← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 90

Sashe 90

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A ɓangaren diyana kuwa sun gama shiri tsab sun nufi Airport ita da Aunty farida da junior dan zuwa kano sai murna diyana keyi yau zata ga yaya Aryan.

Karfe 2:20 limamin babban masallacin juma'a ya miƙe ya fara sanar wa kamar haka

A yaune dubbanni jama'a suka saidai É—aurin Auren (Safras Abubakar Saraki tare da matar sa hiyana Ahmad)
(Aryan Abubakar Saraki tare da matarsa diyana Ahmad) (Khalid Usman saraki tare da matarsa Fatima Zahra Abubakar Saraki) (Yusuf Abubakar Saraki tare da matarsa lamrat Ahmad) (Fahad Abubakar Saraki tare da matarsa Amrat Ahmad) a sukwane gaba ɗaya matasan Abba suka miƙe lokachi guda kamar abun haɗin baki, chikin tashin hankali Aiman ya dafe saitin zuchiyarsa murya na rawa ya fara magana

"Abba karka min haka wlh ni nake son diyana ba Aryan ba tun lokacin da nafara ganin ta na kamu da matsanan chin Son ta ban samu daman faÉ—a mata ba sai shekaran jiya kuma wlh Abba diyana ni take so ba Aryan ba dani take soyay...bai karisa maganar ba ya yanke jiki ya faÉ—i kasa bai ko shura ba, a sukwane dukkan su sukayi kansa suna kiran sunan sa ban da Aryan da Bgs Aryan kam yama rasa me zai che ji yayi duniya na juya masa tunani ya shigayi anya zai iya hakura da diyana kuwa? kai gaskiya ba zan iya ba, Bgs kuwa yama rasa ta ina zai fara magana a kan abun da Abba ya masa É—agowa Abba yayi zaiyi magana kenan sai yaji karar wayarsa daga aljihun sa
Alama ya yiwa Aryan da ido akan yazo ya chiro wayar jiki ba kwari Aryan ya kara so yasa hannu ya chiro wayar Abba daga aljihun sa, ganin sunan my first born ne ya bayyana a kan screen É—in wayar hakan yasa Aryan yin picking call É—in da sauri tare da manna wayar a kunnen sa

daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tafara magana chikin tashin hankali "hello Abba na diyana ta ɓata wlh bamu gan taba nan na barta zaune da junior sai dai na dawo na samu junior da kuma mayafin ta da ɗan kwalin da jakar ta, Abbana da alama sache ta akayi wlh nashiga uku" chikin fushi da tsawa Aryan ya fara magana " Aunty farida daman yarinya nan tana wajen ki!? Daman ashe za'a iya haɗa baki dake a chutar dani!?why zakimun hakan!? Why!?
"Aryan yanzu dai duk ba lokachin yin wan nan maganar bane kaji pls kusan abun yi da wuri idan ma sache ta akayi to kuyi sauri fara neman ta tun wayan da suka sache ta basu yi nisa ba"
Chikin tsarkewar murya yace "yanzu dai kiyi sauri ki bar wajen ki É—auki junior ku koma gida gani nan zuwa yana gama faÉ—in hakan batare da ya jira amsar taba ya katse wayar, sauri sauri ya chiro wayar sa daga aljihu ya fara kiran layin Shahram

Bugu É—aya Shahram ya É—aga tare da faÉ—in" hello sir" "Shahram ku shirya min jirgi zuwa Maiduguri yanzun nan nan da 10mnt zan zo yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran batare daya bi ta kan kowa ba ya fice daga masallaci, da alama ya manta dasu Abba yazo dan baya chikin hayyachinsa

Har ya kai wajen moton chin su sai kuma yaji wayar Abba dake hannun sa tana ringing, tsaki yaja tare da miƙawa ɗaya daga chikin sojojin sa wayar akan ya kaiwa Abba ansar wayar sojan yayi da sauri ya nufi chikin masallaci shi kuma Aryan ya shige chikin mota tare da bawa driven sojan umarni akan sutafi batare da bata lokachi ba sojan ya tada motar da gudu suka bar masallaci

Abangaren sojan kuwa yana shigowa chikin masallaci ya miƙawa Yusuf dake tsaye ta bakin kofa wayan Abba dake ta ringing tana neman ɗauki, ansar wayar Yusuf yayi ganin sunan Ammi ne yasa yayi saurin daga kiran chikin ruɗu da tashin hankali Ammi tafara magana "ranka ya dade kuyi sauri kuzo Allah yayiwa lamrat rasuwa, ai Yusuf bai san lokacin da yasaki wayar Abba ta faɗi kasa ba, a sukwane ya juya ya fice daga masallaci.

Ɗagowa Abba yayi yana kallon Bgs dake tsaye yama kasa magana mamaki ne ya kama Abba wai yau ɗaya daga chikin ƴaƴan sa ne ya suma amma Safras yake tsaye haka kamar ma bai san ana yi ba lallai yau da alama ran maza ya ɓachi sosai, chikin sanyin murya Abba yace "Safras kazo ka ɗauki Aiman ka kaimin shi mota mu wuche asibiti ko

kamar daman jira Bgs yake amasa magana Chikin fitar hayyaci da karfi yace "No Abba No me yasa zakamin haka kasan duk duniya ba wan da na tsani gani kamar yarinyar nan ni kwata kwata ma banson Auren ban son ganin mace kusa dani suna da rauni Abba wlh ka chucheni ka gama dani Ni ba zan zauna da itaba gaskiya dan haka na sak...✍️

To masu karatu nan na kawo ƙarshen book 1 masu son chigaba da karanta littafin duk karfin izzata Naira 300 kacal 👌 kuyi payment ta wan nan account din 3167987863 first bank Musa fatima zahra sai ki turo receipt ta wan nan number 09162620621 har kullun takuce Princess teema Star Lady more love

Akoi fa chakwakiya shin wanene zai hakura ya barwa É—an uwan sa diyana? Yaya Bgs zai karke da Abba akan hiyana? Shin inama diyana take waye ya sache ta? Me ya samu lamrat? Yaya ma komar Ahmad da hiyana? Yaya Fahad zai yi da Auren Amrat? Duk wan nan amsoshin suna Book 2 sai mun haÉ—u karku bari abaku lbr yanzu asalin wasan zai fara

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)

*Baby*
By (Mhiz innocent)
Chapter 90 · 0% Book details