← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 90

Sashe 24

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kaya dayawa Aunty farida tafara ludan musu kuma tache suma suzaba duk abun dasuka ga yamusu su dauka " Zahra kam duk abun datagani mai dan kyalkyali sai tache wan nan zayyiwa Hiyana kyau ta dauka mata sunyi sayayyar kayan sawa dayawa san nan sukaje wajen takalma da jaka suma dayawa suka dauka suka koma wajen kana nan kaya Hiyana naganin breziya tafa boye fuska Zahra nata mata dariya
Aunty farida kuwa chewa take My Diyana kemafa kin kai sa bra ba Hiyana kawaiba dan kema naga ba bayaba wajen chikar halitta rufe fuska Diyana tayi da hannunta tana murmushi
Amrat ne tayi magana da fullanchi tache zata sha ruwa Aunty farida tache ku fassaramin metache " dariya Zahra tayi tache kai Aunty farida yakamata kema kikoyi fillanchi ruwafa tache zatasha
Aunty farida tache to daga yau hausa zamu rinka yimata dan itama ta iya hausar to waima ya akayi ku kuka iya hausa ita bata iyaba
Hiyana tache mu munazuwa tallan nono ne a chan akoi hausawa suna zuwa saye itakuma kullum tana gida tana aiki bata zuwa ko ina " a gida kuma ba mai jin hausa sai fullanchi kawai shiyasa bataji
Aunty farida tache to yanzu dai hausar za'ana mata har ta iya to kawai sukache san nan sukachigaba da sayayyar su
Bayan sungama daukan bra da pant suka wuche wajen dankunne da sarka nanma dayawa aunty farida ta dauka musu har da gold saida sukachika keken zuba kaya uku da kaya tukun nan Aunty farida tache ya isheku ne kokuma akoi wani abun dakukeso " da sauri Hiyana tache ya isa " Aunty farida tache aa kuduba da kyau dai " hiyana tache allah ya isa haka nan " Aunty farida tache to shike nan kutura kayan muje wajen biyan kudi harsun kai wajen biyan kudin kuma sai Aunty farida tache inazuwa chikin shopping din tashiga bangaren always tanufa ta daukoh guda 6 ta dawo ta zuba musu a chikin kayan
Diyana sarkin baki tache aunty menene wan nan kamar breadi Aunty farida tache nakine ke da hiyana da zahra kuma ba bread bane always ne " Diyana ta mai mai ta su nan always to me akeyi dashi ko chi akeyi diyana ta tambaya.
Aunty farida dai taga alamar kamar diyana bata fara period ba saitache mata inmunje gida ki tambayi zahra zata fada miki to kawai diyana tache
Nanfa aka fadamusu bill na kuÉ—insu Aunty farida ta chiro ATM nata tamikamusu suka chiri kudin san nan aka samusu kayan a leda Abdol yafara kwasan kaya shida yaran shagon suka kai mota
Aunty farida kuwa takama hannun diyana sukayi waje su Zahra suka rufa musu baya
Aunty farida tache Zahra da lamrat da hiyana suje su shiga motar da takawosu itakuma zata shiga motanta itada diyana da amrat . Tana kaiwa nan tashige chikin motar rike da hannun diyana amrat ma tashigo ta zauna kusa da diyana su
zahra kuwa suka nufi motarsu suka shiga nantake sojojin suka tada motochin suka nufi gida
Suna isa gida kai tsaye bangaren Ammi suka nufa a palo suka sameta nan suma suka baje kolinsu suka fara nunawa Ammi kaya. Ammi kam sai sannu da dawowa take musu tana sawa Aunty farida albarka takuma yaba kayan sosai tache su tattara suje su shiryasu a indaya dache, haka suka kwashi kayan sukayi dakinsu dashi

Aunty farida tadawo da hankalinta ga Ammi tache Ammi gobefa zan koma Mai duguri
Ammi tache ai naga wan nan karanma anbarki kindan dade " Aunty farida tache eh wlh shiyasa nakesan komawa dan kar a hanani zuwa sallah kinga azumi yakusa " Ammi tache ai garakam kikoma kije kikula damijinki yanzu dai kije ki kwanta ki huta a daki sai zuwa dare makarasa hirar
Mikewa Aunty farida tayi tana chewa to Ammi dan allah dai kiyi kokari kishawo mana kan mai martaba daya taimaka yabamu diyana da lamrat
Ammi tache to zanyi kokari . Betroom din Ammi aunty farida tashiga ta haye gadanta ta kwanta bajimawa barchi ya dauketa

Zaune suke a tsakiyar gado gaba dayansu hiyana tache aunty zahra dan allah inasan kifara koyamin karatu kinji lokachin muna kanana bappa yana koyamana karatu har munyi nisa danni har nakai izu 10 a karatun qur'ani kuma inasan in iya karatun qur'ani sosai
Zahra tache zan koyamiki hardana bokoma bana qur'ani kawaiba harda addoe dasu hadisai kuma akoi malamin dayake zuwa yana koyamin karatun islamiya kullum dayamma yanzu tare zamuna zuwa ya koyamana
Diyana tache yauwa nima inaso aunty zahra " zahra tache ai gabadayanku ma yazama dole kukoyi karatu yanzuma daga gobe zanfara koyamuku " harsuna hada baki wajen chewa to

