← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 90

Sashe 13

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin karfe 5 na yamma jirginsu yayi landing a malam Aminu information Airport kano, wasu dan kare dan karan motochi 5 sukazo ɗaukansu ga motochi 3 chike da sojoji, basu wani ɓata lokachi a chikin jirgin ba suka fito tare suka jera, sai wani kara ɗaure fuska suƙe da ka gansu kaga wayan da akawa zuwa dole, musamman DON nashi daban ne, Abdol da Shahram suna biye dasu a baya,rike musu da trolley sojojin nan na ganin fitowar su suka jinro daga nasu motochin suka nufe su, Fahad na ganin fitowar su ya nufesu da sauri, yana ɗan murnushi hugging na DON yaje yayi yana faɗin "Wellcome back bro, hannu DON yasa yayi taying ɗin yana faɗin "missed U my blood "missed U too yayi maganar yana zare jikin sa daga jikin DON, yajuya yayi rungume Aryan ma, yana faɗin yaya Aryan nayi kewar ku sosai, rungume sa sosai Aryan yayi yace "nima nayi kewar ka sosai my blood, ganin DON yayi gaba ya barsu ne yasa Fahad ya saki Aryan da sauri sukabi bayan DON wajen motochin nasu suka nufa,nan take su Haidar suka fara musu sannu da dawowa ko kallan in da suƙe DON bai yiba bare su saran zai amsa musu, ya shige motar ya zauna yana yamutsa fuska, Aryan ma shiga mota yayi riƙe da hannun Fahad sai da suka zauna san nan ya dubi kannen nasu yace "yauwa to ku shiga mota muje gd koh sai mu gaisa a chan zaifi, da sauri suka koma chikin mota, drivers su kama motochin key da gudun gaske suka bar Airport ɗin gudu suƙe shararawa sosai a kan mikakkiyar titi, sai da suka kusa da bakin gate ɗin gida suka rage gudun motochin, batare da ɓata lokachi ba security daƙe tsaron gate ɗin su wangale musu gate ɗin a nitse suka kutsa chikin gd, kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin, Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar da gudu su kazo suka buɗewa DON da Aryan kofar motar, a nitse DON ya zuro kafafun'sa waje kafin ya fito gaba ɗaya bai bi ta kan kowa ba yanufi ɓangaren sa, Aryan ma ɓangaren sa yanufa riƙe da hannun Fahad suna tafiya suna hira, Yusuf ya karɓi trolley DON daga hannun Abdol yabi bayansa da shi Ahmad ma ya karɓi na Aryan daga hannun Shahram ya nufi ɓangaren Aryan ɗin, su Haidar kuwa kowa yakama kansa yayi part nasa

Ammi na zaune akan kujera a palan'ta tasha kwalliya chikin wata ɗankarekiyar lace baki da ratsin ja mai shegen kyau ga wasu gwala gwalan data zuba a wuya da hannu ta,ba karamin kyau tayiba inka ganta kace bata,wuce 25 years ba, Aunty farida tashigo da sallama ɗauke a'bakinta, da fara'a Ammi ta amsa mata sallamar, shigo chiki palon tayi ta zauna saman sofa mai zaman mutun 2,tana fuskantar Ammi "feeda dayake haka Ammi ke kiran Aunty farida feeda,ina junior yake "Junior yana wajen mardiya chewar Aunty farida " ok kawai Ammi tace tana kallan face ɗin Aunty farida "Ammi magana nakesan muyi dan Allah "ae feeda tun shigowar'ki Na fahimchi hakan, badamuwa ina jinki "Ammi daman, magana che a kan price, tun!bata kai karshen maganar ba Ammi ta ɗaga mata hannu, tana faɗin a'a feeda, kinsan dai bazan saka bakina a maganar bako,babu ruwana, dan kuwa kinsan mai martaba idan yayi magana baya chan'zawa "Ammi mun san Abba idan yayi magana baya sau'yawa, amma ae ke ki nasashi ya sauya magana koh, dan Allah Ammi, ki samana baki pls takarisa maganar kamar zatayi kuka "aa feeda babu ruwa'na wai ni ina ruwa da wani prince, ae wan nan ɗan Ummi ne ba ɗa naba kije kisamu Ummi ita tashiga masa amma ban dani "dan Allah Ammi kinfasan Abba yafi sauraren maganarki fiye da kowa a gidan nan" Feeda kin dai san in nache bazanyi abuba tofa bazanyin bane koh dan haka kibar maganar kawai,"to shike nan Ammi na barta barinaje namusu sannu da zuwa "baki Ammi ta taɓe tana faɗin eh lallai feeda ɗaure wa karya gindi,su da suke kannenki basu zasuzo su gaida kiba ke zakije ki gaida su lallai yaran nan suna abun dasu ka gadama
Aunty farida tamike tana faÉ—in kai Ammi kedai babu ruwan ki tsakanina da yan uwana ko inche yayyuna dan yanzu nabasu girma takai karshen maganar tana kokarin fita daga pallan bata tsaya ta jira amsar Ammi ba ta wuche abunta tana fita tayi part É—in DON

