← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 90

Sashe 46

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai milalin karfe 4:50 aka gama yiwasu hiyana gyaran jiki da lalle sunyi kyau sosai kamar su'sukayi kansu yaran nan gawani kitso guda biyu da aka musu a gefe da gefen kunnen'su ansa manya manyan bit an zuboshi ta gaba har kan chikinsu tsawon gashin, sauran gashin an É—aure musu a tsakiyar kai,anzuba jelar gashin ta baya har gadan bayan'su, musammanba hiyana da diyana gashinsu yafi tsawo da baki ga tsantsi, ba karamin kyau sukayiba kamar, Æ´a'Æ´an larabawa " bill akayiwa Aunty farida ta biya san nan suka nufi waje "
Shahram dake zaune chikin mota,yana ganinsu ya fito da sauri yana faɗin wellcome ma " da murmushi a fuskarta tace sorry Shahram for keeping U waiting " buɗemusu kofar motar kawai yayi batare daya sake maganaba, suna shiga yarufe motar yashiga gaba yabawa motar wuta sai bakin gate mai gaɗin ya wangale masa gate ɗin ya danna hanchin motar waje da gudun gaske ya miƙi titi, gudu yake shararawa sosai, sai daya kusa isa bakin babban gate na gida tukun ya ɗan ragewa motar gudu horn ɗaya yayi nan take security suka wangale masa gate ɗin a nitse ya kutsa chikin gidan, kai tsaye parking space yanufa ," yana kashe motar yafito da sauri ya buɗe musu " fitowa sukayi gaba ɗayan'su suna faɗin thank U uncle " Aunty farida ta rike hannun diyana sukayi chikin gd " da sallama suka shigo palon " da sauri nurse nasu dake zaune saman Sofa tamike tana faɗin ina kukaje natashi barchi ban gankuba, " wajen gyaran jiki mukaje diyana tabata amsa " dukawa tayi kasa ta gaida Aunty farida " da fara'a ta amsa san nan tanufi ɗaki dan yin wanka tana faɗin sister's kuje kuyi wanka kozo kubiya bashin sallar Azhar da la asar dake kanku " har suna haɗa baki wajen chewa to san nan suka nufi ɗakin Aunty mardiya

yau saura kwana É—aya sallah sai shirye shiryen tarban su Abba ake, manya manya shanu 4 aka'yanka da raguna 5 " hayar masu soya nama Aunty farida ta É—aukoh mata'ne masu jini ajiki masu ji da karfi da lfy, san nan tasa aka fitar da manya manyan gas daga store, aiki ake babu kama hannun yaro ,gamasu yin chin chin a gefe, gamasu donut dubula alkaki da dai sauransu, Aunty farida yau bata zauna ba sai hidima take da jama'a " Aunty Maryam kuwa tana É—aki kwanche abunta

Misalin karfe 1:50 diyana na zaune a ɗakin Aunty farida tadage sai make up take, wayar Aunty farida dake kan gado yafara ringing," da sauri ta ajiye jan bakin dake hannuta tanufi wayar, ɗaukar wayar tayi zatayi waje dan takaiwa Aunty faridan, sai taga pic na Aryan ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, sanye yake da kayan sojoji baƙaramin kyau yayiba fuskar nan tashi kamar bai taɓa sanin me dariya'ba," da sauri tayi picking call ɗin " daga ɗayan ɓangaren Aryan yace,"hello my lovely Aunty " ba itabace yaya Aryan ni che ina wuni " lfy lau y jikin naki " nasamu sauki hiyana che kawai tarage bata samu sauki'ba " subhanallah me ke damunta ina nurse naku " nurse ta koma jiya wai zataje tayi shirye shirye sallah " to meke damun hiyanar " chiwon kai da jiri " ok jibi zamu dawo ae sai na dubata amma duk da haka zansa a kawo mata magani " to bari na kaiwa Aunty farida wayar " daman kinsan zaki kai mata wayar'ne kikayi picking call ɗin " eh ae nayine daman dan na gaisheka tun da mun daɗe bamuyi magana'ba " to ae kece kika manta dani shiyasa " dariya diyana ta ɗanyi kafin tace, ni ban manta da kaiba dan bani da waya'ne Allah dana kiraka " wani ajiyar zuchiya ya sauke"to amma kina kewata kuwa " eh mana ina kewar'ku dukkan'ku " ok to shike nan ki ajiye wayar kawai anjima idan Aunty farida tazo ta kirani dan naji Abba na nemana " to kawai tace tare da chire wayar a kunnen'ta ta mayar kan gadan ta ajiye,"takoma gaban mirro tachigaba da kwalliyar'ta

