← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 90

Sashe 36

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin karfe 10 na dare Aryan Aiman yusuf Ahmad Khalid suna zaune a palon hotel ɗin da suka sauka hirasuke gaba ɗayansu ban da Aryan daya zauna shiru kamar bashi a ɗakin " Khalid ne ya ɗan taba shi " a ɗan firgiche ya ɗago ash eyes ɗin nan nasa yana kallan khalid " lfy meke damun ka gaba ɗaya naga kamar mood naka ya chanza chewar Khalid " iska mai zafi Aryan ya fuszar daga bakinsa kafin yasoma magana babu komai kawai inatunanin intashi inje induba prince ne naga wunin yau shiru banji motsinsaba " satar kallan yusuf Khalid yayi san nan yace ok to kaje kadubashi mana " mikewa Aryan yayi yanufi staircase ɗin ya haura sama " murmushi Yusuf yayi yana kallan Khalid " harara Aiman ke wugawa yusuf tare da faɗin me kuke kullawa " shima Yusuf yadawo masa da harara yana faɗin mekuma zamu kulla " tsaki Aiman yaja san nan yamike yana faɗin zakusani dai kubi a hankali dankuwa idan ta kwaɓe muku kunsan sauran " kallan sama da kasa Khalid yawa Aiman san nan yaja tsaki yace. To kayi rashin sa'a nine babba ba kaine babba a kainaba dazaka tsaya kana faɗamin zanchen banza ni wuche kabani waje hai " tsaki Aiman yaja san nan ya wuche yanufi staircase ɗin " dawo da kallansa Khalid yayi kan Ahmad dake zaune ya zuba musu ido to kaima mekake jira dabaka'wuche kabi husainin nakaba " dariya Ahmad yayi san nan yace gulma natsaya jimana ai yau munraba gari da husainin nawa dannikam sainaji gulmar " Khalid bai sake maganaba sai daima yachiro wayarsa yafara neman layin Zahra " wayar nafara ringing yamike yana chewa Yusuf kasameni a ɗaki san nan yawuche " mikewa Yusuf ɗinma yayi ya kyale Ahmad awajen yanufi staircase ɗin shima kai tsaye ɗakin Khalid yanufa da sallama yashiga zaune yasamu Khalid yana waya da zahra, hannu kawai Yusuf yasa ya amshi wayar kana yasa akunnensa yana jiyo hayaniyar, kannen nasu " ina my baby abunda Yusuf yace da zahra ke nan " da sauri zahra tace gatanan tamikawa lamrat wayar " hello yaya Yusuf ina wuni " lunshe ido Yusuf yayi san nan yabuɗe yana faɗin lfy my baby ya school " alhamdulillah lamrat tabashi amsa " shiru yaɗanyi kafin yafurta tsarabar me kikeso inkawo miki " babu komai yaya Yusuf Allah dai yadawo daku lfy shine fatanmu chewar lamrat " bakaramin daɗi Yusuf yajiba azuchiyarsa yafa tunanin yarinya karama da hankalin manya yana chikin tunani yajiyo muryarta tana faɗin allah yaya Yusuf kewarka nake sosai da sosai " sake lunshe ido Yusuf yayi yana murnushi farinchiki kasa kasa yace my baby nima nayi missed naki sosaifa " a shagwabe tace to yaushe zaku dawo " Yusuf zaiyi magana Khalid ya amshi wayar yana faɗin inyamaka zafi kasaya mata nata wayar yayi maganar tare da mikewa yanufi waje " murnushi Yusuf yayi san nan yafurta nice idea yana gama faɗin haka ya haye gadan Khalid yayi kwanchiyarsa

