← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 90

Sashe 82

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye take a gaban miro tana waya da hajj sadiya
"Haba hajj sadiya wlh nache miki ban san ya akayi hakan ta faruba Amma dai zan sa musu ido yanzu" daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace "to wlh hajj Hajara gara tun dare bai mini ba kisan abunyi, bakiga da gagarabadau ya kirani faɗan da yake tayi bane yace wai tayaya za'ayi muyi sakachi har wata tana kokarin kunche masa aiki, kuma yache wlh yarinyar bazai iya yimata komai ba shiyasa da taje tana kokarin yiwa shi Ahmad ɗin addu'a aljanun suke ihu sun kasa yimata komai,saboda askar ɗin datake, idan bamuyi da gaskeba tofa tana gab da kunche aikin nan kuma tana kunchewa inba muyi saa ba to kan ɗaya daga chikin mu zai dawo.
Dafe kirji Aunty amarya tayi kafin tace "munshiga uku hakan ma bazata faruba wlh in dai Hiyana che daga yau bazata sake shiga in da Ahmad yake ba zan mata iyaka da shi, ba zan bari ta ƙara koda ganin saba"

"Yauwa hajj Hajara kiyi kokari dan Allah" "to kawai Aunty amarya tace sanna sukayi sallama ta ajiye wayar saman mirrow ta chigaba da gyara fuskar ta, tana tunanin yadda zata ɓullowa hiyana

To jama'a kwanaki sunja lokachi ya tafi a yau diyana ta chika sati 1 da kwana 3 a gidan Aunty farida Maiduguri

Yauma kamar kullun ta tsara kwalliyar ta kamar yadda ta saba tayi kyau sosai ga wani giba da ta É—anyi sosai ta chiko ta ko ina, shap nata ya kara bayyana ga wani kyau da fatar jikin ta ya yayi, ya kwanta sumul sumul kamar fatar jariri, sai kyalli take ta ko ina, sanye take chikin wani haÉ—adÉ—iyar wandon jeans blue da t-shirt baki, ba karamin kyau kayan suka mataba sun zauna a jikinta sosai ta saki lallausan bakin gashin nan nata har gadon baya sai sheki yake, ta baza takartun makarantar ta a tsakiyar babban palon kasa tanayin home work, sai faman taunar chingum take kas, kas, kas, abunta

Da sallam ɗauke a bakinsa ya shigo palon, a sukwane diyana ta ɗago kai dan voice nashi da tayi, da sauri ta miƙe ta nufesa tana faɗin ƴa...✍️

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*💫STAR LADY💫*34

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3️⃣5️⃣*

.........da sauri ta miƙe ta nufesa tana faɗin "yaya Aryan kai... Bata kai karshen maganar ba ta ɗakata kuma chikin sauri ta dakata daga nufarsa da take, jiki ba kwari ta juya ta koma wajen books nata ta zauna ta dukar da kai ta chigaba da abun da take.
A hankali chikin nitsuwa ya fara magana "me yasa kuma kika juya kika fasa karasowa" batare da ta É—ago ta kallesa ba tache "saboda kai ba yaya Aryan É—in bane, da mamaki Aiman ke kallon ta, chikin mamaki yace "ya akayi kika iya gane chewa ni ba Aryan bane? bayan ko iyayen da suka haife mu in dai ba tare suka ganmu ba, basa iya banbanta mu, sau dayawa Abba na kirana da sunan Aryan haka zalika ya kira Aryan da sunana muna kama sosai bamu da wata bambancin"

Cikin sauri batare da ta É—ago ba tace "wlh kuna da banbanci sosai ma kuwa,
Karisa shigowa yayi cikin palon ya zauna saman sofa mai zaman mutun 2 yana faÉ—in "to menene bambanci namu?, Har lokachin diyana taba É—agoba tana duke da kanta tana ta rubutu a chikin book nata, shikuwa Aiman ya kafeta da Ash eyes nashi sosai yake kare mata kallo

Kanta na kan takar dar da take rubutu tafara magana "yaya Aryan ya fika dogon hanchi, hanchin sa siririne sosai, san nan yafi ka manya manyan ido kuma shi idon shi yayi kalar ash sosai, sannan yana da É—igon baki a ta gefen sagen sa, bakin sa yayi red sosai, kuma yafi ka dogayen yatsun kafa, gashin kansa yafi naka tsantsi da kuma baki, kuma... Bata karisa maganar Aima yace "ke ya isheni haka, a yaushe kika kare mana kallo har haka kuma shi Aryan ya fini komai ke nan? Ni babu abun da na fishi?"

Still dai bata É—ago kanta ba tace "aa yaya Aiman, akoi abubuwan da kafishi mana sosaima, gyara zama Aiman yayi kafin yace "ok ina jinki faÉ—amin ni kuma dame dame na fishi"
"Kafishi katon hanchi mana domin shi yaya Aryan hanchin sa, siririne kuma dogo sosai kai kuma naka dogone amma kuma kato, san nan ka fishi katon kafa, shi kafarsa karamine kai kuma naka kato, ka fishi katon kai, ka fishi jiki, kuma muryan yaya Aryan, É—an siririne kai kuma naka iri na wanchan yaya Umar É—in ne kato kuma .... "Ke dalla kiyi mani shiru idan muryana katone ya akayi dana yi sallama kika kasa gane ba Aryan bane? Ya akayi lokachin da kika É—ago kika ga fuskata baki gane ba Aryan bane? sai da kika zo kusa dani

