← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 90

Sashe 71

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yallaboi ko dai zaku gwada maganin gida ne tun da na asibiti yaki chewar Dr yayi Maganar dai dai lokachin da yake É—aure hannun Ahmad dan neman jijiya,
wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace "Allah ya kyauta abawa É—an uwana wan nan dattin, zan nemo kwararrun likitochi daga kasa da ban da ban suzo su du bamin shi, "Allah ya baka hakuri sir, Chewar Dr ya karisa maganar dai dai lokachin da ya gama sawa Ahmad ruwan, ya tattara kayan aikin sa ya nufi waje

Kallon Bgs Aryan kafin yace "bro wai yanzu menene abun yi, shiri Bgs ya É—an yi kafin yace "ban yi tunani a kai ba amma muje zuwa anjima dole musan abun yi ya karisa maganar yana mikewa, mikewa Aryan ma yayi suka fita tare

Misalin karfe 2 na rana gaba É—aya family sun haÉ—u a palo dan chin abinchin rana ban da Bgs Aiman Fahad da kuma Ahmad, shiru palon ba abun da zakaji sai karan spoons

"My daughter ya kama ki koma gidan ki yau kinji, chewar Abba yayi maganar yana kallon Aunty farida, Mardiya salma Maryam dukka ku shirya kuma kuwuche gidan mazajen ku, "Abba daman gobe in Allah ya kai mu zan koma nariga na faÉ—awa dady'n junior ma chewar Aunty farida, chikin dashe war murya wadda da kaji kasan tasha kuka har ta koshi Aunty salma tace "Abba pls ka barni na kara koda 2dys ne sai mugani y jikin Ahmad É—in zai kasanche "a'a Salma ban yar da ba gobe idan Allah y kaimu kafin karfe 1 kowache ta koma gidan mijin ta, wai ma idan kuka zauna kara masa lfy zakuyi ne? Akoi waya duk abun da ake chiki zan sanar daku ai addu'a kawai yanzu ya ke bukata awajen ku bawai kubar gidan mazajen ku, kuzo ku zauna kusa da shiba,
Har suna haÉ—a baki wajen chewa to Abba Allah ya bashi lfy, gaba É—aya palon suka amsa da amin
shiru palon ya sakeyi ba mai magana kowa kawai tsakuran abin chin yake dan kamar magani suke jin abinchin ba dan daÉ—i suke chiba sai dan kar yinwa ta musu illatasu,

"My daughter kayan nan sun miki kyau Chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana, daman kamar jira take tafara surutu "Abba ai yaya Aryan ne ya bani ji, daman tare ya kawo mana da su Zahra shine ya kulle nawa chikin jaka, sai jiya ya buÉ—e min kuma Abba kaga wata dan kareriyar sar...bata karisar da maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna yaya Aryan yace idan ta faÉ—awa wani sai daketa, jin bata karisar da maganar ba yasa Aryan sauke wata nauyayyar Ajiyar zuchiya wadda yasa Abba É—agowa ya kallesa, kuma sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa diyana ta dakata da maganar bata karisa ba.

saboda jin baki irin na Abba sai yace

"My daughter ya kika dakata da maganar, a sukwane Aryan ya É—ago yana kallon Abba, harara wasa Abba ya wurga masa, da sauri ya mai da kai kasa yana É—an murnushi dan ya gano abun da Abba ke shirin yi, "babu komai Abba kawai dai na manta me zan faÉ—ane diyana ta faÉ—a tana satar kallon yaya Aryan,

mamakine ya kama Abba daman ya tambaye tane dan yaji shin diyana tayi hankali ne ko kuma dai da saura, abun da ya bashi mamaki kuma shine yau diyana che da karya abun da bata taɓayi ba tab lallai na yar da yanzu kam diyana na Son Aryan daman zargi kawai nake Amma bari dai na sake gwada su.

"My daughter ina malamin makaranta kun nan daya taɓa chewa yana Son kin nan?
Ɗaure fuska diyana tayi ta ɓata rai ta turo baki ta fara magana "to ai ni Abba bana son shi soja nake so kuma ai ni tun ranan ma ban sake ganin sa ba wata kila ma ya bar makarantar, kila kuma mutuwa yayi waya sanin masa, gaba ɗaya mutanen palon sai da sukayi mamakin ɗaure fuskantar da diyana tayi har shi kanshi Aryan dan tun da suke da ita basu taɓa ganin ta ɗaure fuska ko ta ɓata rai ba ita ko dukan ta akayi tana gama kuka zata koma dariya

"My diyana menene abun ɗaure fuska kuma? Ai ba wan da zai miki dole mijin da ki ke so shi zamu baki chewar Aunty farida "to ai Aunty farida ni bama wan da nake So sai yaya Khalid a sukwane gaba ɗaya jama'ar palon suka ɗago ido suna kallon ta musamman ma Aryan da atake idon nasa suka sauya zuwa jaa saboda kishi, itakam diyana bata ma san sunayi ba ta chigaba da magana "yaya Khalid yaya Yusuf yaya Aryan yaya Bello Aunty Zahra Aunty mardiya Aunty salma Abba Ammi Ummi Aunty amarya hiyana lamrat da amrat da ke Aunty farida sai Bappa na da Inna ta, ku kaɗai kawai nake so aduniya, wani ajiyar zuchiya Aryan ya saki, ya duƙar da kai ya ɗauki wayar sa dake gefen hannunsa kan table ɗin, yashiga latsawa

"Hiyana karfe 3 dai dai ki dama fura ki ka womin fada Chewar Abba yana magana faɗin hakan ya miƙe ya nufi waje,
Nmiƙewa Aryan Khalid Yusuf sukayi a tare suka fice daga palon, "haidar muje mu duba jikin yaya Ahmad ko Chewar Umar "eh ya kamata kam ya kai karshen maganar tare ta mikewa, mikewa haidar ɗin ma yayi suka nufi waje, a tare Aunty Salma da Aunty mardiya ma suka miƙe suka fice daga palon, Aunty maryam Aunty amarya suma tare suna mike suka fita, Ummi da Ammi kuwa betroom ɗin Abba suka miƙe suka shiga, palon ya rage daga aunty Farida sai su diyana.

