← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 90

Sashe 76

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

playing na video yayi ya fara kallo yana murnushin, zuba mata ido yayi sosai yana kallon yadda ta zura hannu a riga tana kokarin chiro sarkan, bai ankaraba kawai sai yaka boobs nasa a waje daman shekaran jiya ya kawar da kansa bai san taya ta fitar da sarkan ba, ashe wayar sa ta ɗau komai, a sukwane ya chire video ya fita daga App ɗin san nan ya kashe wayar ma gaba ɗaya, ya ajiyeta a saman drawer gefen gadon, shiru yayi kamar mai tunani har barchi ɓarawo ta ɗauke sa batare da ya saniba.

Maiduguri

Aunty farida che kwamche kan katafaren gadonta ta tada kai da chikin yar dadyn junior, suna yar hirarsu yana shafa kyakkyawa kuma lallausan bakin gashin kanta
My farida magana mai muhimmanci nake son muyi dake fa amma kinzauna kinata zubamin shagoɓa

Aunty farida tace "Kai baby Allah kana da neman rigima to yanzu kafaÉ—i maganar mana ina jinka ae,
"Watoma nine nake da rigima ko? "Eh mana Allah my baby kafini iya rigima,
Kwafa dady'n junior yayi yana faÉ—in zamu haÉ—une yanzu dai magana mai muhimmanci nake son muyi bari mugama maganar zakiyi bayani "to shike nan na ji yanzu dai faÉ—amin me ka ke so muyi magana a kai
"Yauwa my farida to bani hankalin ki nan, nitsuwa Aunty farida tayi ta zuba masa ido tana kallonsa

"Wan nan yarinyar da kika zo da ita wlh ta shiga raina sosai dan Allah idan ba damuwa ki faÉ—awa Abba, ya taimaka ya bawa Auta bakura Auren ta,

zubur Aunty farida ta miƙe zaune,tana kallon face ɗin shi taga dai da gaske yake "aa my farida lfy kika miƙe haka ko dai yarinyar matar Aure che? To ai ko matar Aure chema bai kamata kiyi irin wan nan miƙewarba,
"Dady'n junior diyana fa Abba ya riga da ya mata miji wlh, dan da zamu taho har mun shiga mota zamu tafi, Abba yasake bina har chikin motar yamin kashedin kada na kuskura na bar diyana ta kula wani namijin, domin ya mata miji a É—aya daga chikin kanne na Amma bansan wanene daga chikin su ba, dan Abba'n bai faÉ—amin wanene ya bawa diyanar ba

Dogon numfashi dady'n junior yaja kafin yace "to shike nan, nima dai kafin na tambaya nayi tunanin hakan domin abun da mamaki ache yarinya kyakkyawa kamar wannan tafito daga gidan ku, dake chike da zaratan samarin nan, ache ba'a mata miji a chikin su ba abun, abun dubawa ne,
Aunty farida zatayi magana sai sukaji alamar motsi a palon kasa, kallon dady'n junior tayi shima ita yake kallo, a tare suka sauko daga gadon da sauri suka nufi waje

Suna saukowa palon kasa turus suka tsaya, suna kallonta da mamaki, Aunty farida tace "my diyana me kikeyi a nan ? Meyasa kika fito daga É—akin? Shiru diyana bata basu amsa ba tana zaune saman sofa tana kallon kasa ta buga uban tagumi,
juyowa Aunty farida tayi ta kalli dady'n junior, shima ita yake kallo, sake dawo da kallonta tayi kan diyana dake zaune ko motsi batayi, a hankali Aunty farida ta taka zuwa kusa da diyana tasa hannu ta ɗan taɓata tare da kiran sunan ta a hankali,
Firgigit diyana tayi tare da miƙewa, zuba mata ido Aunty farida tayi kafin tace "my diyana lfy kike zaune a nan? Tunanin me kikeyi haka kuma?
Tsuke fuska diyana tayi ta turo baki ta fara magana

"Aunty farida wlh na kasa barchine, kuma ina jin ajikina kamar yaya Aryan bai da lfy san nan kuma Allah idan na rufe idona sai in rinƙa ganin yaya Aryan yana faɗin, bakin ki kawomin coffee ba yau to munɓata, Allah Aunty farida ina son ganin yaya Aryan, kewar shi nake

Tirkashi turus Aunty farida tayi tama rasa me zatachewa Diyana, domin iya gaskiya diyana tafaÉ—a dan bata karya, amma bansan meyasa Abba zai yankewa yaran nan irin wan nan É—anyen hukunchin ba gashi diyana ta kasa barchi, kuma ina da tabbachin shima Aryan É—in yana chikin damuwa.

ganin Aunty farida tayi shiru alamar ta tafi duniyar tunani ne yasa dady'n junior ya dubi diyana yace
"jeki É—aki ki kwanta ko da safe da kaina zan kai ki wajen yaya Aryan kuma ki daina tunanin ko bai da lfy, lafiyan sa kalau sharrin sheÉ—an ne yasa kike ganin kamar bai da lfy, kije kiyi addu'a ki kwanta kinji, to kawai diyana tace san nan ta nufi É—akin ta,

Hannun Aunty farida dady'n junior ya kama suka nufi stair É—in suka koma É—aki,
"My farida wai meke faruwane?, ko dai Aryan shine mijin da Abba yayi wa diyana
"Dady'n junior wlh nima abun yafara ɗauremin kai, nan dai Aunty farida ta shiga bashi lbr duk wani abun da ta sani dan gane da yaya Aryan da diyana, ta karisa maganar dai dai lokachin da suƙe hawa kan gadon su,