Khalid kuwa yana fita kai tsaye ɗakin Aryan yanufa da sallama Khalid yashiga Aryan baya ɗakin dan haka khalid yafito yanufi ɗakin DON da sallama yashiga zaune yasamesu kan kadon, suna fuskantar juna da alama magana mai muhim'manchi suke " jin sallamar Khalid yasa dukkansu suka juyo suna kallansa " ƙarisa shiga chikin ɗakin Khalid yayi shima ya haye gadan ya zauna a nutse yafara magana
Aryan wai meke damun kane naga gaba ɗaya yau ka chanza ne gashi ka ɗan rame kamar baka da lfy chewar Khalid " daga green eyes nashi sama DON yayi kamar mai kallan wani abu kamar kuma mai tunani " zuba mishi ido Aryan da Khalid sukayi suna kallansa " jimkaɗan ya sauke kansa tare da furzar da iska daga bakinsa ya tsare Aryan da ido sosai yake kallansa " nantake Aryan ya mike kamar mara gaskiya yana kokarin sauka daga gadon kamar daga sama yaji muryan DON yana faɗin me kake ɓoyemin ashe akoi abunda bai kamata nasaniba a dangane da kai, kodai matsayina bai kai bane " jin maganar DON yasa Aryan saurin juyowa yana kallansu shiru yaɗanyi kafin nan yace. Taya kake tunanin akoi abun da zan boyemaka dangane dani kai'nefa ni kuma nine kai SO bawani abun boye boye a tsakaninmu wlh kawai bana jin daɗine ni kaina bansan meke damuna ba kwata kwata nakasa samun nitsuwa " shin akoi wani abu mai mahim manchin daka rabu dashine dazaisa kakasa nitsuwa DON yajefo ma Aryan tambayar bazata " aa nikuma ina dawani abu mai muhim'manchi dayawuche kune ai kune kawai masu muhim'manchi a rayuwata " Khalid dai ido kawai yake binsu dashi yadda suke maganar burgesa suke DON akoi kokolwa sosai akoi basira Aryan kuwa akoi wayau sosai shiyasa haɗin nasu yake bada chitta " barchi nakeji kaina chiwo yake min zanje na kwanta chewar Aryan yayi maganar tare da juyawa yachigaba da tafiya har yakai bakin kofa sai yaji muryan DON yana faɗin idanma baka faɗamin yanzuba nasan dole gaba zanji ai " shiru kawai Aryan yayi bai tankaba saima kara sauri dayayi yabar ɗakin

Dawo da kallansa DON yayi kan Khalid yana faɗin akoi abun dake damun ɗan uwana tabbas ba lfy yakeba " murmushi kaɗan Khalid yayi a zuchiyarsa kuwa yace baridai ya ɗan latsa DON yaji yazasu kare ajiyar zuchiya ya sauke san nan yadubi DON yace kasani kodai yafaɗa soyayyane " a zafafafe DON yace what ? hauka yakene kataɓa ganin yana magana da watane ma NO hakan ma bazai yuwuba " mamakine yakama Khalid ganin daga maganar mace DON ya sauya kamar bashiba " nantake ya kara ɗaure fuskar nan kamar baisan me dariyaba Khalid yayi nisa chikin tunani muryan DON takatse masa tunani " Khalid i said get out " kallon DON Khalid yake da mamaki ba musu ya sauka daga gadan dan yasan halin DON yanzu idan yace zai biye masa sai abun yakai'su ga ɓachin rai " fitowa Khalid yayi daga ɗakin DON kai tsaye yanufi ɗakin Aryan

