← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 84

Sashe 20

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhamdilillah, Hafsa ciniki ya nata haɓɓaka, sai ai babban abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya bai wuce yadda maza ke zuwa su taru a wurin ba wanda sam hakan ba ya yi mata daɗi, gashi wasu 'yan iska wasu na kirki, da yake gata ga wurin mai shayi, wasu ma haka zasu zo su zauna suna shan sigari a wurin.  A haka wasu suke nuna suna sonta, da zarar ta musu halin nata na miskilanci, sai zagi da cin mutunci, ita dai bata taɓa ɗaga kai ta kula kowa ba balle ta bar abin faɗa.
Abin na damunta, amma ba ta gaya wa Mama ba, dan da zarar ta ji abin da yake faruwa, zata iya dakatar da cigaba da sayar da awarar, kuma idan ta dakatar sana'ar me za suyi?. Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru, take ta Addu'a Allah ya kawo musu mafita.

Tun bayan fitowar su daga test, Fadeela sai murna take yi, ko bakomai ta samu abin da ta rubuta, amma sam ba ta ji ta damu da abin da ya faru da Yazeed ba, dan a ganinta ai ba ita tace ya taimaka mata ba.
  Tana tsaye tana waige-waige, ta hango Yusra tana ƙarasowa in da take, ta kalli Fadila ta ce "Girl ya na ganki duk wani iri ne?"

"Bari kawai unexpected test aka yi mana".

Yusra ta yi murmushi ta ce "Baki shirya ba kenan?".

Fadila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Ina na wani shirya, ni gaba ɗaya ma bana gane course ɗin, gashi dama muna takun saƙa da lecturer, kinga wata applied question da ya yi mana, abin ba a magana".

"Amma dai kin rubuta wani abu ko?".

"Me kuwa na rubuta? Wani ne ya gaya mini na rubuta, shi kuma aka yi masa minusing marks".

Yusra ta ce "Subhanallah garin yaya?".

Nan Fadila ta bata labarin Yazeed.
"Girl gaskiya ba kya kyautawa, ban ji daÉ—in abin da kike masa ba".

"Ni na sashi ya dinga mini shishshigi? Kinga ni muje in samu wani abun in ci yunwa nake ji".

Yusra ta kalli agogon hannunta ta ce "No, kinga yau Friday, zo muje masallacin cikin school mu saurari huÉ—uba, idan aka yi sallar juma'a, sai mu je muci Abincin daga nan mu tafi gida".

Fadila ta ce "Masallacin Juma'a sai ka ce wasu maza?".

"Kin ji ki, ai mata ma na zuwa sallar juma'a, ma samu muji huÉ—uba"

Haka Yusra ta takurawa Fadila, suka tafi masallaci, a hanya Fadila take sanar wa da Yusra da batun dawowar Khalil. Suka dinga planing É—in yadda zasu shawo kan Khalil a kan ya so Yusra.
Suka ƙarasa masallacin mata, suka shiga suka zauna. Sai dai shiru liman bai zo ba, balle a fara huɗuba, can aka fara gyaran murya aka fara da buɗewa da addu'a, can kuma ya fara gabatar da huɗuba cikin harshen larabci.
Subhanallah, kai ba ka ce mai yin huɗubar ya taɓa jin yaren hausa ba, duk da Fadila ba ta jin larabci, amma ta nutsu tana sauraren yadda huɗubar ke ratsata, bugu da ƙari yaren larabci na matuƙar burgeta, aka jima ya fara huɗubar da Hausa, wanda yayi huɗubar akan tsoron Allah da riƙon gaskiya yayi, ya yi amfani da hikima sosai a wurin gabatar da huɗubar.
Bayan ya kammala kuma, aka tada salla. Subhanallah sai da ya fara karatun Alkur'ani, a lokacin wata nutsuwa ta sake saukarwa Fadila, muryarsa mai daÉ—in amo da saurare, ga wurin yayi tsit kamar ruwa ya cinye su. Fadila ji ta yi tamkar kar a idar da sallar nan, saboda tsananin daÉ—in karatun, tabbas makarancin gwani ne wurin iya sarrafa harsashe, dan hatta a cikin huÉ—ubarsa akwai salo na narka zuciyar mai sauraro, karatunsa akwai amo mai sanyawa zukata nutsuwa.
Haka aka idar da sallar nan suka nufi wurin cin abinci, amma still Fadila na cigaba da jiyo karatun nan a cikin kunnuwanta, tamkar ta magantu sai kuma ta yi shiru, suka tafi cin Abinci.

