← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 84

Sashe 44

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsa ta rushe da wani irin kuka, jikinta har karkarwa yake yi, Khalil ya yi shiru, ya kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi.

Ayshercool
08081012143

RUƊIN ƘURUCIYA

https://arewabooks.com/chapter?id=6220844388e1ec3a041032a8

_*ƘURUCIYA: Ita ce mataki mafi hatsari da kowane ɗan Adam yake tsallakewa kan ya zama babban mutum me cikakken hankali. Sai dai wannan mataki da ɗan Adam ke tsallakewa shekaru ne masu hatsarin gaske, idan ya wuce su lafiya ana saka masa ran samun kyakywar rayuwa zuwa tsufa, idan kuwa aka samu tangarɗa rayuwa ta samu tawaya zuwa tsufa. SHIN KE UWA CE? SHIN KINA CIKIN WANNAN MATAKI NA ƘIRUCIYA HAR YANZU, KO KUWA KAI NAMIJI NE KANA DA 'YAN UWA MATA? Ya dace ki karanta wannan littafi. Rayuwar matasanmu a makarantun sakandare, hatsarin wasu al'adun bahaushe ga 'ya'yayensu mussaman mata, illar sangarta, Cutar depression, shaye-shayen matasan yara mussaman mata, dama abubuwa da baku yi zato ba, suna nan a cikin wannan littafi, ku garzaya manhajar Arewabooks don mallakar naku, ko ku kira wannan lambar don sayen naku a kan kuɗi ƙalilan 08081012143*_

Ayshercool.
GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

*Littafina Aƙidata da kuma Ruɗin ƙuriciya, na kuɗi ne, sauran duk free me*

20-21

Wani irin abu mai bala'in ɗaci ne, ya shiga tsirgawa Khalil tun daga maƙogwaronsa zuwa cikinsa, duk da sanyin AC dake cikin motar, bai hana shi tsatstafar da wani irin gumi ba, idanunsa suka yi jawur. Yayi shiru ya rasa abin da zai ce, sai kukan Hafsa da ya cika motar ya ke masa amsa kuwwa a cikin kunnunwamsa.
Tamkar mai koyon magana ya fara shirya jimlar da zai rarrashi Hafsa da ita, sai dai suka maƙale a iya wuyansa, ya kasa furata su a kan harshensa.
Da ƙyar ya iya cewa "Is ok, kukan ya isa haka, kije gida, ki samu wuri ki kwanta ki huta" Hafsa ta kalli Khalil tana son karantar wani abu a fuskarsa, amma ta kasa kasancewar, ya kauda kansa gefe. Cikin ɗan ragowar kuzarin da ya rage mata, wanda take jin tamkar ba zai iya ɗaukarta ba, ta buɗe murfin motar, ta ja ƙafafuwanta da suka gama yi mata sanyi kamar ba a jikinta ba, zuwa cikin soron gidansu, wanda duhu ya mamaye, ta durƙusa ta haɗa kanta da gwiwa ta cigaba da rera kukanta.
Sai da Khalil ya tabbatar ta shiga gida, sannan sannu a hankali ya kunna motar ya bar wurin, cikin tsananin tunani da damuwa Khalil ya nufi hanyar gida. Ikon Allah ne kawai ya kai Khalil gida, saboda tuƙi yake sam hankalinsa baya jikinsa, dan lokaci lokaci ya kan daki sitiyarin motar tasa da ƙarfi yana huci.

Amina ta zazzage kayan da Ammin Azima ta bata, har da kayan kwalliya, da wasu dogayen riguna da atamfa, ga kayan ciye-ciye.
"Ohh ni Amina, Allah sarki ashe akwai masu kuɗi masu mutunci, matar nan har da rungumeni kamar 'yar da ta haifa, a gidan nan kuwa bayan hantara da kyara ba abin da suka saka gaba, muma Allah kai mana arziƙi na halal muyi ta jawo 'yan uwa talakawa muna ci tare.

