← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 84

Sashe 13

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka har garin Allah ya waye, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake gudanar da komai, yana nan zaune a bakin gate yana ta jujjuya yadda zai ɓullowa lamarin, wajen ƙarfe goma Fadila ta fito ta fita, wajen ƙarfe sha ɗaya kuma Alhaji Ahmad ya fito, cikin wani ash ɗin yadi, an fito masa da motar sa da zai fita da ita.

Alhaji Ahmad yana ƙoƙarin shiga mota, Baba Hassan ya cin masa, cikin girmamawa ya gaisheshi, Alhaji Ahmad ya amsa cikin mutuntawa.

Baba Hassan ya duƙa ya ce "Yallaɓai dan Allah alfarma nake nema".

Alhaji Ahmad ya gyara tsayuwa ya ce "Ina jinka".

Baba Hassan ya ce "Dama Yallaɓai game da 'yar wajena ce, jarrabawar nan ba a samu damar yin ta ba"

"Subhanallah, garin yaya?"

"Kuɗin aka kai a ƙurarraren lokaci, to yarinyar tawa tana son ta yi karatu sosai da sosai, to ka san mutanenmu na karkara, 'yan uwana ba son karatun nata suke ba, to rashin samun damar rubuta jarrabawar ya sanya suna ƙoƙarin su Aurar mini da ita. Shi ne nace dan Allah tun da dama Asabe ta tafi, a taimaka mini a ɗauki yarinyar tawa ta maye gurbin Asabe, idan ya so kuɗin aikin nata sai a sakata a makarantar boko, a dinga biya mata kuɗin makarantar".

Alhaji Ahmad ya ce "Malam Hassan wannan ai ba wani abun damuwa bane, bakomai ka kawota ai ilimi ga 'ya mace abin so ne, idan na dawo an jima ka tuna mini zan yiwa mutan gidan magana, ka kawota".

Wata ƙwallar farinciki ta cikawa Baba Hassan ido, ya zube ƙasa yana faɗin "Na gode, Na gode Allah ya jiƙan magabata ya yauƙaƙa Arziki, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi duniya da lahira, yadda ka Sanya farinciki a cikin zuciyata da ceto 'yata ubangiji Allah ya faranta maka, yayi maka tukuici na Alkhairi".

Alhaji Ahmad ya ce "Haba Malam Hassan, kar ka damu dan Allah wannan ai ba wani abin damuwa bane, Allah yayi wa yaranmu albarka baki É—aya".

"Ameen Yallaɓai godiya nake".

Baba Hassan ji yake kamar an yaye masa damuwar da yake ciki, dan yana zuwa É—akinsa yayi sujudu shukur, ya lalubo wayarsa ya kira Saminu.

Sai da ta kusa tsinkewa Sannan Saminu ya É—aga, suka gaisa Baba Hassan ya ce "Saminu, dan Allah idan ka tashi tahowa, duk yadda zaka yi ka taho mini da Amina garin nan, ko a tasha ka ajiyeta sai ka kirani in zo in tafi da ita".

Saminu ya ce "To shikenan, amma ba zan taho yau ba gaskiya, sai dai gobe in Allah ya kaimu"

"Bakomai, amma dan Allah kar ka bari su farga su san da ita zaka taho, idan kuka taho daga baya nazo in musu bayani, idan suka san zaka kawo mini ita ba zasu bari ba".

Saminu ya ce "ba komai, kar ka damu Baba insha Allah zan kawo maka ita lafiya".

"To shikenan Saminu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

************

Yau Juma'a dan haka wankan hijjabi ta yi, pink tun daga sama har ƙasa, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, ta shigo tana rataye da jakarta pink, hannunta riƙe da robar ruwa da mukullin motarta, bai san yadda aka yi ya shagala da kallonta ba, tayi kyau ƙarshe, ga wani irin sassanyan ƙamshi da take yi. Sai dai ta yi missing ɗin lectures ɗin farko da aka yi, dan suna takun saƙa da malamin, dan haka yau ba ta yi attending darasin sa ba, kuma darasin da yayi da lissafi a ciki, kuma ko da kai aka yi lissafin a ajin, abu ne mawuyaci mutum ya fahimta saboda yayi tsauri da yawa.