Bayan sun kammala cin abincin, Yusra ta tafi don ta kammala lectures É—inta na ranar, Fadila kuwa suna da lectures 2-5.
Ko da ta shiga ajinsu, ta tarar da duk matasan samarin nan na ajin su, sun kewaye Yazeed, shi kuma ya ɗan ɓata fuska duk da da wuya ka ga fushi a fuskarsa, dan mutum ne mai yawan murmushi, da alama dai sun takura masa, sai sunkuyar da kansa yake yi.
Captain ya cire hular kan Yazeed, ya duƙa a gaban Yazeed yana cewa ya Sheikh, a shafa mana karama.
Wani siririn kyau ne ya bayyana a fuskar Yazeed, bayan Captain ya cire masa hula, yana da wani kwantaccen baƙin gashi, da ya haɗe da sajensa ya kwanta a fuskarsa, zuwa ɗan madaidaicin gemunsa.
Ya miƙa hannu ya karɓi hularsa tare da mayarwa kansa. Yamutsa fuska Fadila ta yi ta ce "Dan Allah ku tashi ku bani wuri, kawai kun kafa daba kun cikawa mutane kunne da hayaniya".
Captain y kalli Fadila ya ce "Ke kul, mun kafa dabar kwasar tabarraki ne, ashe muna zaune da babban malami amma babu labari, ai tun da nake zuwa sallar juma'a ban taɓa jin huɗubar da ta ratsani kamar wadda Sheikh, Malam Yazeed ya yi ba" Saroro Fadil ta kalli Captain ta ce "Kamar yaya?".

"Ai duk wanda ya je sallar juma'a yau a masallacin school É—in nan, ya ji yadda ya dinga zuba larabci, sai ma da ya fara karatun Alqur'ani, kamar mutum ya suma dan daÉ—i"
She can't believe that Yazeed ne ya yi wannan karatu, guntun tsaki ta ja, ƙila ma ƙaryar Captain ce kawai.
Zama ta yi a wurin zamanta ta yi shiru, tana tunanin muryar da aka yi huÉ—uba, tabbas muryar Yazeed ce, ko da be fiye surutu ba, amma muryarsa a nutse take cike da nutsuwa da kuma iyayi, kamar yadda take faÉ—a.
Shi kuwa Yazeed tuni ya bar ajin, dan baya son abin da suke masa sam.
Nan taji ana hirar, limamin masallacin ne ba lafiya, ya shirya zai taho, ya yanke jiki ya faɗi, kuma ba a samu information da wuri ba, an tsaya mujadalar wanda zai ja Sallar, shi ya karɓa ya yi.

Har aka shigo lectures, Fadila na satar  kallon Yazeed, da son tabattar yanzu daga bakin wannan ɗan tahalikin wannan karatun ya dinga fitowa ɗazu? Sam babu kama.
Karaf Yazeed ya É—ago ido, suka haÉ—a ido da Fadila, wata uwar harar ta watsa masa, kamar ba ita take kallonsa ba.
ÆŠauke idonsa yayi, yana fatan Allah ya sa ba wata tsiyar Fadila take shirya yi masa ba.

Amina wuni tayi tana sintiri tsakanin falo da harabar gidan, dan ganin me kaita makaran ya dawo, amma babu shi babu alamar sa. Gaba ɗaya har ranta ya fara ɓaci ta fara tunanin ko dai ba yau ɗin zai dawo ba.
Shi kuwa Khalil tuni ya dawo, dan tun bayan azahar ya dawo, ya shiga sashinsa, ya yi wanka ya yi kwanciyarsa dan a gajiye yake sosai.
Ya makara sallar la'asar, dan haka a É—akinsa ya yi ta, sannan ya shirya ya fita.

