Sashe 53
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Zainab tayi masa rakiya, yana shirin fitowa ya tuna ƙaramar wayarsa a ɗakin Computers ɗinsa ya barta, ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Duba mini wayata a ɗakin aikina please"
Ba tare da ta ce komai ba, ta tafi É—auko masa wayar.
Sai dai data tashi dawowa, yayi tozali da littafin Amina da ta bar shi a É—akin a hannunta, ta nufo shi tana masa wani irin kallo da ya kasa tantancewa.
AYSHERCOOL
0808102143
GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)
PAGE 28-29
Sai da hantar cikin Alhaji Ahmad ta kaɗa, saboda tsananin tsoron da ya shiga, har wata ƙishirwar wucin gadi ce ta kama shi, amma cikin dakiya da maziya ya maze ya bari ta ƙaraso.
"Meye wannan nake gani haka?" Tayi maganar tana nuna masa littafin.
Cikin rashin fahimta ya kalleta ya ce "Ban fahimta ba"
"Littafin 'yar aiki na gani a É—akin aikin ka".
Alhaji Ahmad ya miƙe tsaye ya ce "Eh, na shiga zan yi amfani da ɗakin, amma duk yayi ƙura, duk da ba na shiga sai ina buƙatar yin aiki, ai Yakamata ki dinga sakawa ana gyarawa, ko gogewa ne ayi, ganin ba ayi hakan bane ya sa na bawa yarinyar umarnin gyarawa, ina ga mantawa tayi da shi a ciki". Har zuciyarta ta ji ta gamsu da bayanin da yayi mata.
'haka ne, hankalina ne bai kai a gyara ɗin ba, kuma nafi son idan za a gyara ɗin, a gyara ina wurin kar ayi maka ɓarna. A dawo lafiya"
"Yauwa na gode" ya amsa cikin mazewa ya juya ya bar Falon, yana yiwa Allah godiya da ya rufa masa asiri.
Amina kuwa da shirirtarta, tunani ta dinga yi a kan ta yaya ake sayar da kuÉ—i, kamar yadda Daddy ya gaya mata, amma bata iya gano ta yadda za'a sayar da kuÉ—i ba.
Lesson ɗin da take zuwa Makaranta ta fara gajiya, dan babu hutu sam, ga aikin gidan nan ba afuwa, kullum da abin da za'a ƙaƙalo a saka ka.
Yau Fadila a makare ta zo ita ma, motarta ta so ta bata matsala a hanya, sai dai tana zuwa ta tarar da kankiya ne a cikin ajin, bata ko bi ta kansa ba ta shiga ajin, sai dai ta hango Yazeed a wurin zamanta, a jikin window.
Tuno ranar da tayi masa wulaƙanci tayi, har ciwonsa ya tashi, dan haka ba tace masa komai ba ta zauna a kusa da shi. Wani irin warning glance sir Kankiya yayi mata, amma ta share shi, ta ciro littafinta daga jaka.
Gaba É—aya annurin fuskar Kankiya ya É—auke, ya É—aure fuska gashi baya son ya aikata wani abu, da zai sa wani ya fuskanci son Fadila yake, kuma yana adawa da Yazid.
Haka ya gama lectures É—in yana harar Fadila, ita kuwa ta nuna sam bata san ma me yake yi ba.
Bayan fitarsa ta ɗan saci kallon Yazid, ta basar, shikuwa ƙamshin turarenta ya hanashi sukuni.
Littafinta ya janyo, ya juya bayan yayi rubutu "Ina kwana ukuty?" Kallonsa tayi, gata gashi maimakon yayi mata magana, amma saboda wani salon rainin hankali shine ya rubuta mata.
Banza tayi masa taƙi kulashi. Ya sake rubuta mata 'Ya kika yi shiru, ko in tasar miki daga wurinki, naga kin haɗe rai?"
Babban abin da ya bata mamaki,bai wuce yadda yake rubutun da irin handwriting É—inta ba. Kallonsa tayi cikin mamaki tana sake kallon rubutun, ba wanda zai ce ba nata bane.
Ganin tana kallonsa tare da kallon rubutun ne ya sanya shi É—age mata gira É—aya.
