← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 90

Sashe 67

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

....BGS juyowa ya kalli Aryan,ba tare da yayi magana ba, chikin sauri Aryan ya juya ya ɗauko allura ya haɗa ba tare da Aiman ya Ankara ba Aryan ya tsira masa alluran nan take yayi shiru difff kamar an ɗauke wuta sai kuma ya sake wa BGS dukkan jikin sa alamun yayi barchi, ɗaukan sa BGS yayi chak ya saɓa sa a kafaɗa ya nufi waje da shi

Hannu Aryan yasa ya É—ago Ahmad daga kwanchiyar da yake ya zaunar dashi ya sa masa fillo a bayan da ya jingina shi da jikin bango yana kallon face nashi, ban da ido ba abun da ke iya motsi a jikin Ahmad, juyawa Khalid yayi ya bar É—akin dan zuchiyar sa ta gama karaya dab yake da fashewa da kuka

Aunty salma Aunty farida Aunty Mardiya hiyana sun fi kowa kuka a ɗakin shi kan shi Abba daure wa kawai yake, jiyake kamar yayi kukan shima ko zai samu sassauchi a zuchiyarsa, Ammi da Ummi sai sharan kwalla suke Aunty amarya kam bata wani damu sosai ba, dan ko kwallin hawaye bata yiba, sosai Aunty Maryam ma ta shiga damuwa dan itama har chikin zuchiyar ta tana son yan uwan ta, su hiyana ne dai bata so, Fahad ma daurewa kawai yake amma shima idon sa ta chika tab da kwalla, Haidar Umar sai kwalla suma suƙe dan gaba ɗaya ƴaƴan Abba suna matikar kau nar junan su, shiru Yusuf ya zauna dan shi tsabar tashin hankali ko hawayen ya gagara fita

"Hauwa'u ki tattara su gaba É—aya ku tafi kowa ta tafi ban garen ta kuyi shiru kukan ya isa haka, addu'a zaku masa chewar Abba yayi maganar yana kallon Ummi, jiki ba kwari dukka matan suka fita ya rage mazan

da sallam BGS ya dawo É—akin kusa da Abba yaje ya zauna suka zubawa Ahmad ido shima dai Ahmad É—in su yake kallon kamar zai yi magana amma ya kasa, cikin tsawa BGS yace "kai ku mana shiru yayi maganar yana kallon haidar da Umar, nan take suka goge kwallan idon su suka nitsu,

.....Dawo da kallan sa kan Abba BGS yayi kafin yace "Abba yanzu menen abun yi dogon numfashi Abba yaja kafin yafara magana "ina ganin mu fitar da shi waje kawai mu kai shi Us ko UK ko india tun da suna da kwararrun likitochi "aa Abba dan uwana ya fi karfin yaje wata gasa jinya sai dai ita kasar tazo ta same sa a nan, likitan wani kasa kake son yazo ya du bashi, zanyi waya koma wani irin likitane kake so gobe zai zo, "to ka kira likita daga India dan sunfi kwararrun likitochi chan "ok kawai BGS ya faÉ—a san nan ya mike ya nufi waje, mikewa Abba ma yayi yana faÉ—in "Aryan ka kwantar da Ahmad muje ko mu kwalesa ya huta, yana gama faÉ—in hakan ya nufi waje, juyawa Yusuf da Fahad su kayi suka bi bayan Abba haidar da Umar suka rufa musu baya

a hankali Aryan ya mai da Ahmad ya kwantar, san nan ya shafa kansa yace "Allah ya baka lfy my bro, abun mamaki gani Aryan yayi Ahmad ya lumshe ido a hankali ya buÉ—e alamar ya ji daÉ—in addu'ar da Aryan ya masa

.... A sukwane Aryan yace "Ahmad daman kana jin mu, lumsha ido Ahmad ya sake yi san nan ya buÉ—e alamar eh ina jin ku, a ruÉ—e Aryan ya zauna gefen sa ya riko hannun sa yana faÉ—in zaka iya buÉ—e bakin ka juya ido Ahmad yayi alamar a'a, "ok to shike nan bama sai ka buÉ—e baki ba tun da kana jin duk abun da nake faÉ—e, idan eh haka ne sai ka lumshe min ido idan kuma ba haka bane ka É—aga min ido sama kaji,? Lumsha ido Ahmad yayi ya buÉ—e alamar yaji "akoi in da yake maka chiwo ne a jikin ka? É—aga ido sama Ahmad yayi alamr aa "zaka chi abin chi? nan ma É—aga ido sama yayi alamar a'a bazai chiba, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin kunchin Aryan, wai yau Ahmad ne ke magana da ido kai duniya abun tsoro, É—aga ido sama Ahmad yayi alamar Aryan yayi shiru ya dai na kwalla, fika kai Aryan yayi kan goshin Ahmad ya chigaba da kwallar sa, hawayen sa na zuba kan fiskar Ahmad,
Sai da Aryan yayi kukan sa mai isar sa sannan ya É—ago yana bin Ahmad da kallo,