Amina kuwa tana zaune a falo, ta zubawa TV ido, tana kallo, tana fuskantar wani abu daga larabcin da ake fassara yaren jaruman.

Ba tsammani ta ga mutum ya faÉ—o falon, dogo da shi kawai ya sa kai ya nufi sashin Hajiya Zainab, ba tare da ko sallama ya yi ba.

"Kai bawan Allah daga ina? Zaka faɗowa mutane haka ba sallama kawai ka miƙa wuya kamar raƙumin jeji zaka wuce".
Cak ya tsaya, ya waiwayo ya kalli bakin mai wannan maganar, gabanta ne ya faɗi da suka yi ido huɗu da shi, sai yanzu ta tuna da uwar ba'ar da tayi masa, ga kammaninsa sak da Alhaji Ahmad sun bayyana, ba in da ya bar mahaifinsa a kamanni, sai dai yafi Alhaji Ahmad ƙuruciya ko ba a gaya mata ba ta san wannan shi ne wanda aka ce zai dawi.

Amina ta hau kame-kame "Yi haƙuri dan Allah, na manta Hajiya ta ce zaka dawo, kuma kaga kaine ma da ka shigo ba ka yi ko sallama ba, amma dai Hajiyar bata nan ta fita, ina wuni".

Ƙare mata kallo ya yi a ransa ya ce "Ko wacece wannan, a ina aka samota kuma oho?" Bai kula ta ba ya cigaba da tafiyarsa. Yana wucewa Amina ta ce "Subhanallaahi, na yi shirme wannan shegen bakin nawa, Allah ya sa kar ya gayawa babarsa na masa rashin kunya. Amma ai ba rashin kunya ba ce gaskiya ce ka shigo zalau-zalau babu sallama".

Amina na nan zaune ta taradaddin abin da ta aikata, Hajara ta fito falon, sai dai Amina ba ta gaya mata me tayi ba.
"Amina ya na ganki wani iri ne haka?"

Amina ta girgiza kai ta ce "Ba komai".

"To shikenan, mai yakamata a dafa ne yau da daddare?"

Amina ta ce "Nima ban sani ba, a dafa abin da ya sawwaƙa"

"Wai naga gaba É—aya yanayinki ya canza".

"Ba komai fa, kawai ina tunanin Baba ne".

"Ke Amina, baban da É—azu ya tafi kuma zai dawo".

"Ai ba yau zai dawo ba, wataƙila sai gobe ko in Allah ya kaimu jibi" suna tsaka da hirar sai ga Khalil ya fito, nan da nan Amina ta yi shiru.

Hajara ta risuna ta ce "Ina wuni Yallaɓai, ashe ka dawo?".

"Eh na dawo, Fadila ba ta dawo daga school bane?".

"Eh har yanzu ba ta dawo ba".

Khalil ya ce "Well Shikenan".

Hajara ta sake risunawa ta ce "A kawo maka Abinci ne?"

"Eh ajiye mini a kan dining, zan shigo in ci".

Amina dai ba tace komai ba, sai zazzare ido da take yi.

Bayan fitarsa Hajara ta ce "Shi ne fa wanda zai kai ki makaranta, da ki ke ta jira ya dawo, ya dawo amma ba ki iya gaishe shi ba".

"Na gaishe shi mana, ai ina zaune a nan falon ya zo ya wuce".

Hajara ta ce "Au to, ai na zaci baki kula shi bane, shi gaskiya ba shi da matsala sosai, be fiye wulaƙanci kamar ƙanwarsa ba".

Ita dai Amina fatan ta, Allah ya sa kar abin da tayi masa ya sanya ya ce ba ze kaita makaranta ba.
Chapter 20 · 0% Book details