Hafsa kuwa sai da tayi kuka mai isarta, sannan ta share hawayenta ta shiga gida.
Mama ta ce 'Khalil ɗin ya tafi ne?" Jinjinawa Mama kai kawai tayi, ta shiga ƙoƙarin gyara shimfiɗarta ta kwanta.
"Ko dai halin naki na wulaƙanci kika yi masa ne? Naga kin dawo ba walwala jiki duk a sake" Murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo Hafsa tayi ta ce "Haba Mama, ba abin da nayi masa, lafiya ƙalau muka rabu, bacci nake ji ne".

"To shikenan, ba zaki ci Abinci ba zaki kwanta".

"Eh, na ɗumama da safe, cikina ya ɓaci ɗazu"

"To shikenan, Allah ya sawwaƙe"

Hafsa ta nemi wuri ta kwanta, ta shige cikin bargo, ta ɗauko 'yar wayarta ta zuba mata ido, tana tunanin ko Khalil zai kirata a wayar, har ku san sha ɗaya na dare, ta kasa bacci tana dakon saƙon Khalil kamar yadda ya saba, amma shiru nan da nan wata karaya ta zo mata, ta sawa zuciyarta cewa Khalil babu lallai ya cigaba da sonta ko ya aureta, Gashi ta kamu da soyayyarsa ba da wasa ba. A hankali ta sanya hannu ta toshe bakinta, ta lumshe idanunta hawaye suka dinga zuba daga idanunta.
"Hafsa ya naji kamar kina nishi? Ko mura kike?"

"Eh Mama"

"Sannu, daga yanzu idan ya zo ki dinga yi muku shimfiÉ—a a soro, kinga garin da sanyi sosai, har da wannan iskar ta saki mura"

Hafsa ji tayi tamkar ta ce "Mama ba zai dawo ba' Amma ta ce "To" ta ja bakinta ta tsuke.

Khalil juyi kawai yake a kan gadonsa, ya rasa in da zai sa kansa yaji daɗi, idan aka jima sai ya tashi zaune yayi tagumi ya rirriƙe kansa, idan ya gaji sai ya koma ya kwanta. Tunani daban daban a zuciyarsa, me yasa dangin Mahifin Hafsa suka kasance a haka? Tuna nasu dangin mahaifin yayi, yadda suke nuna musu ƙauna da soyayya, amma sam Mummy ba ta son alaƙar su da su, tabbas da sune suka tsinci kansu a halin da su Hafsa suka tsinta, ya san babu yadda za ayi, dangin mahaifinsu su wulaƙanta su haka.
Gaba daya bacci ya gagari idanun Khalil, saboda damuwa.
Washegari da safe ma haka ya tashi duk babu daÉ—i, dan haka ya kashe wayoyinsa, dan karma wani ya takura masa.
Har ƙarfe sha biyu na rana ba Khalil babu dalilinsa bai fito ba, balle ya karya kumallo.
Mummy ta kasa jurewa ta tafi sashin Khalil, abin mamaki ta ganshi a ƙudundune a kan gado. Da sauri ta ƙarasa tana kiran sunansa, tare da janye bargon. A hankali ya ware idanunsa a kan Mummy, sai da ta tsorata da yadda taga idanunsa sun yi jawur, jijiyoyin kansa duk sun kumbura.
"Khalil lafiyarka ƙalau kuwa?" A hankali ya gyara kwanciyarsa, ya tashi zaune yana sauke ajiyar zuciya.

"Magana nake maka fa, baka da lafiya ne?".

"Da ciwon kai na kwana ne"

"Amma shi ne baka gaya mini ba? Kalli yadda duk ka koma wani iri, kwanciyar ce zata yi maka magani? Tashi kayi wanka ka karya, muje in kai ka Asibiti".

Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Mummy ki bari ba sai naje Asibiti ba, zan warke".

"A'a ban yadda ba, tashi kayi wankan, sai in kira Aliyun ya zo gida ya dubaka" haka Khalil ya tashi ya nufi banɗaki, yana jan ƙafa kamar wanda yake maye.

Ko da Mummy ta koma ta tura Amina, taje ta gyarawa Khalil É—aki ta kai masa Abinci.

