Sashe 35
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hafsa ba kya tausayina ko? Kin san so kuwa? Saboda ke fa na baro aikina na taho, kawai dan na ganki, meyasa ba zaki dubeni ba. Ko ina da wani aibu ne ban sani ba?".
"A'a, baka da wani aibu ni dai kawai ka rabu da ni".
"Shikenan tunda haka kike so, jibi in Allah ya kaimu zan koma, zan zo muyi sallama, ina sonki sosai Hafsat.
Kalmar ina sonki, ta daki Hafsa sosai, dan har cikin kwayarta taji tasirin kalmar, amma ba ta jin zata iya yadda da soyayya balle tayi aure, gara su cigaba da lallaɓa rayuwa ita da Mama.
Khalil bai taɓa zaton akwai ranar da zata zo, ya dinga 'yar talakawa kamar Hafsa yana neman soyayyarta tana gara shi ba.
Aminatun Baba Hassan kuwa, ta ƙara kilewa sosai da sosai, tayi sababbin ƙawaye, gashi nan da nan ta zama sananniya a makarantar saboda ƙoƙarinta da kuma surutunta, suna ta shirye shiryen fara jarrabawar zango na farko.
Amina ta mayar da hankali wurin tattalin haddar Alqur'aninta bata zube ba, dan tana yawan tilawa kuma ta cigaba da rubutun alƙur'ani tana sake gyara kura kuranta,ta ɗora haddarta tana samun masu duba mata a makarantar.
Hajara ce a sashen Mummy, tana ta aikace aikace, Hajiya Zainab ta fito ta tarar da ita a falonta, ta kalli Hajara ta ce "kira mini 'yar mai gadin nan" Hajara ta ce to, ta tafi kitchen ta kirawo Amina. Suka dawo tare. Hajiya Zainab ta kalli Amina ta ce "Muje sashen maigidan na nake so a gyara a yiwa kwalema, gobe in Allah ya kaimu zai dawo".
Amina ta ce "To, amma na É—ora girkin rana".
"Bar shi ita ta ƙarsa, muje in buɗe miki wurin" Amina tabi bayan Hajiya Zainab, zuwa sashen da take kyautata zaton shi ne na Alhaji Ahmad.
Masha Allah, yafi ko ina kyau da tsaruwa a gidan, duk ya yi ƙura amma hakan bai hana sashin yin kyau ba, duba da kayan alatun da aka ƙawata wurin da shi.
"Gashi nan, ki gyara duk abin da yakamata, karki mink rawar kai ko kiyi abin da ban saki ba, ki gama aikin da na saki ki fito".
Amina ta ce "To insha Allah".
Bedroom kawai guda biyu ne a sashen, kowanne ya sha furnitures na alfarma. Falon kawai gari ne guda, dan set É—in kujeru biyu ne a falon.
Amina mamaki ta dinga yi, duk wannan aljannar duniya, amma ace mutum sai ya bar gida har wurin watanni uku ba nan, yana wata uwa duniya ta daban.
Amina haka ta dinga tular uban aiki, da tana ganin kamar aikin babu yawa, amma da ta fara taga aikin nayi ne, haka ta zage, wanke wannan goge wancan, karkaÉ—e can haka ta kusa wuni tana fama, sai dai idan za tayi salla ta ajiye aikin taje tayi.
Sai da ko ina ya zama tsaf ta gyara, sannan ta koma da baya, tana ƙarewa ko ina kallo, ta tabbatar komai ya gyaru tsaf, hankalinta ya sauka a kan katafariyar plsma tv wadda ta kusa cin rabin bango, tunani ta fara yi a ranta, ko a cikin wannan tv mutane sunfi girma a kan sauran ƙanan tv. Take zuciyarta ta raya mata ta kunna taga ya zata ga mutanen cikin.
Aikuwa Amina ta ƙarasa, ta kunna Tv da fari sai da ta rage yadda ta ware idanunta, saboda hasake da kuma yadda taga mutane sun bayyana a tv, kamar ta zura hannu ta ɗauko su.
A hankali ta buÉ—e idon, ta cigaba da kallon mutanen tv, shaf ta manta da a ina take, ta samu wuri ta zauna a kan kujera, tana cigaba da kallon Tv.
Sai ga Amina ta bararraje ta shantake, ta cigaba da kallo abinta hankali kwance.
"Ke ubawa ya baki izinin zama a kan kujerar nan? Lallai ne gidan ubanki ne nan É—in?" A tsorace Amina ta waiwaya ta kalli in da Hajiya Zainab ke tsaye tana nunata da yatsa. Da sauri Amina ta tashi tsaye, tana rarraba ido.
"Waye ya ce ki zauna a falon mijina, har ki harɗe ƙafa kina kallo, nawa ne a ciki kuɗin babanki da aka haɗa aka gina ɗakin aka zuba furnitures ɗin?" Babu babban abin da ke ƙular da Amina irin da tayi laifi, sai a fara ambaton Baba ana ci masa zarafi.
Amina tayi shiru tare da sunkunyar da kai, tana jin yadda sautin maganganun Hajiya Zainab ke amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, suna sukar zuciyarta.
Maganganun Baba ta tuna, da yake nanata mata ba yau ba gobe a kan tayi haƙuri, dan ta samu ta kammala karatun ta lafiya, hakan ya saka nutsuwa da haƙuri ya shigeta, a sanyaye ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, insha Allah ba zan sake ba".