"Ai saboda ina sunkuye da kai na kasane ne shiyasa naga kamar yaya Aryan ne, wlh da ina a tsaye ne na ganka bazan che yaya Aryan bane, saboda kuna da banbanci sosai kuma ai don na daÉ—e banji muryan yaya Aryan bane shiyasa naji kamar shine"
"Ok to ya isa ina Aunty farida" "Aunty farida bata nan taje shopping" "waya miki kwalliyar nan" ya tambaya yana kare mata kallo from head to toe, sai lokachin diyana ta ɗago kai chikin zumuɗi tace "ni nayi yaya Aiman, nayi kyau ne? "Murmushi yayi kafin yache sosai ma my sister, ai daman ke kyakkyawa che, da sauri diyana ta miƙe ta dawo kusa da shi ta zauna tafara magana

"Yaya Aiman kasan me, batare da tajira amsar sa ba ta chigaba da magana "yan school namu kowa chewa yake wai ina kama da laraba ina da kyau sosai" "eh mana sister ai gaskiya suka faÉ—a miki kinma fi larabawa kyau ai" murnushi tayi sosai wadda yasa har dimple nata ya lotsa, shi kuwa Aiman ya zuba mata ido kawai yana kallonta daga samma har kasa

"Yaya Aiman ina yaya Aryan yake? ya akayi kazo kai ka É—ai? "Abba ne yace nazo Aunty farida nason ganina, san nan kuma yaya Aryan yana gida" "to yaya Aiman ka kiramin shi awaya inason yin Magana dashi" "ok kawai Yaya Aiman yace san nan ya fito da wayarsa daga aljihun wandon jeans dake jikinsa, ya kunna hasken screen É—in wayar, ya shiga contact yana neman layin yaya Aryan.

Da sallama Aunty Farida ta shigo palon hannunta riƙe da manya manyan ledoji shopping, da sauri Aiman ya ajiye wayar sa ya miƙe ya nufi Aunty farida ya ansa mata ledojin yana faɗin "Wellcome Aunty babba" "Aiman ka iso kenan? "Eh yanzu na shigo,

Zama sukayi saman kujera É—aya mai daman mutun 3, nan suka fara gaisawa

"Yaya Aiman kazo ka kiramin yaya Aryan É—in mana" chewar diyana, waro ido waje Aunty farida tayi chike da mamaki tache "ke wani yaya Aryan É—in kuma wato yanzu diyana duk maganar da namiki bata shiga kunnen ki ba koh?
Turo baki diyana tayi chikin shagwaɓa tace "kiyi hakuri Aunty farida na mantane shiyasa, amma ba zan sake ba" subhanallah ido kawai Aiman ke binta dashi yama kasa magana kawai kallon ɗan karamin bakin nan nata yake baya majin me take faɗe shidai bakin kawai yake kallo.

"To tashi ki kwashe books nakin nan ki mai da ɗaki kizo mu shiga kichin yau da kaina zan yiwa yaya Aiman girki kizo kema ki tayani, da sauri ta miƙe chike da zumuɗin zata shiga kitchin yau.

tattare books nata tayi ta maida chikin jaka ta É—auki jakar ra nufi stair É—in.

KANO

wani zazzaɓi mai zafin gaske ne ya rufeshi, sai rawan sanyi yake, ga ash eyes nashin nan sun chanza sunyi jaa sosai gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi, zaune yaƙe saman sofa ya dafe kansa da hannu ɗaya, yayi shiru kamar mai tunani.

Almost 10mnt yana wan nan yanayin, a hankali yasa hannun ya É—auko wayarsa dake gefe guda, kunna hasken wayar yayi ya chire password É—in san nan ya shiga contact, layin Aunty farida yayi dealing ya fara kira, ringing É—aya Aunty farida tayi picking tare da faÉ—in "hello Aryan"

Da kyar ya iya buÉ—e baki, baka jin voice nashi ma sosai ya fara magana "Aunty farida y kk" , subhanallah! Aryan baka da lfy ne? Yana ji voice naka haka? Tayi maganar a ruÉ—e "Aunty Farida Abba da Ammi suna neman kasheni da kansu" "A uzubillahi!! haba Aryan me suka maka haka? har zakache suna neman kasheka"
"Aunty farida sun ɓoyemin matata wlh ina sonta ina san ganin ta, ina chikin damuwa Abba yaki faɗamin in da take Ammi kuma bata isa ta faɗamin ba saboda dole tabi umarnin Abba, pls Aunty farida kisa Abba ya dawomin da ita in dai ba so kuke ku kashe niba, kin san yadda nakeji a chiki zuchiyata kuwa? Ya karisa maganar chikin rau'nanniyar murya

Wani irin farin cikin Aunty farida taji, jitake kamar ta zuba ruwa a kasa tasha dan daÉ—i yau Aryan da bakinsa yake faÉ—in zai iya mutuwa a kan mace, lallai diyana kin chiri tuta waiii, jin Aunty farida tayi shirune yasa yace "Aunty babba ko kema kina bin bayan Abba ne? Da sauri tace "a'a Aryan yanzu kasan ya zamuyi kaje ka sanar da Abba kana sonta kuma Auren ta zakayi nan ba da dadewa ba, nasan kana faÉ—a masa haka zai dawo maka da ita"
Dogon numfashi yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin yace "No Aunty farida ni bazan faÉ—awa kowa ina sonta ba kema na faÉ—a mikine dan keche sirrin mu kuma pls kada ki faÉ—awa kowa, har sai É—an uwana ya samu matar da yakeso shima sai a haÉ—a Auren nu lokachi guda.
Chapter 82 · 0% Book details