← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 90

Sashe 74

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai dai wajen part na Ammi sukachi karo da su Zahra sun fito daga palon Abba.
Ganin Bgs da yaya Aryan yasa diyana ta fasa ihu ta watsa a guje ta shige ɓangaren Ammi, da gudu hiyana tabi bayan ta, su Zahra ma ba'a barsu abaya ba da gudu suka wache suka bi bayan su hiyana.

"Bgs gaskiya baka kyauta wa yanzu dan Allah dubi yadda yaran nan suke ihu da suka ganka kamar sunga dodo, wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace "bana son haka Aryan ka daina kawomin maganan yaran nan, "ai gaskiya na faÉ—a maka bro menene anfanin kasa su suna jin tsoronka, shiru Bgs yayi bai sake magana ba har suka karisa chikin fada

Misalin karfe 11 :20 Aryan ya fito daga fada ya nufi part nashi dan ya je yayi wanka yazo dai dai part na Ummi sai yaji haidar da Umar suna hira tsayuwa yayi da kyau ya kasa kunne yana jin su,

"Umar ai wlh ko baka faÉ—aba kowa yasan Son yarinyar nan yaya Aryan yake, bakaga yadda yake kallonta ba idan mun haÉ—u wajen chin abinchi,

"kai haidar kai kallo kawai ka gani ka dubafa yau saboda ita yaya Aryan yayi faɗa da yaya prince, ai mugu mugun Son ta yake, wani dariya Umar yayi kafin yace "tab aiko zamuga ya, yaya prince zai yi idan yaji lbr yaya Aryan ya faɗa soyayya dariya suka kwashe a tare har da riƙe chiki,

A fusache Aryan ya juya ya fasa shiga part nashi ya nufi part É—in Ammi sai wani huchi yake, chikin ransa yana faÉ—in soyayya ni wai aa never wlh har abada.

da sallama yashiga palon bb kowa kai tsaye betroom É—i ta ya nufa, a bakin kofa ya tsaya yayi sallama, Ammi na daga chiki ta amsa masa tare da bashi izinin shigowa, shiga yayi ya zauna saman manya manya throw pillow dake tsakiyar É—akin
"Aryan lfy kuwa naga ranka a ɓache haka, "Ammi so nake yarinyar nan ta bar gidan nan "wace yarinyar kuma? "Wan nan yarinya dake kawomin coffee "au diyana? "eh ita ban son sake ganin ta gaskiya, yana kaiwa nan ya miƙe ya fita rai a ɓace, miƙewa Ammi tayi itama ta ɗauki alkyabban ta ta sanya ta fito ta nufi fada

Da sallama ta shiga ta karisa wajen Abba ta zauna saman kujera tana masa sannu da hutawa "Aisha lfy naga kamar ranki a ɓache? Abba ya tambaya yana kallon face nata, Ammi bata ɓata lokachi ba wajen sanar da Abba abun da Aryan ya faɗi

a tunanin ta Abba zai ɓata rai sai kuma taga yana murmushi ya ɗauko wayar sa dake gefensa yafara kiran layin Aunty farida,
Bugu É—aya Aunty farida ta É—aga tare da faÉ—i "hello Abba na "my daughter ki zo fada yanzun nan ki sameni, yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran,

baifi minti 5 sai ga Aunty farida ta shigo da Sallama har kasa ta duƙa chikin girmamawa ta gaida Abba da Ammi, da fara'a dukkansu suka amsa, "zauna my daughter muyi magana chewar Abba
Miƙewa Aunty farida tayi ta kowa saman kujera ta zauna ta zubawa Abba ido tana sauraron taji mai zai che "so nake yanzu ba sai anjima ba ki ɗauki diyana ku koma Maiduguri da ita, kuma karki kuskura ki sanar da wani tana wajen ki koda Aryan ne ko zai miki tambaya dubu idan ki ka kuskura ki ka sanar da shi to ban yafeba. Sai da Abba ya daka ta da magana sannan Ammi ta fara magana

Ranka yadaÉ—e me yasa zaka che hakan? "Aa Aisha ku kyaleni tun da har Aryan bai ji kunyar idon ki ba yazo yace baya son ganin yar É—an uwanki to wlh sai nayi maganin sa, "tayaya zakayi maganain sa to? Ai naga shi yace bai son ganin ta to kaga idan ta tafi ai sai yafi kowa murna da hakan "Aisha ke nan yanzu kina nufin bakisan chewa Aryan na Son diyana ba, to idan ma baki sani ba yau kin sani, kuma So bana wasa yake mata ba "amma yana Son ta kuma yace baya son ganin ta a gidan nan?

