashi shi ba wani aboki ne da shi ba, balle ta tambaya.

"To ma ina ruwana da rashin zuwansa' ta tambayi kanta, ta cigaba da ƙoƙarin mantar da kanta batun Yazid.

Amina kuwa nadamar abinda ta aikata ya addabeta ya hanata sukuni, ta kai ta kawo, idan taga Daddy ta gaishe shi, sai dai ya amsa sama-sama, alamar fushi yake da ita.
Gashi ta rasa hanyar da zata bi wurin bashi haƙuri. Ranar asabar da safe, tana gyarawa Hajiya Zainab falo, ya shigo falon, Amina ta risuna ta gaishe shi.
"Lafiya lau" ya amsa. Ya wuceta ya nufi bedroom É—in Hajiya Zainab.

A tsaye ya tarar da Hajiya Zainab, ta sanya skirt É—in lace, tana kwalliya a gaban mudubi, ba ta saka rigar ba tukuna.
Ya ɗan ƙare mata kallo sannan ya nufi in da take yana faɗin "Bainu ba kya tsufa"

Ta ce "Hmm, ka fito kenan, ya ka kwana da jikin?"

"Ba zan amsa ba, tun da baki kwana da ni ba, duk da kin san jikina babu daÉ—i".

Hajiya Zainab ta waiwayo ta kalleshi ta ce "Sai kace wani ƙaramin yaro, da ban kwana da kai ɗinba, ba ga ka nan ras da kai ba, jikin yayi sauƙi".

Ya ƙarasa bayanta ya tsaya, ya rungumeta ta baya, ya zagaya hannayensa a cikinta, tare da kwantar da kansa a kan kafaɗarta ya ce "Ko ba komai kasancewarki a kusa dani, zai sa naji daɗi"

Ɗan ƙoƙarin ture hannunsa take ta ce "Kaima dai, ba magungunaka suna nan ba, ka sha ka kwanta kayi bacci, ko kaje Asibiti mana"

"Duk ba wannan nake buƙata ba, ke ɗin dai, attention ɗinki, kulawarki da hirarki domin ɗebe mini kewa, musamman na ɗauki hutun shekara saboda in kasance da ku, duba da yanayin aikin ina daɗewa bama tare amma duk kinfi mayar da hankali a kan 'ya'yanki, business ɗinki da sauransu, ni ba kya kulawa da ni sosai, ina buƙatar kulawa nima" yayi maganar yana cigaba da ƙanƙameta yana shaƙar ƙamshin man da ta shafa.

Ɗan tsuke fuska ta yi ta ce "Ahmad meye haka ne? Dan Allah Yakamata ka san yanzu ba da bace bafa, mun girma fa yanzu,da auren wuri muke yiwa yaranmu da yanzu muna da jikoki, yanzu jikinmu hutu yake buƙata ba wannan abin ba,  abin da aka yi a baya Allah ya amfana".

Alhaji Ahmad ya sake ƙasa da muryarsa ya ce "Am not old for that, ban san me kike nufi da ni ba, ban yi girman da na wuce samun kulawa da tatali daga iyalina ba, Please kar muyi haka da ke"

"Kaga dan Allah ka rabu da ni, unguwa zan fita ni"

"Unguwa ƙarfe goma na safe, ke kenan kullum cikin fita da wadda na amince, da wadda ban amince ba? Dan Allah ki zauna a gida mu wuni tare yau"

"A'a wallahi, fita ta tana da muhimmanci sosai, zan zaga shaguna na, daga nan zanje biki, classmate ɗinmu na auran 'ya" ta zame daga jikinsa tana ƙoƙarin ɗaukar rigar kayanta ta saka.

"Haba Zee, shikenan let's have some fun before you go" yayi maganar yana kuma ƙoƙarin rungumota.

Cikin tsawa ta ce "Wai meye haka ne, na ce maka bana so, dan Allah wai sai yaushe zaka girma, you don pass this level, haba dan Allah"

Lumshe idanunsa yayi, ransa a ɓace, ya kalleta da idanunsa suka fara sauya launi, "Zainab, ki bini a hankali tura ta kai bango"

"Da tura ta kai bango, saika rushe bangon ai, shikenan shekara da shekaru ana abu É—aya, shekaru sun ja ma amma mutum bai san ya girma ba"
Daddy bai kuma ce mata uffan ba, ya juya ya fice.

Amina tana mopping a babban falo ya fito, kallo É—aya tayi masa ta fuskanci akwai damuwa, amma bata da ikon magana, haka ya koma nasa sashin.

Babu daɗewa Hajiya Zainab ma ta fito, ta sha uban ado sai ƙamshi take, hannunta riƙe da mukullin mota, sai yatsuna fuska take ta dubi Amina da take ƙarasa mopping ta ce "Idan an tashi girkin rana, ba sai an yi da ni ba,  dinner ayi abinci mara nauyi"

Amina ta ɗan basar ta ce "Shikenan" dan a duniya idan da mutumin da ta tsana bai wuce Hajiya Zainab ba, saboda rashin mutunci da wulaƙancinta.
Chapter 76 · 0% Book details