← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 84

Sashe 65

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zage shi nayi tsaf, amma banga alamar zai saduda ba, bina yake kuma yi, wai zai yi mini bayani, na rasa mema yakamata in yi"

Turai ta ce "Ke, ta bayan gida zaki ɓullowa lamarin, Khalil dai ɗanmu ne, ba zaki cigaba da zuba masa ido ba a mallake miki shi a banza ba"

Mummy ta tari numfashinta ta hanyar cewa "Kamar kin san har da maganar tayi masa girki ya ci naji, gaba ɗaya jiya da ƙyar nayi bacci wallahi"

Hajiya Salma ta ce "Kut kinga Zainab bamu ga ta zama ba, ba mun san in da yarinyar take ba, ai mu muka ganota a hanyar zuwa plaza, zuwa za muyi mu kasa mata warning, ko nemi gidansu muje har gidan nasu mu samu uwarta, mu musu wankin babban bargo, idan suna da zuciya zasu rabu da shi, kinga ko ya ƙi Allah ya haƙura"

Mummy ta ce "Amma kamar ƙasƙanci ne, mu wanke ƙafa mu tafi gidan talakawa yawon yi musu warning, gaskiya Khalil ya gama da ni, wai 'yar masu awara a kan kwalta, wannan yaro duk matan garin nan"

Hajiya Salma ta ce "Meye wani ƙasƙanci, biyan buƙata ai yafi dogon buri, da su mallake shi fa, da munyi nasarar raba su, ki nemo masa mata ya aura"

Mummy ta ce "Haka za ayi, bari ƙarfe huɗu bayan sallar la'asar, mu haɗu ku rakani muje"

Turai ya ce "Allah ya kaimu yammar" suka amsa da Amin.

Ganin yau ƙarfe goma babu malamin da ya shigo, ya sanya Fadila tafiya Library, dan Captain ya sanar da cewa malamin ba zai samu shigowa ba, kuma ga exams na gabatowa.
Ta nutsu sosai ta mayar da hankalinta kan littafin da ke gabanta, ba zato ba tsammani taji an ja kujerar da take ta baya, kamar zata faɗi, a razane ta ƙwala wani marayan ihu, saboda ta tsorata sosai da sosai.
Sai da hankalin wasu daga cikin tsirarun ɗaliban da ke cikin libraryn ya dawo kansu, bai saki kujerar ba, ya leƙo fuskarta ta sama yana kallonta yana murmushi.
Ta marairaice kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah ka sauke kujerar nan kar in faÉ—i"

"Ba zan bari ki faÉ—o ba ai".

"Dan Allah ka ajiye kujerar, bana so"

"Haka kike shagwaɓaɓiya, faɗi sunana sai in saki kujerar"

"Dan Allah ka bari, zan faÉ—o fa"

Sake matso da fuskarsa yayi saitin tata ya ce "Sai kin ce Yazid tukuna"

"To ajiyeni sai in faÉ—a"

"Ni zaki yiwa wayo yarinya, faɗi ko in kai ki ƙasa a kan kujerar" yayi maganar yana sake jan kujerar baya.

"Wayyo Allah Daddy, Yazid na faÉ—a ka ajiyeni dan Allah"

"Wow, sake maimaitawa in ji"

"Dan Allah ka bari" tayi maganar tana rirriƙe hannunsa, jin yadda yake kuma baya da kujerar.

"Kar ki saka mutane su juyo suna kallonmu, ke zasu gane ni na da mask a fuskata, sake faÉ—a"

A hankali ta ce "Ai na faÉ—a"

"Ki ka ce me?"

"Yazid"

"To daga yau, kar ki sake zuwa ki tsaya a kaina, cikin tsiwa kina wani cewa Ustaz"

"To naji, ajiye ni"

Zuba mata ido yayi, yana kallon bakinta, yadda take motsashi a hankali cikin tsoro.
A hankali ya mayar da kujerar yadda take.
Dafe ƙirji tayi tana sauke ajiyar zuciya, saboda yadda ta tsorata.
Kujerar gabanta ya ja ya zauna, yana kashe mata ido. Wata uwar harara ta watsa masa.
"Da kika samu na saukeki shine ki ke hararata ko" wata harar ta kuma watsa masa tana ta sauke ajiyar zuciya.
Jan littafin gabata yayi ya ce "Kawo mu gani, me kike karantawa"

Janye littafin tayi ta ce "Ina ruwanka da abin da nake karantawa".