Wasa-wasa kan Doctor Aliyu ya zo, wani irin zazzaɓi ya rufe Khalil, ga jiri da yake ɗibansa yana daga kwance.
Nan da nan kowa hankalinsa ya tashi a gidan, suka shiga damuwa Daddy da baya nan ma ya dawo gida, duk suka kewaye Khalil da Mama ta lallaɓo shi, ta dawo da shi falo ta bashi Abinci, shi ma da ƙyar ya ci ya ce ya ƙoshi.
A tambayoyin da Aliyu ya yi masa, ya fuskanci kamar wani abu ne a ransa yake damunsa, amma ganin Khalil na kakkaucewa ya Sanya ya ƙyaleshi, ya rubuta allurai da ruwa ya bayar aka sayo.
Ita Amina har mamaki abin yake bata, murƙusheshen ƙato kamar Khalil, amma dan yana zazzaɓi an kewaye shi, sai sannu suke masa, wanan na shafa kansa wannan na wannan, fuskokinsu duk damuwa.
Suna nan zaune aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, Amina ce ta tashi ta je ta buɗe, Abdul ta gani a tsaye.
Murmushi tayi masa tare da gaishe shi, ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Khalil na ciki ne? Na kira wayarsa a kashe, kuma na zo É—akinsa tun É—azu baya nan".

Amina ta ce "Shigo gashi nan bashi da lafiya"
"Subhanallah" shi ne abin da ya furta, ya shiga falon da sauri.

Mummy na tozali da Abdul ta haÉ—e rai, haka ma Fadila, suka wani tsuke fuska tamkar sun ga kashi.

Abdul ya sha jinin jikinsa, amma ya basar, ya ƙaraso ya gaida Daddy, Daddy ya amsa masa cikin sakin fuska, Mummy kuwa da ƙyar ta amsa masa, ya miƙawa doctor Aliyu hannu suka gaisa.
Abdul ya ce "Daddy meya sameshi haka? Shekaranjiya mun haɗu lafiyarsa ƙalau".

Daddy ya ce "Ka san shi Allah ba yadda ba ya juya lamuransa, yau dai ya tashi jiki babu daÉ—i, ni ban sani bama, na fita muna shirya wata seminar da za ayi da a Kano.
Khalil ya buÉ—e idonsa ya kalli inda Abdul yake.
Abdul ya ce "Khalil, sannu ya jikin"
Khalil baya son yin magana, dan haka ya yiwa Abdul alama da ya matso kusa da shi.
Abdul ya matsa kusa da Khalil yana masa sannu.
Ya kamo hannun Abdul, ya É—ora a goshinsa, a hankali ya furta "Abdul kaina kamar zai fashe".

"Sannu zai daina, ya a kai ka kwana babu lafiya baka gayawa kowa ba?"

"Ka bari kawai, ka zauna a nan kusa dani"

"To ina nan kusa da kai"

Haushi ya kama Mummy, Fadila kuwa kallon da Abdul ke mata ne, ya sa ta ja tsaki, tana harare harare.

Doctor Aliyu ya kalli Fadila ya ce "Autar Mummynta, ina abokin nan naki kuwa ya jikin nasa?"

"Ya warke" ta bashi amsa.

"Masha Allah, yana nan dai ƙalau ko? Ko shi ne sirikin Mummy ne?"

Haushi ne ya kama Fadila ta ce "Ban sani ba" ta miƙe ta bar falon, Mummy ta bita da kallo. Ta kalli Aliyu ta ce "Wai a kan wa kake magana ne?"

"Wani abokin karatun ta ta kawo mana Asibiti, bashi da lafiya yana fama da asma, shi ne nake tsokanarta".

Mummy ta É—an gimtse baki, tana hura hanci.

Abdul yana nan zaune, har ruwan da aka sakawa Khalil ya ƙare, lokacin la'asar tayi, Khalil ya ce masallaci zai tafi.
Mummy ta ce "Ka haƙura kayi salla a gida, saboda jirin".

"A'a Mummy, zan bi Abdul" ba dan Mummy ta so ba, ta ƙyale shi.
Chapter 44 · 0% Book details