Sashe 46
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haba Hafsa, Wallahi ba haka bane, labarinki ya tsma zuciyata to the extent tun da na bar wurinki bani da lafiya, sai yau na samu sauƙi. Ina da ƙanwa mace, mai rawar kan tsiya da tsiwa, sai dai idan makamanciyar ƙaddara irin taki ta sameta wani ya muzanta ta yaƙi aurenta, ko ya ce ƙarya ne abin da ya sameta bai mini adalci ba, Saboda na fi kowa sanin halinta, duk rashin jinta, tana da kamae mutuncinta, kwatankwacin yadda kike.
Meyasa zan ƙi dawowa gareki, dan wani abu da kika rasa a sanadin ƙaddara wanda ko ni ɗin ne na karɓe shi, iya na lokaci ɗaya ne, kyawawan ɗabi'unki da halayarki da su zan rayu tsawon rayuwata?.
Matasa da yawa bama yiwa kanmu adalci, wurin zubar da mutunci da ƙimarmu kan mallakar abin da Allah ya halarta mana na aure. Sai dai akwai tsautsayi da ƙaddara, abin da kika gaya mini na yarda ɗari bisa ɗari, kuma ni banji cewar zan iya rabuwa da ke saboda haka ba, ina son ki Hafsa, kuma ni aurenki zan yi, dan Allah ki daina wannan kukan"
"Dan Allah haryanzu kana sona?" Tayi maganar tana kallonsa.
Yayi mata murmushi ya ce "Ina sonki mana, kema kina sona?"
Murmushi take haÉ—e da hawaye ta ce "Na zata ba zaka dawo ba ka daina sona, shiyasa nayi ta kuka"
"Allah sarki Sweetheart É—ina, ni damuwa ce ta sani rashin lafiya, na kashe wayoyina, amma kina zuciyata am sorry for not hearing from me"
Hannayenta biyu ta haÉ—a a fuskarta ta cigaba da kuka.
"Babu ya isa haka mana, ki daina kukan nan mana"
"Kukan farinciki nake ka ƙyaleni"
Murmushi yayi ya ce "Dole ki kuka, Allah ya azurta ki da É—an shawalwalin saurayi kamata, É—an beauty da ni"
Murmushi tayi, duk da akwai hawaye kwance a fuskarta.
"Yanzu gaya mini, kina sona?"
"Sai nayi shawara" ta faɗa tana dariya, wadda ke ƙara mata kyau.
"Kin ma isa? Sai kin faÉ—a ai".
"Ina sonka Ibrahimul mu'azzam" ta faÉ—a tana kauda kanta gefe guda.
"Alhamdilillah, Masha Allah, bana jin ko Daddy da ya raɗa sunan nan, ya taɓa daɗi a bakinsa kamar yadda ya yi a naki bakin, Ibrahimul mu'azzam. Kai amma na sha gwagwarmaya kan in shawo kan wannan Japanese baeb ɗin"
"Nice Japaneese É—in kuma?"
"Eh mana, My Japanese doll"
murmushi suka yi gaba É—aya, Khalil ya dinga kwantar mata da hankali, da sake bata tabbacin iya wuya, zai aureta yana tare da soyayarta.
Suka kasance cikin nishaÉ—in da sai da ya wanke musu zukatansu daga dukkanin damuwowin da suke ciki.
Khalil ya nisa ya ce "Ina ga idan na sake dawowa, zan shigar da ƙarar dangin mahaifinki, in ɗaukar muku lawyer, a ƙwato muku hakkinku.
Hafsa ta girgiza kai ta ce "A'a, ni bana son duk wani abu da zai sake haɗamu da su, mun barwa Allah, wanda ya tara dukiyar ma yau yana ina? Allah ya karɓi abunsa, ni fatana Allah ya bamu mafita kawai"
"Allah sarki babyna, insha Allah very soon zan aureki, mu wuce wurin nan, sonake ai komai da komai a abinda bai wuce 6months ba"
Hafsa ta ce "Kai, yayi wuri da yawa ai".
"Ba wani wuri, amfanin soyayya aure, sai munyi aure za muyi soyayya ta gaske"
"Ni ban isa aure ba" ta faɗa a shagwaɓe.