Da sallama tashiga palan nasa babu kowa, kai tsaye betroom É—in sa tanufa, yana tsaye gaban mirrow yana gyara gashin kansa,sanye yake da bakar jallabiya, da alama wanka yayi, jin sallaman ta yasa yaÉ—ago green eyes nashi ta chikin miron yana kallan'ta, batare da ya juyo ba "yace Aunty babba yanzu nake tunanin inje in ganki, kafin inyi barchi
Harara wasa Aunty farida ta wurga masa tana fadin "daka ganniba dole kafaÉ—i haka nasan da banzoba ba zuwa zakayi ka nemeni'ba, slowly ya juyo ya zuba mata green eyes nashi nan kafin yace "a'a Aunty farida ae kema kinsan dole na nemeki

Karisa shigowa chikin ɗakin tayi tai, a bakin katafaren gadansa dake shinfiɗe da White bet shit ta zauna tana faɗin,"to ya hanya "Tafiyar da bada san ranmu mukayotaba Tafiyar dole,ya kae karshen maganar yana ɗaure fuska , guntun murmushi Aunty farida tayi kafin tace, "hmmm yanzuma nagama magana da Ammi kafin nazo nan, kara ɗaure fuska yayi yana faɗin "ai dama baki mata magana ba, da baki ɓata bakin ki bama dan nasan baza ta saurare mu ba jinjina kai Aunty farida tayi kafin tache,mudaiyi addua karkadamu inshaa allah komai zaitafi yadda kakeso,tana kae karshen maganar tamike,bari na dubo Aryan, batare da ta jira amsar saba tayi waje dan tasan ba amsa war zai yiba,"juyawa yayi yachi gaba da abun daya'keyi

Tana fita ɓangaren DON tanufi ɓangaren Aryan bakin ta ɗauke da sallama tashi palon babu kowa a palon sai sanyi A.c dake ratsa jikin betroom nashi tanufa, sallama tayi a bakin kofar kafin ta tura kofar tashiga kwanche ta same sa akan katafaren gadansa,idon sa a lumshe da alama barchi,yafara ɗaukan, jin an taba kofar ne yasa ya buɗe idon'sa da kyar, yana ganin ta ya dan saki fuska yana da kyar ya buɗe baki da murya irin na mai barchi yace "Allah ya barmana ke aunty mu wlh naso nazo,na dubaki amma barchi ya hanani, murmushi tayi tana faɗin "an dawo lfy my tagar "lfy lau lovely Aunty "to bari na kyale kayi barchin ka daman dai ina san inzo inji an iso lfy ne tun da lfy ba wata matsala ayi barchi lfy sai mun haɗu awajen chin abinchin dare ahuta gajiya,tana kae karshen maganar ta juya tanufi waje juyawa yayi shima yana fuskantar gefen dama yachigaba da barchin daya fara"

Misalin karfe 8 nadare gaba É—aya family Abba sun haÉ—u a palon, dan chin abinchin dare, banda Aryan DON da kuma Fahad, sun zauna shiru suna jiran fitowar Abba, Ammi che ta katse musu shirun da chewa "nikoh meyasa mairo da salma basu zo bane kodai basu da lbr meeting martaba ya shirya
A tsiyache Aunty amarya tace ke Aisha kidaina ɓatamin su nan yarinya, kuma ina ruwanki da zuwar ta inba muna furchiba
"haba Aunty amarya daga tambaya chewar Ummi "ke Ummi baa kasa dake ba idan kemaÉ—in muna furchinne sai naji akule Aunty mardiya tache "a'a wlh ya isheki haka gaskiya bazaki zauna kina zagin iyayen mu, a gaban mu'ba tayi maganar tana nuna Aunty amarya ta hannu, hannu Aunty farida tasa ta É—an buge bakin Aunty mardiya, tana faÉ—in to ke ina ruwanki ae dukkan'su iyayen'mune wan nan fadar'sune tsakanin'su
Umar ya ɗago rai a ɓache yana faɗin "to ae gashi muma Aunty mardiya rashin kunya kike neman kiyiwa mahaifiyar tamu, A'kule haidar yache "haba Umar kai bakaji abun da Aunty amaryan ke faɗe bane, dafe kai Khalid yayi yana faɗin, to ya isa haka ae kuyi shiru, amma ina ba wan da ya saurari Khalid sunki yin shiru wan nan ya faɗa wan nan ya faɗa abun hat'tafara zama kamar faɗa
Dafe kai kawai Ammi da Ummi sukayi suna kallan ikon Allah kowa kokari yake yakare ma haifiyar'sa wan nan abu dame yayi kama" sai faman kache na che suke abu har ta fara zama kamar faÉ—a

Kamar daga sama sukaji gyaran murya daga bayan su nan take, sukayi tsit dan kuwa ko basu juya ba sunsan mai wan nan voice É—in tsaye yake a bakin kofar shigowa palon, yazura hannu a aljihun wandan,sa' yana kallon su fuskar nan tamkar batasan menene dariya'ba a daure take tam, a nitse yafara takowa izu chikin palon,wajen table É—in yanufa,da sauri Haidar yamike, yaÉ—an jamasa kujeran zaman, baya tayadda zaiji daÉ—in zama gaba É—aya matasan suka mike,ban da Khalid da Aiman da Yusuf jiki na kerma sukafara "faÉ—in sannu da fitowa yaya Aryan zama yayi batare daya amsaba yana binsu da ido jiki ba kwari suma suka koma suka zauna, murya na rawa Zahra tache "sannu da dawowa yaya Aryan
ko kallan in da take bai yi ba bai kuma amsa sannu nata ba ita ma,nan take kowa a chikin su yasha jinin jikin sa kallon fiskokin su yake sosai kamar mai karantar wani abu a tattare dasu
Chapter 13 · 0% Book details