"Hmm babu ruwana, me kika ce zan koya miki jiya?"

Cikin tsiwa ta ce "Ai na ce maka na fasa, bana son koyarwar taka"

"Aikuwa karki nuna kin sanni a exam hall"

Hararsa tayi ta saka takalmanta zata tashi.

Ya ce "Haba Besty, zauna muyi karatun mana, tun da kika shigo school É—in nan nake biye da ke, kika je wurin Yusra, ki ka koma Aji, sannan ki taho nan"

"Wallahi ka takura mini"

Yazid yayi murmushi ya ce "To ya zan yi tun da bani da abokai, ana abota da ni ne saboda abin a za a mora wurina na karatu, ni kuma nafi son ayi abota da ni saboda Allah"

"To ni ina ruwana da wannan bayanan naka?"

ÆŠan tsura mata idanu yayi yana nazartar yanayinta, a hankali ya furta "Happy birthday in advance"

Waro idanunta tayi tana kallonsa, "Waye ya gaya maka birthday na?"

Murmushi ya yi ya ce "Password É—inki na System da kika saka na gane date of birth É—inki, gobe in Allah ya kaimu shekarunki Ashirin da biyu, Happy birthday 'yar yarinya".

Fadila ta ce "Allah ya hore maka saka ido, da bin ƙwaƙwƙwafi, kai dama ɗan sanda ka zama"

Yayi murmushi ya ciro leda a aljihunsa, cikin fargaba ya miƙa mata.

"Meye wannan?"

A ɗan sanyaye ya ce "Karɓi ki gani, sai dai ban sani ba, ko kina karɓar abin da ya fito daga hannun talaka kamar ni ba, first gift as a brother, and at the same time friend"

Ɗan taɓe baki tayi, ta karɓi ledar ta buɗe, ta fara ciro abin da yake ciki, turaren lailatul sahara da Bushra, da kuma wani abun hannu da zobensa, da gani dai ba mai tsada bane, amma taji kyautar ta kama zuciyarta.
ÆŠan murmushi ta yi ta ce "Kai ka mini kyauta ta farko wannan birthday, na gode sosai"

"Da gaske Kin karɓi kyautar da nayi miki?x yayi Maganar da mamaki, dan bai taɓa zaton zata karɓa ba.

Tayi murmushi ta ce "Gashi kuwa kana gani" ta ɓalle abin hannun ta saka, ta zura zoben.

Ta ce "Na karɓi abin hannun Ustazu" tayi maganar tana dariya, tana kallon hannunta.
Yazid yayi mata ƙuri da ido, yana kallon yadda take murmushi, da yake matuƙar burge shi, sai dai ya san cewa abu ne mawuyaci idan ya bayyana mata haƙiƙanin abin da yake zuciyarsa ta yarda da shi ba. Yanzun ma ya aka cika, shirin nasu baya ɗaukan lokaci, suke ɓatawa.

"Ya ka zuba mini ido ne?" Ta miƙa masa greeting card ɗin da yake cikin ledar, wanda rubutun larabci ne a jiki ta ce "Fassara mini wannan"

Ya kalleta ya ce 'Ki karanta mana"

"Amma dai ka san ban iya ba"

"Birthday wishes ne kawai" ta ce ok

Ta jujjuya katin tana kallon adon da ke jikins, ta ɗago ido, taga yadda ya ƙureta da ido.

"Wai kallon me kake mini ne?

"Ba komai, lokacin salla yayi, muje muyi salla" ta jinjina kai ta miƙe, ta ɗau jakarta, da ledar da ya bata suka fita daga libraryn.