"To ni na isa, ki bari idan muka yi auren, sai mu gani in dagaske baki isa auren ba" Jin Khalil zai ɓaro magana ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.
 Kayan ciye-ciye ya bata, tare da bata saƙon gaisuwar sa zuwa ga Mama, ya yi mata sallama ya tafi.
Ba kowa a falo, sai Daddy yana ta aiki a computer, Amina ta hango hasken lantarki a falo, ta fito falon da nufin ta kashe wutar, ta tarar da Alhaji Ahmad yana ta aiki a kan system.
Komawa tayi kitchen, ta yayyanka fruit ƙanana, ta ha ɗa cofee, ta ɗoro a plate ta fito falon.
"Daddy sannu da aiki"
Ya É—aga kai ya kalleta ya ce "Yauwa sannunki"
Ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a gabansa ta ce "Ga wannan naga kana ta aiki"
"Masha Allah, na gode sosai kuwa"
"Ba komai" ta juya zata koma ya ce "Yauwa, an kirani daga makarantarku É—azu, sun ce kije ranar Saturday"
"Ok Allah ya kaimu, zan je insha Allah"
"Good".
"Gobe in Allah ya kaimu ma da wuri zaka fita?"
Daddy ya ce "Eh da wuri zan fita muna seminar ne"
"Ok, to shikenan sai da safe"
Ta juya ta nufi in da É—akinta yake, ta ci karo da Hajara a tsaye tana binta da kallo.
Shareta Amina tayi ba tare da ta kula Hajara ba, ta wuce É—akinta tare da faÉ—in "Kema Allah zai mini maganinki"
RUƊIN ƘURUCIYA
https://arewabooks.com/chapter?id=6220844388e1ec3a041032a8
_*ƘURUCIYA: Ita ce mataki mafi hatsari da kowane ɗan Adam yake tsallakewa kan ya zama babban mutum me cikakken hankali. Sai dai wannan mataki da ɗan Adam ke tsallakewa shekaru ne masu hatsarin gaske, idan ya wuce su lafiya ana saka masa ran samun kyakywar rayuwa zuwa tsufa, idan kuwa aka samu tangarɗa rayuwa ta samu tawaya zuwa tsufa. SHIN KE UWA CE? SHIN KINA CIKIN WANNAN MATAKI NA ƘIRUCIYA HAR YANZU, KO KUWA KAI NAMIJI NE KANA DA 'YAN UWA MATA? Ya dace ki karanta wannan littafi. Rayuwar matasanmu a makarantun sakandare, hatsarin wasu al'adun bahaushe ga 'ya'yayensu mussaman mata, illar sangarta, Cutar depression, shaye-shayen matasan yara mussaman mata, dama abubuwa da baku yi zato ba, suna nan a cikin wannan littafi, ku garzaya manhajar Arewabooks don mallakar naku, ko ku kira wannan lambar don sayen naku a kan kuɗi ƙalilan 08081012143*_
Ayshercool.
08081012143
Ayshercool
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P22-23
Arewabooks Ayshercool7724
Amina ta shige ɗakinta, ta cigaba da saƙa da warwara a cikin ranta, daga bisani ta tashi ta hau gyaran kayanta, dan ba ta jin bacci sam, ita wannan hutun duk ya isheta so take ayi a koma makaranta.
 Kamar yadda Daddy ya gaya mata, ranar asabar ta shirya ta tafi makaranta, taje ta tarar Quiz ne aka yi musu, domin fitar da gwanayen da za'a tafi da su Abuja, wurin yin babban Quiz na ƙasa. Suka gabatar da quiz, da kuma mini exam da aka yi musu, wanda iyayensu suka je, suka karɓar musu results ɗinsu, Amina na ji tana gani, haka ta dawo gida ba a bata result ɗin ta ba, haka ta dawo gida duk ranta babu daɗi.
Khalil jinsa yake tamkar an masa bushara da wani abu na musamman, wata irin Soyayya da shaƙuwa ce suka shiga yi a tsakaninsa da Hafsa, a haka hutunsa ya ƙare, ya koma wurin aiki, cike da kewar Hafsa. Ya labartawa Abdul yadda yayi nasara, Hafsa ta karɓi soyayyarsa, Abdul ya taya shi murna sosai, sai dai a ransa yana tausayawa Khalil gwagwarmayar da zai sha da mahaifiyarsa kan ta amince.