"Talk" ya sake rubuta mata.
"Bani littafina, tun da kurmancewa kayi yau"
Murmushi yayi ya ce "Ban kurmance ba, azumin magana nake".
Ta zura littafin a jaka, ya miƙo mata wasu takardu, tasa hannu ta karɓa tana dubawa.
Presentation É—in da za suyi ne, na 'yan group É—in su gaba É—aya yayi musu, kuma a rubuce ya kai fullscap bakwai,tabi tsararren rubutun nasa da kallo, sannan ta kalleshi cikin mamaki 'Wai duk daga jiya zuwa yau kayi wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
"Amma ai ka wahalar da kanka da yawa, wannan uban rubutun haka? Shikenan Sai mu kai Cafe a buga?"
Duk da yau baya son yin Magana, amma yaji daɗin yadda ta yaba ƙoƙarin sa.
Dan haka ya ce "Eh, da ina da babbar waya ko system, da a ciki zan mana sai ayi printing, kowa a bashi wanda zai yi presenting"
Fadila ta ce "System ɗina na mota, bari in ɗauko sai in fara typing ɗin, kar aikin yayi maka yawa" ƙarara yake ganin tausayawa a idonta.
"Muje in rakaki" Suka tashi suka jera zuwa in da motarta take, ta buÉ—e ta É—auko system É—in sannan suka dawo aji.
Ya nemi wuri ya zauna, ta buɗe system ɗin ta kunna, hotonta ya bayyana a kan lock screen, ta saka password sai ga wani ya bayyana a wallpaper ɗin ta, ba ƙaramin tafiya da Yazeed hotunan suka yi ba.
Amra ƙawar Fadila a baya, banda yanzu da ta daina shiga sabgar ta, saboda Amran na da wasu halaye da ba su yi mata ba, ta ƙaraso in da su Yazid suke zaune, suka gaisa sama-sama da Fadila. Sannan ta kalli Yazeed ta ce "Yaya Yazid dan Allah wurinka na zo, 'yan group ɗin mu zaka ɗan taimaka mana a kan presentation ɗin da zamuyi"
"A yanzu dai aikin namu yake yi, kuna iya jira zuwa ya gama" Fadila ta bata amsa.
"Bafa da ke nake ba" Amra ta mayar mata da martani.
Yazeed ya ce "Afuwan Amra, bari in kammala namu, sai in zo"
Guntun tsaki Fadila tayi, ta cigaba da operating system É—in.
Janyo System ɗin gabansa yayi, dan a ganinsa bata sauri a typing ɗin, tunda ya zuba yatsunsa a kan keyboard ɗin nan yake sarrafasu cikin gwanancewa kamar wani inji. Fadila ta ƙureshi da ido, shi kusan komai ya iya, ana batun Mutane gifted bata taɓa gazagata hakan ba, sai a kan Yazeed.
Ji tayi kamar ta tambayeshi a ina ya koyi computer, amma ta basar.
Lokacin sallar azahar yayi, Yazeed ya ce "Zai je yayi sallah, idan ya dawo zai cigaba.
Ta tashi ta bashi wuri, ya tafi salla, ita ma tashi tayi ta bar System É—in a wurin saboda careless, ta tafi yin salla da cin abinci.
Bayan ya dawo ya tarar da komai yadda ta barshi, ya zauna ya tattara mata litattafanta, minimising yayi, ya zubawa kyakywar fuskarta da ke kan screen É—in system É—in ido, yana jin yadda wani abu ke sake fuzgarsa game da ita.
"Ina sonki Fadila" ya furta yana cigaba da ƙarewa screen ɗin kallo.
"Malam Yazeed wai haryanzu baka gama ba?" Ya ji murayar Amra a kunnensa.
Yazeed ya kalli Amra ya ce "Ku mini haƙuri, na kusa gama namu, idan na gama zan zo in sha Allah"
"To shikenan" ta amsa masa tana ƙoƙarin barin wurin, Fadila ta shigo hannunta da leda, ta ƙaraso ta zauna, tana kallon screen ɗin system ɗin.
