← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 90

Sashe 6

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kyakkyawar yarinya che fara tas ga dogon hanchi har baka doguwa che amma ba sosai ba bata da kiba duk da tana sanye chikin hijabi, hakan bai hana gashin dake kwanche a gaban goshin ta fito waba dark black ne gashin very smooth gata da manya manyan blue eyes, laɓɓan'ta ɗan karami pink colour bazata wuche 14 years ba sanye take chiki wata ko ɗadɗiyar atamfa ta koɗe tayi fari ga wata je mam miyar hijabi baki ne amma saboda koɗewa sai da ya dawo ash colour tsaye take tana riƙe da bokiti irin na penti almost 5mnt tana tsaye chikin fushi tafara magana da harchen fullanchi "hiyana idan bazaki fitoba wlh tafiyata zanyi na barki, tayi maganar tana kallan kofar wani gida
Gida ne ɗan ma dai dai chi kofar gidan ansa masa buhu an rufe a matsayin labule,irin gidan fulanin nanne masu kiwon shanu ke waye gidan yake da zana, daga chikin gidan hiyana ta da wata murya mai daɗin gaske tana faɗin adin kai diyana ina zuwa ina dubawa amrat hijabi ne "to wai waya chemaki amrat zata bi mu ne, zamuɗebo har da rabonta dan haka ta zauna a gida taƙarisa maganar tana yamutsa fuska " yaye labulen buhun hiyana tai tafito, subhanallah sarki ya tabbata ga ubangiji da yayi wan nan halittar hiyana tafi diyana kyau sosai ta ɗan fita fita tsawo, kuma da alama zata ɗan fita shekaru dan hiyana zata kai 16 years farache sosai tafi diyana haske idon tama yafi na diyana girma da shiga colour idon ta yayi blue sosai kyakkyawa che ajin farko, rike take da hannun wata yarinya wadda bazata wuche 11 years ba yarinyar tana kama da diyana sosai sai dai ita idon ta baki ne manya manya, karaso'wa wajen da diyana ke tsaye su kayi hiyana na faɗin kiyi hakuri diyana kinji "haba hiyana ke che babba amma keche ke ja'mana duka kullun "to shike nan diyana kiyi hakuri zan gyara kinji muje to "aa bazamu tafi da amrat bafa ki mai data gida "diyana kibari mutafi da ita mana babu kowa fa a gidan bappa kuma yayi barchi kin sani bansan mu barta a gd ita kaɗai "nikuma Allah hiyana bansan amrat tabi'mu rafin nan akoi wahala Allah "to yanzu kam tun da mun fito muje kawai mu daina ɓata lokachi, juyawa diyana tana tura ɗan karamin bakin tan nan suka jera su kasa amrat a tsakiya

Wani dan siririn hanya suka nufa mai chike da dogayen chi yayi tsakiyar chi yayin suka kutsa tafiya sukayi mai nisan sosai kafin su isa wani rafi mai girma gefe gefen rafin chike yake da gona'ki da shuke shuke, ruwa suka ɗiba a buket ɗin dasuka riƙe hiyana ta ɗora'wa diyana nata buket ɗin chike da ruwa san nan da kyar itama ta ɗora nata ta kamo hannun amrat suka fito daga rafin suka kama hanyar gd, tafiya suke ba wan da yace da ɗan uwan sa ko kala, a dai dai wata katuwar bishiyar mangoro wani saurayin da bazai wuchi 24 years wani ɗan dotti dashi pusu pusu kamar an kwato shi daga bakin Kura ba yasha gaban hiyana birki suka ja suka tsaya suna kallan sa, ɗaure fuska diyana tayi tana faɗin "buba me haka dan Allah kabamu hanya mu wuche, wani kallan uku 10 buba ya watsawa diyana kafin yace "ke ba take nake ba tukun nan kibari nagama da hiyana zan dawo kanki "chikin sanyin murya hiyana tafara Magana buba kayi hakuri kaji kabar mu,mutafi wlh ruwan nan akoi nauyi kabari in muka dawo ɗiban na biyu sai mu tsaya muji me zakache "ke ni sa'ankine dazaki che na jira ku to baku isa ba yanzu nake san yin maganata idan ruwan yamuku nauyi,sai ku sauke kasa ku ajiye idan nagama maganan da zanyi sai ku ɗauki ruwan kutafi, diyana sarkin rashin hakuri a kule ta juye'wa buba ruwan dake kanta ajikin sa tun daga kansa har kafa yamike shar'kaf ta watsa a guje tanufi hanyar gida, dafe kai hiyana tayi tana faɗin "kayi hakuri buba..bata kai karshen maganar ba buba ya buge ruwan dake kanta ya faɗi kasa ya zube ɗaukar boket ɗin buba yayi yafara bugawa da katsa yana kokarin fasawa, hiyana kuwa ganin hankalin buba ya koma kan yana san fasa musu boket ne yasa ta kama hannun Amrat suka kwasa aguje sukayi hanyar gd, sai buba ya gama fashe musu bo'kitan gaba ɗaya san nan yabi bayan su a guje