"Kedai ba ruwanki kuyi abun da nache muku wlh duk wadda tasake ta faɗi inda diyana take to sai na ɓata muku, kutashi kuje, my daughter yanzun nan ku tafi kuma karki bari kowa yaga kin fita da diyana, "to kawai Aunty farida tace sannan ta miƙe tanan murna sosai dan ambata diyana atare suka fito fada da Ammi

Yola

Ihu take tana faÉ—in nashiga uku na ku kawo min agaji zan mutu, da gudu yaya bello ya fito daga chikin gonar sa ya nufi gonar bappan su dan daga nan yake jiyo ihun,

"Subhanallah innar buba lfy? Chikin ihu da kuka innar bubu tace "Bello mutuwa zanyi na shiga uku kumurchin machijine ya sareni a kafa, chikin sauri bello ya kai kallonsa kan kafar nata, gaba É—aya kafar ta kunbura sundum, girgiza kai Bello yayi yana faÉ—in "shike nan dafin yagama shiga jikin ki wlh ko kinsha magani yanzu ba lallai ki chigaba da takawa da kafar ki ba, dan dafin ta riga ta illata namar kafar taki

"Bello ka taimake ni mutuwa zanyi wayyo Allah, da gudu yaya bello ya juya ya koma chikin gonarsa ya tsinko wasu ganye ya nufi rafi ya wanke su tas, san nan ya É—auko wani É—an kwarya, ya dawo wajen innar buba, murje ganyen bello ya shigayi chikin kwaryar sai da ta fitar da ruwa san san nan ya bawa innar buba, ruwan akan tasha ganyen kuma ya manna mata awajen chizon machijin.

Tana shan maganin ta fara amai, amai sosai ta amayar da dafin machijin, amma kafar ta kuma har yanzu a kunbure yake gashi yayi wani green dashi, ɗaukan kwaryar yaya Bello yayi ya koma rafin ya ɗebo mata ruwa ya dawo ya bata tasha, san nan ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗar sa ya nufi hanyar gida

Da sallama ya shiga gidan hasana na tuƙa tuwo ganin yaya Bello ɗauke da innar buba a kafaɗar sane yasa hasana miƙewa da sauri ta ɗauko ta barma mai kyau daga ɗakin ta ta shin fiɗa a tsakar gidan.

A hankali yaya Bello ya kwantar da innar buba a kan ta burman, san nan ya dubi hasana yace "kiyi sauri ki kammala abinchin ki zuba mata, to kawai hasa tace Sannan ta miƙe ta koma wajen girkin nata, innar buba kuwa sai hawaye take saboda azabar da kafarta ke mata,

Masu karatu na muku wan nan ɗan takaitaccen page ɗin ne saboda nasan kuna chikin zullumin ya diyana da Bgs zasu kare, shayasa na muku amma gobe ba update sai Monday shiyasa ma ban tsaya awajen da zaku shiga tunani ba 😸😻

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

More comments an like pls

*💫STAR LADY💫*

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3️⃣1️⃣*

Aunty Amarya che zaune a bakin gadon ta tana waya da hajj sadiya

"To yanzu hajj sadiya ya ki kayi dashi ne nifa wlh na matsu, banson ganin yaran nan a gidan nan, daga É—ayan bangaren hajj sadiya tace "haba hajj hajara sai kace yau muka fara aiki da gagarabadau, ki kwantar da hankalin mana yanzu zan miki bayani ai tun da ki kaga na kiraki kam kema kinsan akoi bayani "to hajj sadiya ki faÉ—amin da wuri mana dan na matsune naji ai

"Jiya naje wajen sa, yana faÉ—amin chewa Aiki na tafiya yadda ya kamata, dan yache ma akoi wani shu umin malamin da basu san daga ina yake ba yana taimaka musu sosai, shima yana bibiyar rayuwar yaran ne, ahalin da akechiki yanzu yama kusa kunche tsarin dake jikin yaran saura kaÉ—an, amma fa yace ita babban wlh ba wanda ya isa ya mata wani abu asiri ba zai kamata ba, aljanu ma bazasu iya shiga jikin taba, dan tana karatun qur'ani tana askar, bata wasa da sallah kuma tana sallan dare gashi bata shiga harkan kowa, yaso shiga jikin ta last month da tana period ma amma sai dai kas bai yi nasara ba, domin duk da tana period, tana askar, kuma tana zama da alwala,ba ta yadda zaiyi ya shiga jikinta, su kuma sauran nan da two weeks, malin Chan in ya gama kunche tsarin jikin nasu, yana gama kunchewa shikuma gagarabadau zai É—aura nashi aikin a kansu
Dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace "to shikenan Allah ya kaimu "amin Hajj Hajara karki damu ke dai ki kara hakuri saura kaÉ—an yauwa baki bani lbr sabon sarkin ku ba ya ake chiki? " Hmmm ke dai hajj sadiya bari wani sarki wlh ranan da ya fara hawa kujerar mulkin nan tun ranar ya fara rashin lfy baya magana baya motsi, sai dai numfashin sa kawai da zakiji shine zai tabbatar miki da bai mutuba abun gwanin ban tausayi,
Wani shewa hajj sadiya tayi ta chikin wayar kafin tace "ai albishir ya kamata kimin hajj Hajara kiche aikin gagarabadau yayi kyau,
zubur Aunty amarya ta mike muryar ta har rawa yake wajen faÉ—in "hajj sadiya kenan ke kikayi wa Ahmad wan nan abun? ke nan daman ba chiwon Allah da annabi bane ya kamashi? tsaki Hajj sadiya taja kafin tace.

Kamar ya ni na masa, ke dai kika masa ba niba, dafe kirji Aunty amarya tayi ta zaro ido tana faɗin "ni kuma hajj sadiya a yaushe na masa hakan, "Hajj Hajara wai lfy ki?, watoma kin manta aikin da kika sani naje na sa gagarabadau ya miki akan, idan ba mijin ki ko ƴaƴan ki ba, ba wanda zai karɓi mulkin nan duk kuma wan da yayi kuskuren hawa mulkin tofa mutuwa zakiyi
Chapter 74 · 0% Book details