"Kinsan me my farida, batare daya jira amsar taba ya chigaba da chewe "Abba yana da gaskiya domin kinga dukkan kannen namu basu taɓa soyayya ba hasalima basu ɗauki mace da daraja ba, ganin ta suke kamar abun banza, wlh a irin wan nan yanayin da suke chiki idan aka ɗauki mace aka basu to ta shiga uku domin basusan darajar taba zasu wahalar da ita sosai, yanzu dai ki dubi yadda Aryan ke masifar son yarinyar nan batare da yasan Son nata yake ba amma duk dahaka daga ɗan magana dasu Umar sukayi, ya fusata har yaje ya samu Ammi ido da ido yace bayason ganin diyana kinga a nan ma rashin sanin darajar mace ya bayyana karara, a tare dashi, wlh gwara da Abba ya masa hakan, kuma ku barshi sai ya gasu sosai sai yasan mace fa halittace mai daraja wadda kowani ɗa namiji ke son kasan chewa da ita, ku kyalesa sai ya furata da bakin sa chewar yana Son ta, in ba hakaba ko an musu aure ran da su Umar suka sake mai maita abun da sukayi shima sake mai maita abun da yayi zai yi. da katawa yayi da maganar yana mai da numfashi,

"Kana da gaskiya dady'n junior wlh rashin sanin darajar macece har yasa Aryan ya iya tinkarar Ammi ya faÉ—a mata hakan, to amma abun tausayin a nan shine ita diyana yanzu dai da kunnen ka kaji halin da take chiki, tana son Aryan sosai Amma itama batasan chewa Son nashi takeba, saboda kaga ita yarinya che kuma gashi ba wani ilimin ke gareta ba ita ko kallon film batayi sai dai buga game kawai, ta iya

"Hakane my farida dolene diyana ta zama abun tausayi amma ke zaki jata a jiki domin ki rinƙa rage mata, kewar nashi kada ki bari ta rinƙa zama ita kaɗan, gobe idan Allah ya kaimu zan saya mata sabuwar waya mai kyau sai kisa Sim naki a chiki, ki mata download game's dayawa, idan kin gama ki chire Sim ɗin, san nan kema kiyi taka tsantsan da wayar ki dan kinsan gaba ɗaya kannen ki basa iya yin wuni ɗaya batare da sun kira ki ba, kada ki kuskura ki sakawa diyana Sim card a wayar ta, domin a yadda kika bani lbr na fahimci yariyar akoi kwakwalwa sosai, dan haka sai kinyi taka tsantsan da ita sosai

"To shike nan dady'n junior zanyi duk yadda kace Saboda nima ina kaunar diyana sosai kamar yadda nake kaunar Aryan, bazan so taje gidan mijin da bai san darajar ta ba, zanyi iya bakin kokarina wajen ganin, na bata kulawa na chanza mata abubuwa da dama

"Good my farida hakan yayi to yanzu dai mu kwanta muyi barchi kinga dare yayi ma karisa maganar gobe idan Allah ya kaimu,

atare suka kwanta ta shige chikin kirjin sa ta lafe shi kuma yana shafa bayan ta har barchi ya É—auke su.

Kano

Tun misalin karfe 6 su hiyana suka gama shirin zuwa school, yaya Khalid kawai suke jira yazo ya É—auke su.

sai misalin karfe 7:30 yaya Khalid yazo ya tasa su a gaba suka fito harabar gidan suka nufi parking space, yau da kanshi ya tuƙa su a family car,

Gudu yake shararawa da motar sosai akan shin fiÉ—aÉ—É—iyar hanyar school nasun, chikin kan kanin lokaci suka isa makarantar,kai tsaye parking space na ya nufa yana kashe motar, ya fito a gurguje ya yana faÉ—in "kufito ku tafi class dan kun kusa makara, yana gama faÉ—in hakan ya nufi office na HM na makarantar, domin naje ya biya musu kuÉ—in makaranra.

Abangaren su hiyana kuwa yaya Khalid na tafiya suma ko wace ta kama hanyar class nasu, amma kallo ɗaya zaka yiwa hiyana kasan tana cikin matsanan chiyar damuwa ga blue eyes natan nan duk sun kunbura da alama tasha kuka, dan dai ita ba mai yawan kallon mutane bane kullun kanta na kasa shiyasa mutun ba zai gane kunburin da idon nata sukayiba, tazo dai dai zata shiga class nasu, taji daga bayan ta an che "ke zonan chikin tsiwa, da sauri ta juyo, ganin....✍️✍️

More comments an share
*💫STAR LADY💫*32

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3️⃣2️⃣*

Da sauri ta juyo ganin jabir ne yasa ta ƙara ɗaure fuska sosai, ta sunkuyar da kanta kasa, "my hiyana me ya same ki kikayi kuka? Chewar jabir Ya yi maganar yana matsowa kusa da ita, ɗan ja da baya kaɗan tayi kasa kasa tace "ina kwana, batare da ya amsa gaisuwar nata ba ya sake mai mai ta mata tambayar daya mata da farko "me yasa meki ki kayi kuka? waya taɓamin ke?
Chapter 76 · 0% Book details