"Kai lafiya kar ka cinye ni dalla" tayi masa maganar cikin tsawa.

Sunkuyar da kansa ya yi daga kallonta, ya koma kallon wani wurin daban.

Class rep ne yayi dariya ya ce "Kai Fadila wannan tsawar haka?"

"To ya sani a gaba da kallo, sai na faÉ—i tukuna aikin banza".

Dariya ƙawayenta suka din ga yi, wata wadda ake cewa Amra ta ce "Kyau ki ka yi masa ko ustaz?"

Tsaki Fadila ta ja ta ce kwaji da shi.

Babu jimawa wani lecturer ya shigo, wanda ya basu class work ya ce su yi da waya, nan ya dinga yi musu mita ya ce "Ace gaba É—aya ajin nan babu wanda ya fahimci tambayar da na yi sai mutum É—aya, ina sane nace ku duba waya, dan na san idan har baku fahimci tambayar ba, babu yadda za ayi ku samo amsar. Waye Yazeed Hashim Shareef?".

"Sir" ya faÉ—a tare da É—aga hannunsa sama.

Gaba É—aya idanun mutan ajin suka dawo kansa.

"Wow, dama na gaya muku ustazan nan sune ƙwarin ajin, Malam Yazeed fito ka mana bayanin yadda ka fuskanci tambayar da na yi, har ka samu damar amsawa"

Yazeed ya fita gaban aji, ya ce "Sir zan iya yi da Hausa?".

"Yi da duk yaren da kafi iyawa"

Yazeed na haɗa ido da Fadeela ta ƙunshe baki tana sinne dariya, ta ɗan ɗaga murya ta ce "Sir gara yayi mana da hausar dai, da turancin nan bama ganewa"

Malamin bai kawo komai a ransa ba, ya yin da 'yan ajin suka gane me Fadila take nufi da faÉ—ar hakan, su kai ta yi masa dariya.
Tun a nan ya rasa karsashin da zai yi bayanin, duk ya ji jikinsa yayi sanyi, amma ya daure ya aro jarumta, ya daidaita nutsuwarsa, cikin kamalarsa ta zance da iya sarrafa harshe, yayi bayanin yadda ya fuskanci tambayar da yadda ya bi amsa tambayar.

Malamin da kansa ya tafawa Yazeed ya ce "Weldone Ustaz, you are genius man, ka burgeni ƙwarai mutane masu sharp brain irinka ba su da yawa, Allah ya ƙara basira"

Yazeed ya ce "Thank you sir".

Malamin ya ce "Gaskiya duk ajin nan babu wanda ya amsa daidai sai Malam Yazeed, dan haka kowa yaje ya sake faɗaɗa bincike a kan bayanin da yayi, zan yi test a kansa, idan kuma kuna buƙata ku tuntuɓe shi yayi muku bayani sosai".

"Gaskiya mu dai Sir kai mana bayanin da kan ka" cewar Fadila.

"Meye baki gane ba a bayanin da yayi?".

"Ni ban gane komai ba" ta faÉ—a cike da rainin hankali.

"Well, zaki iya zuwa ki same shi ya yi miki bayani".

"A'a Sir gaskiya gara ka yi mana da kanka".

"Ba zan ba" ya bata amsa.

Tura baki tayi cike tsiwa da harare-harare.

"Leave my class" malamin ya faÉ—a yana nuna mata hanyar fita.

Kamar kullum, ta saɓi jakarta ta fice, tana fita ya kalli 'yan ajin ya ce "A ciro takarda, kowa ya rubuta attendence, attendance 30 marks, test 10 marks.

Takardar attendence ta fara zagawa, har ta zo kan Yazeed, ya kalli takardar attendance ya kalli wurin zaman Fadila, ya rubuta sunansa sannan ya rubuta Fadila Ahmad Musa.