...hawaye kwanche a chikin idon Ahmad ɗin ga wasu na bin gefe gefen idon sa alamar dai shima kukan yake, girgiza kai Aryan ya shiga yi yana faɗin "No bro No bai kamata kayi kuka ba kaga baka da lfy lunshe ido Ahmad yayi alamar yaji, hannu Aryan yasa ya goge masa hawayen, san nan ya miƙe ya koma saman sofa daƙe chikin ɗakin ya zauna yana kallan Ahmad, shiru sukayi dukkan su har bar chi ya ɗauki Ahmad, ganin yayi barchi ne yasa Aryan mikewa ya fiche daga ɗakin daman ya zauna ne dan bai san ya bar Ahmad shi kaɗai.

Misalin karfe 9 na dare zaune Aryan yake a bakin katafaren gadon sa yana latsa waya, sanye yake chikin kayan barchi riga da dogon wando Sky Blue masu kyau da tsada, yayi nisa chikin abun da yake a wayar tasa, yaji wani fitinannen kamshin perfume ta kai mai karo a hanchi kan ya ɗago kai, sai yaji tafiya kwas,kwas,kwas, ai bai ma san san da ya saki wani cool murmushi ba tun bata karisa shigowa ɗaƙin ba,

ba ko sallama diyana ta shigo hannun ta É—aya rike da cup mai É—auke da coffee, É—ayan hannun nata kuma rike da jakar da ya bata amatsayin tsaraba, from head to toe yake kallan ta,

Sanye take chikin wata dan ƙareriyar lace Blue colour da ratsin fari, ɗinkin riga da sket kayan sun zauna a jikin ta sosai, yau ba ta yi make up sosai ba iya powder ta shafa sai man baki, tayi kyau kamar ita tayi kanta, ga ɗaurin dan ɗaurin ɗan kwali ture kaga tsiya da ta yi, yau kam ta rufe kan nata, gawani high heel fari da tasa a kafar ta sai wani fitinannen kamshin turaren humra dake tashi a jikin ta zubawa, a hankali take takawa tana wani rausaya ta kariso chikin ɗakin

.....gaban shi tazo ta duka har lokachin bai dai na kallan ta ba, yama kasa É—auke idon sa daga kanta "ina wuni yaya Aryan, wani dogon numfashi ya ja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya, kasa amsa gaisuwar nata ma yayi, jin bai amsa ba yasa ta É—ago kai a hankali, karaf blue eyes nata ya sauka chikin ash eyes nashi da sauri tayi kasa da kanta,

"yaya Aryan dan Allah ka ansa mana wlh chinyata na min zafi kayan sun matseni sosai ta karisa maganar kamar zatayi kuka, slowly yasa hannun ya ansa cup ɗin ita kuma ta miƙe, tana faɗin yaya Aryan ga jakar ka buɗe min ta karisa maganar tare da miƙa masa jakar, batare da ya ansa ba yasa ɗayan hannun sa ya mata nuni da kan drawar gefen gadon alamar ta zauna, ba musu ta zauna ta ajiye jakar a kasa a gefenta

"Bana hanaki kwalliya da daddare ba, yayi maganar yana ɗaure fuska turo dan karamin bakin nan nata tayi a shagwaɓe tace "to ai Aunty farida che tache nayi kwalliya nazo na kawo maka coffee, shiru yayi bai sake magana ba ya ɗago da cup ɗin sai tin ɗan bakin nasa ya fara sha coffee ɗin yana kallan ta, juyo da kallanta itama tayi kan sa, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke idon ta kasan chewar yana kallon ta

"yaya Aryan me yasa kayi kuka kuma meyasa naga ka rame, a'sukwane ya chire cup É—in daga bakin sa ya kara waro manya manyan ashe eyes nashi yana kallan ta, batare da ta kallesa ba ta chigaba da magana "ko É—azun fa da yaya Ahmad ya fara rashin lfy kowa a palon yayi kuka har da ni, nima nayi amma kai da wan nan mai kama da hiyana da kuma Abba ba kuyi kuka ba to yanzu kuma.....ba shiri ta ja birki bata karisa maganar ba saka makon hannun da Aryan yasa ya rufe mata baki, É—ago ido tayi tana kallansa zaro mata manya manyan ashe eyes nashi yayi ya É—aure fuska sosai da kakkausar murya yafara magana

Waya koya miki kallon maza? zaro blue eyes nata tayi sosai har sai da Aryan ya zame hannun sa daga bakin ta ba shiri, dan ganin idon nata yayi data zarosu waje kamar ta kara musu haske ne har wani kyalli suke, zuba wa kwayar idon ta ash eyes nashi yayi sosai yana kallan su abun ma mamaki ya bashi, ganin haka yasa diyana ta turo É—an karamin bakin nan nata tafara magana "ni bana kallan maza ni ba maza bama har mata dukka bana kallon su.
Chapter 67 · 0% Book details