← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 90

Sashe 31

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bangaren"su hiyana kuwa sunajin Aunty amarya tace umar yakai abinchin yayansu nantake suka fara murna sukamike a tare suna faÉ—in barimuje muyi sallah " Ammi ta kalli hiyana chikin harchen fillanchi tace wani sallah kuma badai kina period É—in kike sallah ba " shiru hiyana tayi dan ita batama san idan a na period baa sallah ba " ganin tayi shiru yasa Ammi ta dubi zahra tace kije ki koyamata abun daya dace tayi " to kawai zahra ta amsa dashi san nan suka fiche

Mikewa Yusuf yayi yana faÉ—in gaskiya lokachi yayi dazan koyi fullanchi nima haba yanagama faÉ—in haka yayi waje " Khalid ma yace tab aiko nima dole naje Zahra ta koyamin irin wan nan wariya daake nunamana kana yamike shima yayi waje " dogon tsaki aiman yaja san nan yamike yafiche " shidai Aryan zaune yake ahiru yana latsawaya har saida yafarajin kiraye kirayen sallah yamike yanufi bangarensa " Ammi da Ummi ma suka fiche sukayi nasu bangaren danyin sallah " palan yarage fahad haidar da Abba " Abba yace wai kunyi arwala'ne kunfasan su safras sunafitowa zamuwuche masallahchi " mikewa haidar yayi yana faÉ—in aa baridai naje nayi " fahad ko chewa yayi nikam nayi Abba" ok kawai mai martaba ya amsa dashi
Shiru suka zauna har sauran matasan suka fito sukajera zuwa masallachi

Aɓan garen inna kuwa da sallama tashiga gidan su buba zaune tasameshi a tsakar gida " buba na ganin inna yafara murmushi yana faɗin inna jamɓandu( inna ina wuni) " lfy buba ya kafar taka " da sauki inna" inna tache to allah yakara lfy ina innarka take " tana garke tanabawa shanu ruwa da abinchi buba yabata amsa " to barina dubota bata jira amsar buba tayi gaba abunta " a garken shanun ta iskoh innar buba da sauri inna ta karisa wajenta tana faɗin albishir rinki yar uwa rabinjiki " ɗago kai innar buba tayi tafara murmushi tana faɗin goro " to kifito muje yau kuɗin sunchika dubu goma dai dai chewar inna " da sauri innar buba ta ajiye sandar hannunta datake juyawa shanu ruwan gishiri tafito daga garken tana murmushi jerawa sukayi suka koma chikin gida innar buba ta ɗaukoh mayafi suka fiche

Wani ƙungurmin daji suka shiga tafiya suke har suka isawajen wani dutse ga hayaki nafitowa daga chikin kogon dutsen chikin kogon sukashiga " wani kasurgumin bakin bokane awajen ga idon san nan jajawur duk yabi ya huhhuda hanchi yasa wasu karafuna gawani katan karfe mai raun dayasa a kunnensa bashida kyan gani ko kaɗan
Zama su inna sukayi kusa dashi " zasu fara magana ke nan yayi wani mahaukachin dariya ha, ha, ha, da murya masa daɗin Ji yace aikin ku bazaiyuwu a chikin azumiba saboda duk an ɗaure mana mutanenmu amma kuje sai bayan sallah kudawo ha ha ha yana gama faɗan haka ya ɓache ɓat " da sauri su inna suka mike suka fito inna tace to yanzu barinaje na ajiye kuɗin sai bayan sallah mudawo da haka suka kuche gida.

Kamar kullum yauma zaune suke a wajen chin abinchinsu na makaranta karatu boko hiyana take yaukam tun da bata da tsarki " zahra da diyana da faria kuwa hirar wani film suke waishi love story English movie
Lamrat da amrat suna rubutu a takardunsu "
Kamar daga sama sukajiyo muryan jabir yana faÉ—in ke hiyana zo mutafi " É—ogo kai hiyana tayi a nitse tafara magana kayi hakuri jabir wlh yau banida lfy ne chikina namin chiwo " to yakikesan nayi ke nan ga abokaina chan kowa budurwarsa tazo ni bandani ke nan ba zaiyiwuba i don't care koma meke damunki, nidai kitashi mutafi " kamar hiyana zatayi kuka haka tamike tanufeshi tana faÉ—in muje " kallan uku 10 diyana tawa jabir kasa kasa tache mugu wlh sainayi maganinka " kallanta zahra tayi san nan taja guntun tsaki " jabir tunda yakira hiyana suka tafi basu dawoba har saida a katashi nanma saida diyana da zahra sukaje wajen dayake zama da abokan nasa sukache hiyana tazo sutafi mai É—aukansu yazo " jabir dayaji haka sai yache to taje zasu haÉ—u gobe " jerawa sukayi suka nufi wajen da suke tsayuwa sujira motochin dake É—aukansu "