"My diyana daga yau idan kinje É—akin yaya Aryan karki sake daÉ—ewa kina jina koh? Chewar Aunty farida, "to Aunty farida ai shi yake chewa in zauna muyi magana ta karisa maganar tana turo É—an karamin bakin nan nata

"eh ko yache ki zauna kiche kina jin barchi sosai, jiya fa har karfe 10 ina ɗakin ku ina jiran dawo warki, amma baki da wo ba, kamar zanzo na kiraki sai kuma nache bari na bari da safe sai na miki faɗa, "to Aunty farida ba ke ki kache idan naje ɗakin na rinƙa koya masa surutu ba tun da baya magana kuma kinche ni bazai bugeni ba ko na masa surutun "eh daaa ni nache hakan amma yanzu na fasa saboda idan namiji da mace suka keɓe to na ukun su sheɗan ne,duk da zan iya shedar kanne na a ko ina, amma dai daga yau kina kai masa coffee ɗin ki dawo kinji, "to Aunty farida kawai na daiii na kai masa coffee ɗin mana tun da hakane "aa karki dai na kai masa ki chigaba da kai wa kinji amma dai da kin kai sai ki dawo, "to kawai diyana tace tare da miƙewa ta nufi hanyar fita "kutashi muje Zahra, chewar Aunty farida, gaba ɗayan su, suka mikewa a tare suka nufi waje,

Karfe 3:5

Da sallama hiyana ta shigo fada hannun ta riƙe da kyakkyawar kwarya ta rufe shi da pai pai, ta sanya zumbulele hijabi har kasa ajikin ta fari tas, fiskar ta sai kyalli take bawani make up da tayi asalin kayan tane kawai,ga ɗan bakin nan nata pink sosai kamar tasa jambaki, geranta kuwa kamar tayi caving, idan mutun yaga hiyana zai rantse da Allah tayi make up, amma haka fuskar ta yake,halittar Allah ne duk da kwayar idon ta Blue ne amma idon nata farine tas manya manya kamar ball, kuma idan ta kalleka kache tasa kwalli amma ba ta saba haka idon yake gata da bakin kwanche cin gashi mai tsantsi a gaban goshinta ga wani baki haɗadɗen saje a kwanche a gefen kumatun ta dogon siririn hanchin nan nata kuwa baa magana har baka yake, duk lokachin da tayi murmushi sai wani haɗaɗɗen dimple irin na Bgs ya lotsa, ga hakoranta farare tas sai wani ɗan siririn wushirya a tsakiyan hakoranta na sama

a hankali take takawa kamar mahauniya, gaban kujerar Abba taje ta duƙa kasa ta, dukar da kai chikin ladabi da girmama wa tace "barka da hutawa Abba, wani murmushi Abba ya saki dan shi har chikin ran shi yana kaunar hiyana sosai akoi ta da ladabi da girmama na gaba da ita ga sanyin hali bata son hayaniya son addini ga sun katun boko da arabic dukka,

Da fara'a Abba ya amsa mata, san nan ta juyo kasa kasa ta kallin in da Bgs ke zaune tace "ina wuni yaya prince, bai amsa ba kuma bai ko kalli in da take ba saima latsa wayar sa da yake,chikin kwanchiyar hankali
Hiyana bata damu da rashin amsa gaisuwar nata da Bgs yayi ba, dan in da sabo sun saba da halin sa, "Abba ga furan ta faɗa tare da ɗago kai ta miƙawa Abba kwaryan dake hannun ta,
Ansa Abba yayi zai yi magana Bgs ya mike yana faÉ—in "Abba zanje É—aki sai da daddare, "aa Safras dawo ka zauna ai ban sallame kaba, ba don yaso ba hakan ba ya koma ya zauna dan ba yadda zai yi da Abba ne kuma ba zai iya yiwa Abban musu ba
dawo da kallon sa Abba yayi kan hiyana dake duƙe kanta na kallon kasa

"My daughter jeki kawo wa yayan ki nashi furan kinji, to kawai hiyana tace san nan ta miƙe da sauri ta nufi waje

"Abba nifa bazan sha wan nan abin ba Chewar Bgs É—in ya faÉ—a yana yamutsa fuska kamar wadda yaga kashi, "Allah sai ka sha, na dai faÉ—ama ni ba santin furar bane ya jani har nabi Ammin ku Yola na kasa samun kwanchiyar hankali sai da na Aure ta, kuma ita ta koyamin sha dan nima da bana sha É—in, "to Abba ai kai kache ba ni ba ni kam bana so kyama yake bani "koma me yake baka Allah sai ka sha na dai faÉ—ama ka, kasani ma ko daga sha.... Sai kuma Abba yayi shiru bai karisa maganar ba, dan yasan in ya karisa to wlh ko ya zai yi Bgs ba zai sha furar ba, shi daman Bgs ba wani sauraron maganar Abba yake ba kasan chewar yasa blooth a kunne É—aya,
Chapter 71 · 0% Book details