← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 90

Sashe 59

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a tare driver's ɗin su kawa motocin key da matsakaicin gudu suka bar Airport ɗin suna fita suka karawa motochin gudu, gudu suke sosai chikin ƙan kanin lokachi suka iso security suka wangale mugu katafaren gate ɗin, a hankali su ka kutsa motochin chikin gidan, kai tsaye parking space suka nufa, suna kashe motocin DON yafito da sauri bai bi ta kan kowa ba yanufi ɓangaren'sa da sauri Aryan ma ya nufi ɓangaren'sa don bai san kowa ya lura da jinin diyana dake jikin rigar sa dan rigar ma launin ta ba mai haske bane, Khalid da Yusuf kowa yanufi ɗakin sa, Ammi da bataliyar ta suma suka nufi nasu ɓangaren.

*DUK ƘARFIN IZZATA*

👑UK Writers👑

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 24*

A gurguje Aryan ya karisa ɓangaren sa, kayan jikinsa yafara ragewa, ya rage da gashi sai shot ya nufi toilet dan yin wanka, after 45mnt yafito ɗaure da towel ya nufi gaban morrow, wayar sa dake saman drawer mirrow ya ɗauka yafara kiran layin Aunty farida, budu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗin "hello bro, "Aunty babba pls ki turomin yarin yar nan bari na dubata "ok bari na kawota da kai na dan bazata iya tafiya ba tana ganin jiri, batare daya sake magana ba ya katse kira da sauri sauri ya shafa mayu kan sa masu kamshi da tsada feshe jikinsa yayi ta haɗaɗɗiyar parfume nashi mai shegen kamshi da tsada, gyara haɗaɗɗen kuma lallausan bakin gashin kanna nasa yayi, ya ɗaure a bayan ya zuba jelar gashin a bayan wuyar sa sai kelli gashin keyi,

zubawa mirrow sosai ido yayi yana kallan kansa, shiru yayi kamar mai tunani, jin motsi a pallo ne yasa ya juya da sauri yanufi dressing room nashi dan shiryawa,

da sallama Aunty farida ta shigo É—akin rike da hannun diyana sai faman lumshe ido take, ganin É—akin ba kowa yasa Aunty farida tace "my diyana jeki zauna a saman sofa ki jirashi kinji, "to kawai diyana tace tanufi sofan da kyar take tafiya saboda sarawan da kan ta ke mata, Aunty farida kuwa juyawa tayi ta fice daga É—akin,

Zama diyana tayi ta jingina da jikin sofar ta kwantar da kanta ta lumshe ido kamar mai barchi, Almost 12mnt tana zaune shiru,har barchi yafara É—aukar ta, wani fitinannen kamshi ne ya daki hanchin ta wadda yasata sauri waro ido karaf blue eyes nata suka sauka cikin ash eyes nashi, tsaye yake sanye da jallabiya Black colour zuba mata ido yayi sosai yake kallonta, da kyar ta iya buÉ—e baki tace "ina wuni yaya Aryan, juyawa yayi batare da ya amsa ba yanufi wajen drawer

A box ya ɗauko ya dawo kusa da ita ya zauna,spirit and cotton ya fitar yafara mata dressing wajen, chikin shagwaɓa da murya kamar na mai kuka tace "yaya Aryan zafi ya'kemin sosai ta karisa maganar tana turo baki, subhanallah wani irin shock yaji saboda yadda tayi maganar, zuba mata ido kawai, yayi ya dakata da aikin da yake har takai karshen maganar, da kyar ya iya sai ta tunanin sa, ya buɗe baki murya kasa kasa kamar mai raɗa "sorry kinji dole zai miki zafi amma zan miki a hankali,

Sake turo baki tayi tana faɗin "to ni kawai kabari tun da akoi zafi "kinfi san ki zauna da chiwon ke nan, gyaɗa masa kai tayi alamar eh "bakisan yin kwalliya ke nan, da sauri tace "a'a inasan kwalliya "to in baki tsaya an miki magani ba to fiskan ki zai ɓachi bazaki rinƙa kwalliya ba, chikin marairai chewar murya tace "to ayya yaya Aryan kamin a hankali kaji wlh akoi zafi, ta karisa maganar kamar zatayi kuka, shiru yayi batare daya sake magana ba ya mai da hannunsa kan goshin'ta ya chigaba da dressing na wajen,

sai mutsu mutsu diyana keyi taki tsayawa zafi wajen ke mata sosai nan take tafara ruwan hawaye, dafe kansa yayi da hannun sa É—aya yana faÉ—in "kinsan ban san kuka ko kiyi shiru ae nakusa gamawa kinji, gyaÉ—a masa kai kawai tayi amma bata dai na hawaye ba "wai ba ke che kika che zaki auri soja ba,ya tambaya yana kallan face nata, da sauri ta É—aga masa kai alamar eh "to ai matan sojojin jarumai ne basa kuka, cikin shesshekar kuka tace "Allah yaya Aryan zafi yake yi mini ne shiyasa amma na daina kukan ta karisa maganar tana goge hawayen ta, girgizar kai kawai yayi ya chigaba da aikin sa sauri sauri yake mata dan karta chigaba da kuka bai san kukan nata ko kaÉ—an,in tana