"Ki ma sake, munafuka sai kin yi rashin mutunci ki koma kina wani kwantar da kai, ni zan fita Yanzu, ki zo ki wuce ki bar sashen nan, idan na fita daga ke sai halinki a gidan, idan kin ga dama, ki kuma aikata wani rashin mutuncin, sai kin koma in da ki ka fito" Amina dai ba tace uffan ba, sumi-sumi ta bar falon, ƙasan zuciyarta kamar ta ƙundumawa Hajiya Zainab ashariya, dan ɓacin rai.
Ɗakinta ta koma kawai ta fashe da kuka, dan ta samu sassauci daga zafin da maganganun Hajiya Zainab ke mata a zuciyarta, gaba ɗaya zaman gidan ya sire mata, sai da tayi ta gaji, sannan ta wanke fuskarta ta fito, tana fitowa babban falon gidan ta ci karo da wasu manyan mata, kai da ka gansu kaga gogaggun 'yan duniya, sun sha ado sai baza ƙamshi suke.
ÆŠaya ta kalli Amina ta ce "Ashe da mutane a gidan, muke ta kwaÉ—a sallama amma shiru".
Amina ta ce "Eh da mutane, amma masu gidan basa nan".
"Tayi nisa ne?" Suka tambayeta.
Amina ta ce "Ai da yake ni É—in ba 'yar ta bace, balle in san in da ta tafi, bata gaya mini ba sai dai ku kirata a waya"
"Ikon Allah, ke baki iya magana bane?"
Amina tai shiru ba tace komai ba, suka sami wuri a kan kujera suka zauna, Amina ta kalli ƙafar ɗaya daga cikin su, fuskarta fara tas ta sha mai, amma ƙafarta kamar ta ƙone ga ƙafar ta ta kamar ta maza, ga taƙi ɗaukar bleaching ɗin.
A zuciyarta ta ce "Ikon Allah, wata ƙatuwar ƙafa kamar ta Jarmai".
"Ke ɗan bamu ruwa, ƙishirwa ta dameni".
Amina ta koma ciki ta É—oro pure water biyu a plate ta kawo ta ajiye musu.
"Hajiya Sarah, yau nake ganin ikon Allah, wace irin 'yar aiki Zainab ta samo haka bagidajiya, ke mun miki kama da wanda zasu sha wannan ruwan? Babu na roba?".
"Ai gidan nan baƙi ba su da hurumin shan ruwan roba, na leda kawai aka ce in bayar guda ɗaya" tayi maganar tana ɗan hura hanci, alama matan sun fara takurata.
Nan suka cigaba da hirarsu da 'yan zage-zagensu, Amina kuwa ta bar musu falon. Kusan Mintuna talatin Amina ta kuma fitowa da niyyar idan sun tafi, ta gyara falon amma ta tarar da su basu da niyyar tafiya, sai ma ƙure tv da suka yi suna kallo.
Ba tunanin komai ta wuce ta kashe socket É—in tv gaba É—aya.
"Ke lafiya, meye haka?" Cewar Hajiya Turai.
"Ai ba wuta solar ce, kuma ta fara ƙara a kowane lokaci zata iya ɗaukewa, mai siyo fetur kuma baya nan, dan haka idan ta ɗauke ni za a saka zuwa sayen fetur ni ba namiji ba, kinga ai gara in kashe ai reserving solar".
"Ke wai ke meye matsayinki a gidan nan ne?".
" 'yar aiki" ta faÉ—a kanta tsaye.
"Kin san mu suwaye da kike mana wannan iskancin?".
"A'a Anty, ba laifina bane dokar matar gidance a haka".
Hajiya Sarah ta ce "To bari Zainab É—in ta dawo muji daga bakinta"
Komawa kitchen Amina tayi, a ranta tana ƙunƙuni.
Sai daf da magariba sannan Hajiya Zainab ta dawo gidan, ko da ta shigo falo ta tarar da su Hajiya Turai, suka sanya wata uwar shewa.
"Hajiya Turai yaushe ki ka shigo ƙasar nan?"
Hajiya Zainab tayi maganar tana ƙoƙarin zama, cike da mamakin da ya mamaye fuskarta.
Turai ta ce "Sati na É—aya, nace bari nayi miki zuwan bazata".
"Amma Sarah meyasa baku gaya mini zaku zo ba? Ai da ban fita ba. Hajiya Turai mutanen Saudiyya" Nan suka ɓarke da hirar yaushe gamo.
"Kun ci abinci kuwa?".
"Wane Abinci, ke dai a garin yayime yayimenki sai kin yayi mo mai zane ki, wata tsigalalliyar yarinya muka tarar marar mutunci, ko ruwa hanamu tayi sai pure water ta bamu".
Hajiya Zainab ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan Yarinyar ta zame mini jaraba, tun da tazo gidan nan nake fama da ita".
"To ki sallameta mana" Hajiya Sarah ta faÉ—a tana yatsuna fuska.
"Yarinyar ce tunda nake masu aiki, ban taɓa samun 'yar aiki mara son jiki kamarta ba, ba ta jin jikinta wurin aiki, ba ta da ƙyuya ba munafunci, sai iya shege da rashin mutunci a cikinta. Sai naji kamar in koreta amma sai in tuna irin aikin da take mini in ƙyaleta".
"Ai irin haka warning zaki kasa mata, koma ki bata suspension, Yarinyar bata da kunya sam".
Rai a ɓace Hajiya Zainab ta dinga ƙwalawa Amina kira, ita sam Amina ma bata san ta dawo ba, ƙasa-ƙasa take jiyo kiran, ta fito falon tana sussunkuyar da kai kamar mara gaskiya.
"Ke shine nayi baƙi kika wulaƙanta su, ki ka basu ruwan leda dan baki da mutunci?"
"Hajiya kefa kika ce kar in sake bawa duk wani baƙo ruwan roba balle Abinci sai pure water, shiyasa na basu".