Hutunsu Fadila ya ƙare, ji take tamkar ta ɗora hannu a ka tayi kuka, dan sam bata son stress da takurar makaranta.
Wannan semester da sabuwar mota dal ta koma school. Bayan ta ƙara kusan kwanaki uku a kan hutun nasu. Kwanaki ukun da ba ta zo ba, har an yi wasu lectures ɗin bata nan.
Haka kawai ta fara waige-waige a ajin, ko zata hango Yazid, amma sam ba ta ganshi ba, tana cikin tunanin ko shi ma bai dawo hutun bane, Kankiya ya shigo ajin. Yana shigowa ta haɗe rai, dan ko san ganinsa ba ta yi, tun da ta fara ganin zancen Yazid na daf da zama gaskiya, saboda yadda yake uzzura mata da saƙonni, da kuma kiran waya ba gaira babu dalili.
 Har kankiya yayi lectures ya gama yana satar kallon Fadila, da ba kowa ne ya san yana mata ba, sai ita ɗin da ya addabawa da ido.
Amina na zaune a gaban TV stand, tana gogews, aka turo ƙofar falo haɗi da sallama. Ta ɗaga kai tana amsa sallamar. Hajiya Turai ta gani a tsaye, ta gama ƙarewa Amina kallo daga sama har ƙasa, tana sanye da doguwar riga ta ɗaura ɗankwalin atamfar, kai ba ka ce 'yar aiki ba ce.
Ta ɗan taɓe baki ta ce "Hajiya Zainab na nan ne?"
Amina ta É—an kalleta ta ce "Eh tana nan, ki zauna yanzu zata fito".
Hajiya Turai za tayi magana, sai ga Hajiya Zainab ta fito cikin shiri, da alama fita za tayi.
"Hajiya Turai, har kin ƙaraso?".
"Eh, yanzu na shigo ashe ma kin shirya"
"Wallahi kuwa, ai na san ba kya son jira, bari muyi mu tafi" ta mayar da hankalinta kan Amina ta ce "Ki kula mini da gida da kyau, ki kammala girki da wuri, bana son Fadila ta dawo ba a gama girki ba".
"To insha Allah" Amina ta faÉ—a cikin girmamawa.
"Wai ni kuwa Zainab, haka kika bar Yarinyar nan tana miki yawo a gida, ga mijinki ga ɗanki, ba zata dinga saka hijjabi ba, naga wancan zuwan da muka yi da hijjabi a jikinta, tafa fara girma kalli ƙirjinta a cike fam, kalli ƙugunta"
Amina a ranta ta ce "Ji 'yar bala'i har ta ga ƙirjina, ta rasa in da zata kalla sai nan, wannan ai iskanci ne, tubarkallah".
Mummy tayi wata dariyar ƙeta ta ce "lallai Turai kin manta wacece Zainab ne, Ai Alhaji Ahmad na riga na zame masa teku, na sha kansa ba yadda ya iya da ni, gidan nan daga ni sai 'ya'yana, da can bai ƙara aure ba sai yanzu da girma ya kama shi, Khalil kuwa shima ya san bai isa ya kawo mini jinin babu cikin zuriyata ba"
Sukayi dariya tare da yin shewa suka fice. Kwaɓe baki Amina tayi, ta cigaba da aikinta a ranta ta ce "Ko ni me zanci da dattijo ma oho, in banda tsautsayi wa zai auri jinin wannan matar ko ya auri mijinta, bala'inta ya ishi mutum?'
ƙarshe dai Amina ta manta da batun Hajiya Zainab, ta fara tilawarta tana yi tana aikinta.
 Ta kammala goge gogenta, ta miƙe zata bar wurin, tayi ido huɗu da Alhaji Ahmad, da ke tsaye yana kallonta.
Shan jinin jikinta tayi kamar mara gaskiya, ta É—an diririce, dan sam ba ta zata yana gidan ba.
"Ina kwana" ta furta tana kauda kanta gefe.
Bai amsa mata ba ya ce "Kawon breakfast"