Misalin karfe 8 na dare gaba daya family sun hadu a palan mai martaba
mai martaba da don da aryanne kawai basa wajen shiru kowa yayi daga masu daddanna waya sai wayanda sukayi tagumi suna jiran fitowar Abba
Aunty farida che ta kalli Fahad tache wai inasu prinse ne kullumfa sune suke bayan zuwa wajen nan " Fahad yayi shiru kamar bazai tankaba kusan 2mnt tukun nan yache nimafa tun dazun damuka rabu bansake shiga wajensuba
Ammi tache au ashe zaka tankamata ai nazachi bazakayi maganaba mutanene yadda kasan wasu kurmaye aimusu magana sunaji amma bazasu amsaba kukan wlh bakuji dadin halinkuba " Fahad dai shiru yayi kamar baijin me Ammi ke chewaba
Aunty farida tache kai Ammi hakafa akesan namiji yakasanche ba mai surutu barkataiba " harara Ummi ta watsawa aunty farida kana tache aidaman ke'ki'ke kara injizasu dan kuwa ke awajenki komai sukayi dai dai ne basa laifi " shiru aunty farida tayi bata tankasuba sai sukaji muryan mai martaba yanachewa aa karku dakurawa first born dina ku kyaleta haka nan irin wan nan faÉ—a haka
Ummi tache ai daman bakinku daya zama mai martaba yayi yana faÉ—in eh dai munji babu ruwanki farida dawo nan kusa dani
Mikewa Aunty farida tayi takoma kusa da mai martaba ta zauna
Mai martaba yache Amrat ummu waru ( amrat tashi kizo) mikewa tayi taje zaunar da ita mai martaba yayi a kujerar kusa dashi aunty farida kuma tache diyana taso kidawo kusa dani mikewa diyana tai takoma kusa da ita
Zahra'kam ko ajikinta dan ita koma kusa dawa zama zatayi amma yanzu da hiyana sukazo tare suke komai dan haka yanzuma suna zaune kusa da juna
Takun tafiya sukaji wanda kobasu juyaba sunsan takun manyan boss ne nantake palan ya nitsu tsit wasuma da kyar suke numfashi chiki har da zahra da umar
Su hiyana kam ko ajikinsu dan basumasan masu shigowarba
Kai tsaye kan table din suka nufa suna sanye chikin fararen jallabiya dukkansu sai kamshi sukeyi kamar anyi barin turare ajikinsu zama sukayi " don ya dauki bottle na ruwan dake kusa dashi ya bude ya tsiyaya ruwa a cup yasha san nan ya ajiye ragowar a kusa dashi nan take kannen nasu suka fara gaidasu amma babu wanda ya amsa a chikinsu saida kannen nasu suka gama gaidasune
Zahra ta dan zunguri hiyana tamata alamun ta gaidasu chikin gurbatatchen hausarta tache inawuni hamma basu amsaba kuma ko kallanta basuyiba
Diyana kam achikin zuchyarta tache wlh bazan gaishekuba mutane saikache wasu shadanu a muku magana bazaku amsaba kuma kuche inba amukuba zaku hukunta mutun to wlh nikam bazakumin hakan na daukaba yauwa dai dai nake da kowa

Saida palan yayi shiru san nan chikin nitsuwa don yache inawuni Abba mai martaba ya amsa da lfy " ya dawo da kallansa kan su Ammi suma yabisu É—aya bayan É—aya ya gaidasu
San nan aryanma yabi iyayen nasu É—aya bayan É—aya ya gaidasu
Shiru kowa yayi a palan sai aunty farida tachewa kuyangun dake tsaye a kansu dasu zubawa kowa rice an beans da sauri suka fara sarving nasu suna turawa kowa
Aunty amarya tache nikam bashi zaku zubaminba kuzubomin semo da miyar agusi
Bawanda ya tankata a palan sai aunty farida ne tache kuzuba mata mana tunda shi take raayi da sauri suka zuba mata suka mika mata
Suna chikin chin abinchi hiyana tafara shakuwa shakuwa yaki tsayawa hannutasa ta dauki cup din ruwan da don ya ajiye kusa dashi daya tana kusa dashi tafara sha kamar daga sama taji saukar mari a fuskarta har saida tamike batasaniba,dafe kunmatunta tayi da hannu tana kallansa hawaye nazuba daga fuskanta wani tsawa ya daka mata wanda yasata zurawa aguje tabar palan tayi sashen Ammi kowa na palan sai daya tsorata banda mai martaba da aryan
Aunty farida ne tayi karfin halinchewa haba prince meyasa zaka mareta bakaga yarinya bache kuma inkalura batasan ruwan shanka ta dauka bafa
Ko kallan aunty farida baiyiba barema yabata amsa abinchinsa kawai yachigaba dachi shiru palan yayi ba abunda kakeji sai karan spoon
Zahra kam jikinta sai rawa yake tanasan tashi tabi bayan hiyana amma tana tsoro
mikewa diyana tayi tabi bayan hiyana lamra naganin diyana tamike itama tamike da gudu tabi bayansu amrat zata tashi mai martaba ya riketa yache zauna yata kichi abinchinki karki damu
Kuka amrat ta pashe dashi tana fadin aa nakoshi nikam zanje wajen Aunty hiyana na " mai martaba dayaga haka sai yache zahra dauki abinchin naku kikama hannun amrat kutafi kuje daki kuchi a chan " da sauri zahra tamike ta dauki abinchin nasu takama hannun amrat sukayi waje
Chapter 24 · 0% Book details