YOLA

Inna na ɗaki kwanche a kan yar gadon chiyawar'ta taji sallama daga kofar gd mikewa tayi daga kwanchiyar datake tana amsa sallamar,"ɗaukar mayafinta tayi tanufi waje " ganin bello ne ke sallamar yasa inna ta ɗaure fuska sosai tafara magana to yau kuma dame kazo funafiki " ina wuni inna " daban wuniba zaka ganni'ne " to Allah yabaki hakuri daman naga gobe sallane shine nache bari na sauke hakkin ma kwabtaka na kawo miki wan nan,"yayi maganar tare da ajiye wa inna gaji guda uku a gaban'ta, batare daya jira amsar'taba yayi wuce warsa gidan'su " da mamaki inna ke kallansa har yashiga gida, duƙawa tayi ta ɗauki kajin tayi chikin gida," a tsakar gida ta ajiyesu san nan ta ɗaukoh wuƙa tayanke igiyar da aka haɗesu aka ɗaure, ta samu wani igiya ta ɗauresu ɗai ɗai ta kaisu kichin tafito takoma ɗaki ta kwanta," tana kwanchiya babu jimawa buba yashigo gidan da sallama yana ɗingisa kafa da sanda " tana daga chikin ɗaki ta amsa masa san nan tace yashigo " shiga ɗakin yayi hannunsa riƙe da buhu " lfy buba ina zakaje da buhun nan " bappa'ne yace na kawo miki, shin kaface wai kiyi girkin sallah " da murna inna tamike zaune wayyo Allah kacewa bappa ngd sosai Allah yaƙara arziƙi " amin yafaɗa tare da ajiye mata buhun ya juya yafita " buɗe buhun tayi taga shin kaface mai kyau da murna ta tura buhun bayan kyaure ta ɓuye

KANO

Misalin karfe 7 na dare, sun haɗu a palon Abba suna buɗa baki " kai my diyana sarkin san kwalliya chewar Aunty farida tayi magabar tana ɗan jan kumatun,diyanar " ae kwalliyar dazanyi gobema sai yafi wan nan kyau " Allah ko ae haka akesan mace takasan'ce mai tsabta da kwalliya " Zahra tace Aunty farida ae muma munayi " eh kunayi amma my diyana tafikuyi sosai, kuma kuƙara dagewa " to shike nan zamu rinƙayi sosai " ok to kuchi abinchin'ku dawuri muje mu kwanta dan kunga gobe sallah zamu tashi da wuri " har suna haɗa baki wajen chewa toh " shiru kakejin palon babu mai magana sai paran spoon kawai zakaji " sallama sukaji anyi a bakin kofar palon " amsa sallamar Aunty farida tayi san nan taba da izinin shigowa " ɗaya daga chikin security bakin gate ne,har ƙatsa ya duƙa ya gaida Aunty farida " ta amsa tare da tambayar'sa ko lfy " eh lfy wani likitane yakawo saƙon nan wai inji oga yace abawa hiyana " ok to ajiye a saman table ɗin gaban kan nan " mikewa yayi ya ajiye sakon san nan yanufi waje
Bayan sun gama chin abinchine suka mike zasu tafi É—aki, Aunty farida tasa hannu ta É—auki sakon tana faÉ—in muje É—aki kisha maganin hiyana " toh kawai hiyana tace, san nan suka nufi waje " sai da Aunty farida ta tabbatar hiyana tasha magani san nan takama hannun diyana da amrat suka nufi,dakinta, a gurguje sukayi wanke sukayi sallar issha suka kwanta asuba tagari

Tunda sukayi sallar asuba yau basu mai da barchiba " diyana tun karfe 7 take gaban mirro ta goga wan nan ta fenta wan nan ba karya tayi kyau sosai tamkar zataje gasar sarauniyar kyau " da sallama Aunty farida tashigo ɗakin tana waya da Aryan, wow my diyana kin ganki kuwa kamar wata sarauniya " dariya diyana tayi tana faɗin ngd Aunty farida " dawa kike magana kuma Aryan ya tambaya " hmm nina mantama muna waya wlh, kyan my diyana ne ya rikitani " shiru ya ɗanyi kamar mai tunani chan kuma sai yace to ɗauke'ta hoto ki turomin naga kyan daya rikitakin " ae kuwa kai ma idan kagani sai ka rikiche " to shike nan turomin ɗin dai kekam " ok tace tare da chire wayar daga kunnen'ta ta katse kiran" tadubi diyana tace to tashi kisa kaya namiki hoto " yauwa Aunty farida Allah yamiki albarka daman inasan inje in anshi wayar Aunty Zahra nazo nayi hotan, tayi maganar tana kokarin mikewa..✍️

More comments pls
💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 19*
Chapter 46 · 0% Book details