"Ka kusa gamawa ne?"
"Eh, saura kaÉ—an, so nake in yi in gama, wancan group É—in suna jirana".
Fadila ta yamuatsa fuska ta ce "Kaga kayi mana abinmu a nutse Please, ba suna da waya ba suje suyi mana, ko su tafi Library"
Yazida ya ce "A'a ba'ayi haka ba, zasu ga ban kyauta musu ba, kuma wulaƙanci babu daɗi"
Taɓe baki tayi ta miƙa masa leda ɗaya gabansa.
Ya kalli ledar ya ce "Meye wannan?"
"Abinci" ta bashi amsa.
"Alhamdilillah na gode, amma na ƙoshi"
Cikin tsiwa ta ce "Saboda na zuba wani abu a ciki?"
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Idan ma kin zuba wani abu a ciki da ina jin yunwa ba ruwana cimyewa zan yi"
"Wannan shi ne karo na biyu na baka Abinci ka ƙi ci, meye dalili?".
Yazeed ya ce "Nifa yau azumi nake"
"Dama ana azumi ranar talata?"
"Eh mana, azumin Annabi dawud, yau kayi gobe ka sha ruwa"
Tsuke fuska tayi ta ce "Sannu waliyyi, kamar fa raina mini hankali kawai kake yi, ba wanda zai iya irin wannan azumin"
"Inji wa? Gwauraye na yin irin wannan azumin, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ne ya bawa samari shawarar yawan yin azumi idan... Sai kuma yayi shiru.
Gaba É—aya Fadila bata gane in da zancen Yazeed ya dosa ba.
"Kaga ni ban taɓa ji ba, ka dubo wata ƙaryara dai kayi"
Ɗan tsuke fuska yayi, ya saka idanunsa a nata, "Ni ne nake ƙaryar?"
Tsiwa ta so yi, amma sai ta kasa jikinta yayi sanyi, idanun Yazid suka yi tasiri a kanta, wanda sai da idanunta suka yi nauyi, ta janye idanunta tana É—an tura baki.
ÆŠauke idonsa yayi shima, yana jin daÉ—in yadda yake yi mata kwarjini wasu lokutan, har ta kasa magana.
Kusan mintuna goma, yana typing, ya ƙi taɓa ledar Abincin.
Can ta kuma kallonsa ta ce"Wai ba zaka É—au Abincin nan ko ruwan ka sha ba?"
"Wai ina ruwanki dani ne, nace miki azumi nake"
"Wane irin azumi ne da za'ace wani azumin samari, ba azumin tsofaffi kawai ake ba?"
Sosai Yazid yake dariya, wata amsa ya so ya bata, amma yaga amsar tayi nauyi da yawa, dan haka ya ƙyaleta ya cigaba da dariya.
Ganin yadda yake dariya sosai, haƙoransa suka bayyana ya sanya ta ce "Wallahi ba azumi kake yi ba" ta faɗa cike da tsiwa.
"Subhanallah, ya aka yi kika san ba azumi nake ba? Shikenan ba azumi nake ba ba zan ci ba"
Haushi ne Yakamata, ta miƙe tsaye ta fara jan system ɗinta.
Ya kalleta ya ce "Ya dai?"
"Bani System ɗina tafiya zan yi" riƙewa yayi yana murmushi ya ce "Sorry yi haƙuri, zan ci" yayi maganar wani irin farinciki yana ratsa shi, kamar a mafarki yake ganin faruwar al'amarin, wai Fadila ce take jin haushi dan be karɓi abin hannunta ba.
"Kar ma kaci, bani tafiya zan yi"
"Yi haƙuri in ƙarasa, sai muje Cafe a cire, nima sonake na gama da wuri, idan lecturer nan bai zo ba, zanje wurin sir Kankiya, mun haɗu a masallaci ya ce idan na gama lectures in je Office ɗinsa"
ÆŠan saroro tayi, ta kalleshi ta ce "Me kayi masa?"
"Nima ban sani ba, kawai dai ya ce inje"
"Yi sauri ka ƙarasa muje"
"Muje ina?"
"Wurinsa" ta bashi amsa.