Da sallama yashiga zaune yasamu Aryan a tsakiyar gado " ba karamin mamaki Khalid yayiba ganinsa zaune karisawa chikin ɗakin yayi ya zauna a bakin gadon " sai lokachin Aryan ya juyo yana kallansa " lfy bakayi barchiba aryan Khalid yajefo masa tambaya " iska mai zafi ya furzar daga bakinsa calmly yafara magana nasaba da shan coffee kafin nayi barchine Khalid dazun nayi order coffee sun kawomin amma ɗan ɗanon bai minba kwata kwata na gida nake buƙata shiyasama kaga nakasa barchi " hannu Khalid yasa a aljihun wandansa ya ɗauki wayarsa yafara kiran layin zahra dan kuwa yanzu yagane matsalar Aryan " bugu ɗaya Zahra ta ɗaga tana faɗin yaya Khalid ɗazun muna hira ka gudu " yanzu me kuke bakuyi barchiba Khalid yajefo mata tambaya " karatu mukayi amma yanzu zamu kwanta ai tabashi amsa " ok ina diyana " gata nan inbatane chewar Zahra " eh bata yayi maganar tare da mayar da wayar a H-free " ansar wayar diyana tayi chikin voice kamar mai jin barchi tafa magana yaya Khalid shine baka nemeniba tun ɗazun inajin kana magana dasu zahra inasu Ammi " suna lfy allah sarki na mantane amma ai gashi yanzu na nemeki Koh " yauwa yaya Khalid daman inasan in'tambayeka chewar diyana " ok tambayi " wai a chan makkan wake kaiwa yaya Aryan coffee " jin tambayar nata yasa Khalid ɗago ido yana kallan Aryan shima Aryan ɗin shiyake kallo " dawo da kallansa Khalid yayi kan wayar san nan yace bari nabawa yaya Aryan ɗin sai ki tambayesa Koh bai jira amsar taba yamikawa Aryan wayan " ba musu yasa hannu ya karɓi wayar yana sauke ajiyar zuchiya " Khalid na mika masa wayar ya mike yace kuyi magana inazuwa yana gama faɗin hakan yafiche daga dakin da sauri yana murmushi

Calmly Aryan yafara magana hello " ina wuni yaya Aryan chewar diyana " wani murmushi Aryan yayi kafin tace lfy y school " alhadulillah tabashi amsa " good yace saikuma sukayi shiru dukkansu " chankuma sai diyana tace yaya Aryan wayake kawo maka coffee a makkan " murmushi ya ɗanyi kafin ya burta babu kowa " yanzu ke nan bakashan coffee ɗin " eh bana sha yabata amsa a takaice " Allah sarki da ina nan dana rinƙa kawoma ai " Aryan baimasan san da dariya ta kubche masaba dan yadda ta furta Allah sarki bakaramin dariya tabashiba amma sai ya danne dariyar yace ashe kinaso na bansaniba ashe kina tausayina " aa bana sonka inadai tausayinka chewar diyana " to meyasa bakisona " shiru ta ɗanyi san nan tace kai'ma ai bakasona ne shiyasa nima bansanka " to wayace maki ni banasonki " Allah yaya Aryan basai anfaɗaminba ni da kaina nasani baka sona dan inkana sona bazakache zaka harbeni da bindiga namutu kowa yahutaba " shiru yayi yana tunanin sai yanzu yagane kuskurensa namata barazana da hakan shi yamata chikin wasa itakuma ashe tarike a matsayin gaske yayi nisa chikin tunani sai yaji tana faɗin yaya Aryan sai da safe su zahrafa har sunyi barchi sun kyaleni " ok kawai yace da ita san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya kwanta bajimawa barchi tayi awon gaba dashi

Lokachin da Khalid yadawo ɗakin dan karɓar wayarsa yasamu aryan yayi barchi murmushi yayi a'fili yafurta ai daman ninasan meyahanaka barchi kai da kanka kake neman kashe kanka anfaɗa maka SO wasane ganin Aryan yana ɗan motsi yasa Khalid ɗaukan wayarsa da sauri yayi waje yana murmushi

Washe gari dawuri suka tashi sukayi shirin zuwa school kamar yadda suka saba haka suka fito yauma kai tsaye wajen motochinsu suka nufa da gudu drivers É—in suka karaso wajen budemusu motochin drivers É—in sukayi
Su diyana Suka shiga suna shiga drivers É—in ma suka shiga da gudun gaske suka tada motochin suka bar gidan gudu suke sosai chikin kan kanin lokachi suka isa school É—in awajen dasuka saba parking sukayi yauma fitowa su hiyana sukayi suka jera zuwa wajen tsayuwa suyi hira kafin a shiga class " drivers kuma suka shiga motochin suka juya suka koma gd
Chapter 36 · 0% Book details