Bayan kammala lectures, malamin ya ƙirga ɗaliban ajin, ya ga mutum ɗaya ya hau kai, aikuwa ransa ya ɓaci, ya ce "Waye ya rubutawa wani attendance? Kowaye ya faɗa kafin in binciko shi da kaina".

Yazeed ya miƙe tsaye cikin jin kunya ya ce "Ni ne Sir".

"Wa ka rubutawa?" Yayi shiru.

Malamin ya kalli Attendance É—in ya É—ago ya kalli Yazeed ya ce "Yazeed Hashim Sharif, Faidla Ahmad Musa, da kai da ita kun rasa wannan 30mrks É—in".

Tana ƙarasawa ƙaramar tashar garinsu, ta tarar an fara lodi, kasancewar fuskarta sanye da niƙabi ne, babu wanda ya gane wacece, ta samu wuri ta shimfiɗa ɗankwalinta ta yi sallar asuba, daga nan ta shiga motar da za ta kai ta babbar tashar ƙaramar hukumar su.
Gari da sauran duhu, haka suka ɗauko hanyar barin ƙauyensu, babu abin da Amina take a zuciyarta sai Addu'a, da fatan Allah ya kaita lafiya ba tare da kowa ya ganta ba.

Ƙarfe bakwai suka isa babbar tasha, ta shiga tambayar direbobin nan Saminu, tare da yi musu kwatancen sa, wasu suka ce ba su gane shi ba, wasu kuma suka ce sun gane shi, amma ya kwan biyu bai shigo tashar ba, ganin gari na cigaba da haske, ya sanya ta fara tsoron kar a biyo sawunta, dan haka ta shiga motar da ake lodin Kano!.

Haka tayi ta rarraba ido, kamar agola a rabon gado, tana kallon hanya, tare da mamakin manyan gine gine da tituna da ababan more rayuwa da suke shimfiɗe a maraya, yayin da ƙauyuka ko oho, banda yau da Allah ya sa ta fito maraya ta gani da idanunta, da sai ta ce ƙaryane a garin Kano babu irin wannan manyan ababan more rayuwar, duba da yadda rayuwar karkara take da wahala, saboda rashin isar da ayyuka yadda yakamata har karkarkara.

Sai da suka yi kusan tafiyar awanni biyu cir a mota, sannan suka iso babbar tashar mota ta kabuga da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.

Ware idanunta tayi a kan manyan motocin da ke shiga suna fita a cikin tashar, wadda ta sha banban da tashar su ta ƙauye, sai a yanzu ta gane tayi wauta, ta ina zata fara neman Inda Baba yake? Ga Saminu ya ce mata yana Ikko, amma yau zai ƙaraso, to idan ya ƙaraso ina za shi? Nan Kano ko can gida? Gaba ɗaya ta rasa abin yi, ga jikinta babu daɗi, cikinta sai hautsunawa yake, saboda yunwa da kuma doguwar tafiyar da suka yi ta mota wadda ba ta saba ba. Ta samu can wani wuri a ƙarƙashin wata bishiya, ta rungume kayanta tayi zamanta tana kalle kalle.

Saminu kuwa cikin dare suka sauka, dan haka washegari da safe baccinsa ya kwanta ya sha hankali kwance saboda gajiyar tafiya. Sai wajen sha biyu saura ya tashi yayi wanka kasancewar juma'a ce, ya shirya dan ya fara biyawa ta gidansu Amina, ya sanar mata da saƙon Baba sannan ya ce ta shirya su haɗu a tasha washegari da safe, ba tare da sanin a ranar za a ɗaurawa Aminan Aure ba.

Ko da yaje gidansu Amina, sahsensu ya nufa ya tsaya a bakin ƙofa yayi salama, aka amsa masa tare da bashi izinin shiga. Sai dai yana shiga yayi tozali da Inno a zaune, idanunta sun yi jawur sun kumbura, sai ajiyar zuciya take yi, ga mata duk a zazzaune a kusa da ita.
Chapter 13 · 0% Book details