suna tsaye awajen sukaji magana daga bayansu " gaba É—ayansu suka juya " hiyana tace uncle Omar ina wuni " da faraa a fuskanshi ya amsa san nan su Zahra suka gaidashi zaisake magana saiyaga motochin É—aukansu yazo nanfa yamusu sallama yawuche " sukuma suka shiga mota kamar yadda sukasaba hiyana Zahra diyana motarau É—aya " amrat da lamrat suma motarau É—aya " da gudun gaske motochin sukabar bakarantar" gudu suke sosai suna kan hanyane" zahra tace kinsanme hiyana " girgiza'kai hiyana tai alamar aa " uncle Omar fa wai san diyana yake chewar zahra " kan uban chan niyakeso lallai kuwa yana ruwa wlh dannikam inba sojaba bazanyi aureba " baki buÉ—e hiyana ke kallan diyana " Zahra kuwa chewa tayi meyasa kikesan soja sojojifa mugayene " eh ae a chikin sojanma mugun nakeso wanda zaiyimin maganin yaya Aryan kuma wanda yake da bindiga shima " zahra tace to me yaya Aryan É—in yayimaki haka dakike neman mugun soja yayi maki maganinsa " to bashine kullun inna masa laifi saiyache zai É—aukoh bindiga ya harbeni namutu kowa yahutaba " aikuwa hiyana bata san sanda takwashe da dariyaba tana faÉ—in kai amma kuwa da yaya Aryan ya kyauta wlh " Zahra kuwa chewa tayi dalla rabu da hiyana kinji faÉ—amin muguntar me yake miki " bayan harbeni dayake chewa zaiyi saikuma jamin gashi da takuramin nasa É—akwali dakuma kawo coffee kullun tayi maganar dai dai lokachin da motochinsu ke parking a parking space na chikin gida
Fitowa sukayi suka nufi chikin gida rike da hannun juna

Misalin karfe 4 na yamma gaba É—aya yanmatan zaune suke a palon Ammi suna kallo hiyana kuma tana karawa lamrat karatun qur'ani gaba É—ayansu shiga iri É—aya sukayi duguwar riga abaya dukkansu colour É—aya baki " Ammi ma nazaune a gefe tana gyarawa amrat jigidarta da Aunty farida ta saya musu to ya matseta sosai " da sallama Khalid da yusuf suka shigo palan " da gudu Zahra ta mike ta nufi Khalid,faÉ—awa kan kirjinsa tayi ta rungumesa sosai tana faÉ—in oyoyo yaya Khalid " Yusuf ne yace my baby kema kizo kimin oyoyo mana " da gudu lamrat ta mike tanufeshi hannu ya buÉ—e masa tafaÉ—a kirjinsa yana murmushi " Ammi data tuno abun da mai martaba yafaÉ—a mata nachewar Khalid na san Zahra yasa da sauri tace ke zahra'u wai yaushe zaki girmane wlh idankika sake wan nan oyoyo zaki chi gidanku " turo baki zahra tayi " Khalid yasa hannu ya É—an bugi bakin kana yace to wa'ake turowa bakin hannunta yarikoh suka koma kan kujera mai zaman mutun biyu

Yusuf ma rikoh hannun lamrat yayi suka koma kan doguwar sofan suka zauna " hannu Yusuf yasa yana shafa kan lamrat yana faÉ—in my baby gashinkin nan kyau yakemin sosaifa " baki buÉ—e Khalid ke kallan Yusuf, azuchiyarsa kuwa chewa yake amma Yusuf iskanchinka yawuche tunani anya kaima baka kamu da san yarinyar nanba kuwa " afili kuwa chewa yayi ai gashin Zahra yafi nakowa kyau " harara Yusuf ya wurga masa san nan yace yauwa Ammi nikam inasan intambayeki kullum mantawa nake " Ammi tace. Tanbayi inajinka " wai aina mukasamu kalolin idon mun nan ne pls " Ammi tace au kache tarihi kakeson ji to gyra zama " murmushi kawai yusuf yayi yazubawa Ammi ido

Kakanku wato mahaifiyar mai martaba itache asalin wanda takawowa family mu kalan idan nan kakanku namiji babban likitane aiki yakaishi Us, a chan yaje ya auro kakarku ta mace baturiyar Us, amma musulmache sunanta sarah to sarah itache mai ido light green irin naka kaida yayanku " sarah kuwa mahaifiyar ta idonta ash ne mahaifintane mai light green É—in ido shiyasa gaba É—aya yayan sarah suka zama masu ido 2 colour wasu ash wasu green gashi abunkuma yabisu har kanku jikokinta, " Khalid yace no wonder, shiyasa muke da kyau kamar yayan larabawa ashe ashe " dariya Ammi tayi tana faÉ—in abun harda yabon kai " Khalid zaiyi magana yusuf yache to ammi su hiyana fa ya akayi suka samu blue eyes
Chapter 31 · 0% Book details