Da gudu diyana ta faɗa gd wani ɗakin buk'ka tashiga,sai haki take tana numfashi da kyar, wani bawan Allah dake zaune chikin ɗakin, a kan gadon chiyawa, daka gan shi kaga ka mannin hiyana duk da tsufa da wahala dake tattare dashi ba zai hana ka gane kyan sa ba "diyana lfy kika shigo kina haki haka meyasaki gudu wani kika tso kana ko "bappa wlh buba ne shine zai bugeni na gudu kuma ba abun dana masa, bappa zaiyi magana sai ga hiyana tashigo rike da amrat dukkan su sai haki suke suna numfashi sama saman "hiyana har dake yau kuma bappa ya tambaya yana kallan hiyana, chikin sar'kewar murya hiyana tace "aa bappa laifin diyana che ta shafe ni, "ya Allah ya kawo muku mafita ƴa'ƴana, har suna haɗa baki wajen chewa ameen bappa, basu gama rufe baki ba aka ba paɗo ɗakin babu ko sallama wata mata che baka mai ƙaton hanchi, damkoh wuyar hiyana ta jata zuwa tsakar gd ta hau bugu matar nan tsaka nin ta da Allah take bugun hiyana, ta ko ina ihu hiyana keyi tana faɗin "dan Allah inna kiyi hakuri, "au kinsan da hakuri ke nan koh har buba zaku jiƙa da ruwa kuma ku zage'shi koh to wlh yau sai kun yabawa aya zakin ta, komawa ɗakin tayi ta damkoh diyana da gudu Amrat tayi bayan bappa ta buye, inna kuwa jan diyana tayi har tsakar gd ta ɗaukoh wani itache ta hau bugun hiyana da diyana dashi bugun su take sosai duk inda ta samu take sauke musu itachen, tun kukan su na iya fita har sautin kukan ya daina fita,duka sosai inna tamusu sai da ta faffashe musu jiki, san nan ta kyalesu takoma gefe kan wani dutse ta zauna tana mai da numfashi, su kuma suka dun kule waje ɗaya suna kuka, sai da inna ta gama hutawa san nan ta ɗago ta dube su tafara magana, "ke hiyana ko kina so ko baki so buba zaki aura dan kin samu ma zai rufa miki asiri, kuma kutashi tun da kun fusata buba ya fasa buket ɗin ɗiban ruwan to da kofi zaku koma ɗiban, wlh kutashi ku ɗauki kofi kutafi kufara ɗiba min ruwa yanzun nan, ku chika komai na gd san nan ku chika durum na dabbobin nan,kutashi tun ban zo na karai'raya kuba ta karisa maganar chikin tsawa, da kyar suka miƙe har suna tangal tangal suka sufi wani ɗan ki chin suka ɗaukoh kofi kowache ta ɗauki cup 1 suka fito suna kuka suka nufi waje

Bappa na zaune chikin É—aki yana hawaye Amrat ta fito daga buyan datayi a bayan sa tafara goge masa hawayen tana faÉ—in bappa ka daina kuka kaji, rungume ta bappa yayi yachigaba ga kwalla

Su hiyana kuwa han yan rafin suka nufa suna rike da kofin suna kuka, "chikin kuka hiyana tace yanzu diyana bakin ga irin abun danake faÉ—amiki ba, kullun ina faÉ—amiki komai buba zai mana muyi hakuri dan in mu kache zamu biye masa wlh mu zamu sha wahala komai kan mu zai dawo amma ke bakiji,bansan wani irin kai ne dake ba "share kwallan fiskar ta diyana tayi tana faÉ—in yanzu hiyana haka zamu chigaba da rayuwa ni gaskiya bazan iya jure wa ba, yazamuyi mu É—ebo ruwa da kofi kuma a che mu chika abuba dake gida da ruwa har dana dabbobi nidai bazan iyaba "to duk bake kika jaba da zaki che bazaki iyaba kin nafa sane da kyar bappa yasamu yaje chikin birni ya sawo mana buket É—in nan, yanzu gashi kinsa buba ya fasa bappa kuma ba takawa yake ba yanzu bare ya sawo mana wani ai dole ma mu É—ebo ruwa da kofin tun da dai kin san inna in tayi magana ba wan da ya isa yasa ta chanza, shiru diyana tayi bata sake chewa komai ba harsuka kai bakin rafin suka É—ebo ruwa a kofin suka juyo suka kama hanyar gd

More comments an share
*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Mrs BMB*

💫New team 💫
⬇️
💖The talent troupe writer's 💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3*
Chapter 6 · 0% Book details