Bayan ya kammala ya mai da komai ya rufe Box ɗin ya ajiye a gefe ya miƙe ya koma bakin katafaren gadon sa ya zauna yana kallan ta, sai faman yamutsa fuska take tana turo ɗan bakin. "me ya haɗaki da wanchan wawan mutumin har ya bugeki haka, yayi maganar yana ɗaure fuska , dama kamar jira take tafara bashi lbr tun shigan ta gidan da yadda ya buga mata sandar duk sai data bashi lbr komai, tun da tafara magana ya kafeta da ash eyes nashin nan, ya kasa chire idon sa a kant, yadda take motsa lips nata nan jiyake kamar yamiƙe yaje yayi kiss na lips ɗin ko zai samu sauƙi abun da yake ji a zuchiyar sa, da sauri ya kori sheɗan ta hanyar furta a'uzubillahi minasshe ɗanir rajin kafin yace "to daman tun asali me tsaka nin ku kuna da dan gantaka da shine, "aa bamu da dan gan taka ɗan yayan Inna che, "what kara waro ash eyes nashi yayi sosai a kanta, nan take ya ƙara ɗaure fuska rai a ɓache yace "to daman kun taɓa samun matsala da shine a baya da har yake ikirarin zai kashe ki, "eh kullun idan inna ta aike mu ɗiban ruwa sai ya tare mu ya zubar mana da ruwa, nan dai diyana tashiga bashi lbr duk abun da yataɓa haɗa su da buba from A to Z har fyaɗen da yaso yayi mata,

shiru yayi, nan take fuskar sa ta sauya kamanni idon sa suka sauya su kayi jaaa sosai, lokachi guda, a fusache ya furta "fyaɗe, a tsorace diyana ta gyaɗa masa kai alamar eh gaban sai faɗuwa yake dan ganin sauyawar yaya Aryan lokachin guda gawani huchi da yake duk jijiyoyin kansa sun tashi sosai, gawani zufa da yake kamar ba A.c a ɗakin jikinsa har wani tsuma yake gaba ɗaya ilahirin jikinsa ɓari yaƙe gashin hannun sa duk sun mimmiƙe,Sai faman chizan red lips nashi yaƙe da karfi kamar zai fasasu, kamar alluran sojan nashi ne ya tashi, nan take matsanan chin tsoran sa ya dira mata a rai, tunani ta shigayi anya bazan tashi in gudu ba kuwa karya bugeta,

dafe hannun sofa tayi ɗakyar tamike wai dan ta gudu kar ya bugeta, cikin tsawa ya furta "ina zakije, jikinta sai kerma yake chikin wata iriyar voice kamar zatayi kuka tafara magana "dan Allah yaya Aryan kayi hakuri karka bugeni wlh ni bana san duka kaji ta karisa maganar tare da sakin wani marayan kuka mai ratsa zuchiyar mai sauraro, runtse ido yayi dan har chikin zuchiyar sa yake jin kukan nata, ya dafe kai,dan bai san kukan data keyi ko kaɗan sassauta sexy voice nashi yayi calmly ya fara magana "nache zan bugeki ne kimin shiru ki koma ki zauna, "yaya Aryan to kishi nake ji ina san in sha ruwa, Slowly ya waro ash eyes nashi a kan face ɗin ta, sai hawaye take wani na bin wani "ok jiki ɗauko ruwa a freij kizo, to kawai tace san nan tanufi palon tana jan kafa a hankali, ido ya zuba mata yana kallonta sosai har ta fice daga ɗakin, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke, kana yasa hannunsa yana yamutsa gashin kansa, wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa a hankali yafara magana "Aryan wai meke damun kane meyasa na kesan yarinyar nan ta rinƙa kasan chewa kusa dani, yanzu dache ta zauna me zan bata,anya ina lfy kuwa? meyasa nake ɓata rai na dan wani ya taɓa chewa zai mata fyaɗe? Meyasa zan bugi malamin makaranta su dan yache bazai dai na Son taba? why me ruwana da ita, shiru ya ɗanyi kamar mai tunani,
Chapter 59 · 0% Book details