Da yamma Fadila ta dawo gida, tana dawowa ta shiga falo ta watsar da jakarta a falo kamar yadda ta saba, ta shilla É—akinta da gudu, saboda fitsarin da ya matseta.
Daidai lokacin Mummy ta fito cikin shiri, zata je ta É—auki su Hajiya Turai.
Jakar Fadila da ta gani yashe a tsakar É—akin ne ya sanya ta gane Fadilan ta dawo gida.
Miƙa hannu tayi zata ɗaukewa Fadilan jakarta, taga leda a ƙasa. Ta ɗau ledar ta buɗe, sai taga turare guda biyu da kati a ciki.

Sansana turaren tayi tana yamutsa fuska, tamkar wadda ta shaƙi warin bola.
Fadila ta fito daga ɗakinta, dan zuwa ɗakin Mummy, amma taga Mummyn tsaye hannunta riƙe da ledar da Yazid ya bata.

"Mummy fita zaki ne?"

"Eh fita zan yi, me kike da wannan a jakarki?" Ta nunawa Fadila turarukan tana yatsune hanci.

"Bani aka yi" Fadila ta bata amsa.

"Waye ya baki wannan tarkacen, turare kamar na 'yan bori"

Fadila ta miƙa hannu ta karɓa tare da faɗin "Wallahi turarukan da ƙamshi, wani ne ya bani"

"Waye wani?"

"Wani É—an ajinmu ne?"

"Meye haɗinki da shi da zai baki wannan tarkacen ki karɓa?"

"Bani da wani haÉ—i da shi, muna mutunci ne kawai, and i can't reject it, ba zai ji daÉ—i ba, kuma bani kaÉ—ai ya bawa ba"

"Shikenan, kar dai ki sake ki shafa wannan turarukan ki shiga jama'a, kowa yaji wannan turaren ya san mai arha ne, wani wari suke kamar na ciyawa, ni zan É—an fita zan je wata unguwa"

"Ok Mummy, safe journey"

"Thank you" ta amsata ta fice.

Alhaji Ahmad bai tura ɗan aike ba, shi da kansa ya je makarantar ya ɗauko Amina, suna tafe suna hira, ya ajiyeta a ƙofar gida ya shiga da motar ciki, dan ko Baba bai san tare suka dawo ba.

Gaba ɗaya hankalin Hafsa yana kan mutanen da take sallama, tana yi tana iza wutar awararta. Wata danƙareriyar mota ce ƙirar Highlander tayi parking a gefen inda Hafsa take. Sam hankalinta baya kan abin da yake wakana wajen abin da yake gabanta.

"Ke!" Taji an yi shouting a kanta.

Cikin É—abi'arta ta ta miskilanci, ko É—aga kanta ba ta yi ba, ta cigaba da sallamar mutane, dan ba ta kawo ma da ita ake ba, saboda yanayin yadda aka yi maganar cikin isa da gadara.

"Ke da ke nake magana, nayi magana kika mini banaza" Jin an dunguri kanta ne ya sanya ta É—aga kai, ta kalli Hajiya Turai dak zazzaro mata ido, amma ba ta ce uffan ba.

"Wai ba da ke nake ba? Ko bayan talauci kuma naksashiya ce ba kya ji ne?" Cewar Hajiya Salma.

Kamar ba za tayi Magana ba kuma sai ta ce "Me nayi miki ne?" Tayi maganar cikin rauni.

"Uwarki ki ka yi mini? Ina magana kina jina dan iskanci kika shareni?"

"Uwata ta gode" Hafsa ta sunkuyar da kai, tana fifita wuta.

Saboda rashin girma, da iya duniyanci, Hajiya Turai ta saka ƙafa tayi fatali da awarar da Hafsa ta riga ta tsame, ta kuma yi ball da wadda take cikin bokiti tana soyawa.

A gigice Hafsa ta miƙe tsaye ta kallesu "Baiwar lafiya,me nayi miki zaki zo wurin san'ata kina watsar mini da kaya? Ni ban sanku ba ban taɓa ganinku ba balle in ce ko wani laifin nayi muku"
Chapter 65 · 0% Book details