← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 90

Sashe 15

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jama'a ne zaune a kofar gidan su diyana suna karɓan kai suwar rasuwar bappa chikin gida kuma matane zaune suna yan koke koken su, hiyana diyana Amrat lamrat kuma suna zaune a kusa da rafe kasan wani bishiyar mangoro suna kuka, duk fuskar su ta kunbura kuka suke sosai kamar ransu zai fita chikin kuka da dashewar murya diyana ke faɗin "shike nan bappa ya mutu ya bar mu munshiga uku ina zamusa ranmu wayyo allah "da kyar hiyana ta iya buɗe baki muryan ta duk ya dashe saboda kukan data sha tafara magana "a'a diyana ki daina chewa munshiga uku gaskiya bamu shiga uku ba tun da mun rike Allah inshaa Allah, Allah bazai kyalemu muchigaba da wulakantaba chikin shessheka lamrat tace "eh hakane Aunty hiyana addua kawai bappa ke bukata, duk kansu suka haɗa baki su kache Allah yajikansa da rahma
Diyana tache "hmmm jiya fa Bappa yarasu amma baza abar'mu mu dan huta ba muji da rasuwar bappa ba inna tace, dan Allah yanzu muji da wanne muji da rasuwar Bappa ne ko kuma muji da É—ebo ruwa
Mikewa hiyana tayi tana faÉ—in "kutashi ma mukarasa É—eban ruwan nan kar inna ta buge'mu da kyar suka mike suka nufi rafin suna rike da cups a hannunsu
Sun É—ebo ruwan zasu wuche ke nan sai sukaji muryan yaya bello na kiran'su daga chikin gona, chikin gonar suka nufa, a zaune a inda yasaba zama suka same sa ga tulu sababbi guda 4 a gabansa
A gaban sa suka duka suka gaidashi ya amsa chikin faraa san nan yamusu taziyar mutuwar bappa tare da adduar Allah ya jikansa suka amsa da ameen, kana yache ku É—auki tulu nan nan dasu zaku rinka deban ruwa dan ku nasaya, duk da kukan rasuwar bappa dasuke hakan bai hana'su yin murna da ganin tulun ba É—auka sukayi suna murna sai godiya suke masa suka fito gonar suka nufi rafi, ruwa suka É—eba a sabon tulun su sai murna suke,suka nufi hanyar gida

One day later

yau Bappa yachika kwana uku da rasuwa, jama'a sun watse babu kowa a kofar gidan kowa kama kansa

diyana hiyana da lamrat sunbar amra a gida tana tikar aiki duk kansu suna dauke da tulun da yaya bello yasa musu suka nufi rafi suna tafiya suna yar hirarsu
Diyana tache "wai ya akayi inna batayi magana akan tulun nan bane Girgiza kak hiyana tayi tana faÉ—in "hmmm ai bata lura bane inda ta lura ai da saita tambayi waya bamu ko kuma ma ta fasasu
Lamrat tache "to yanzu idan inna ta tambayi waya bamu tulun me zamu'che mata,dogon tsaki diyana taja kafin tace "sai muche muma ba mu san mutumin daya bamu'ba,yaga muna É—eban ruwa da kofine sai yabamu "yauwa diyana gaskiya kin kawo shawara daman sai tunani nake idan inna ta tambaye mu me zamu'che chewar hiyana,tayi maganar dai dai lokachin da suka iso bakin rafin ruwa suka debo,a tulun suka juya suka nufi hanyar gd,

"hiyana wai yan zu haka zaki Auri buba diyana ta tambaya, buÉ—e baki hiyana tayi zatayi magana sai taji an ture tukun dake kanta ta baya ya faÉ—i ya tar watse, asukwa'ne buba tagani tsaye yana mur mushin mugunta diyana naganin buba ta kwasa a guje tayi hanyar gida, gudu take iya karfinta har ta iso dai dai zata shiga ke nan tayi tun tube da dutsen kofar gidan ta faÉ—i kasa tulun ya faÉ—i kasa ya tar watse, wani kukan bakin chiki ta sake kuka take kamar ranta zai fita
a wan nan yanayi Hiyana da lamrat suka zo suka sameta tai maka mata Hiyana tai tamike tsaye ga goshin ta sai jini yake, dukkanbsu sai hawaye suke haka suka shiga gida

inna dake zaune a tsakar gd tache ina ruwan, kuma tun dazun na zauna a nan nake jiranku zan dora ruwan shayi
Chikin shesshekar kuka lamrat tace "wlh inna buba'ne ya kifar da ruwan
Da sauri inna tamike tana faÉ—in buba na zakuwa sharriko ai nama buba ya ganku bare ya kifar da ruwan to wlh yau zaku yabawa aya zakin'ta, suna tsaye awajen suna matsar kwalla, har inna tashiga É—aki ta daukoh wasu manya manya bulalin bishiyar dalbejiya

Ta nufosu gadan gadan baji ba gani tafara sauke musu zabga zabgan bulalun nan ajiki babu ko imani bare tausayi, ihu suƙe hiyana da diyana suka haɗu suka kare lamrat, duka inna ta musu sosai sai da ta kutun suna iya kuka har kukan nasu ya daina fita sosai, sai da ta bugesu iya san ranta san nan ta kyalesu tana faɗin kutashi tun kafin na rufe ido na buɗe ku ɗauki kofi ku tafi ku ɗebo min ruwa,yanzun nan kugama kuzo ku jemin tallah tana kai karshen maganar ta nufi ɗakin ta, da kyar suka mike suka nufi Kichin suka ɗauki cups suka fice daga gidan, Amrat dake duƙe a wajen wanke wanke tana wanke kayan inna sai kuka take kamar ranta zai fita ba abun da take tunawa sai mahaifiyar su a zuchiyar ta take faɗin yanzu da umman mu bata rasu'ba da tana nan inna bazata musu haka ba wayyo Allah ka jikan umma da bappa haka dai Amrat wunin ranan ta wuni tana kuka su diyana kuwa suna jidan ruwa da kofi ga yinwa ga nisan rafi ga zafin rasuwar Bappa.

Misalin karfe 11 nadare zaune suke a dakin'su dukkan'su ba wan da yayi barchi saboda yinwar dasuke ji ta hanasu barchi diyana che ta dubi hiyana tafara Magana "hiyana yaufa tun safe jinin nan yasake dawowa na chanza zani har nagaji duk kayana sun kare jinin kuma bai daina fitowaba
A ɗan tsorache Hiyana tache "bari na lallaɓa naje na tambayo innar yaya bello sai muji kodai akoi wani abun da zakisha sai ya daina zuwa a razane lamrat tace "Aunty diyana wani jini kuma, diyana zatayi magana hiyana ta rigata da chewa ina ruwan'ki dake ake magana ne, shiru lamrat tayi taba sake magana ba
Amrat dai takasa magana jimamin mutuwar bappa har yanzu bai saketa ba, dan kuwa duk tafisu shakuwa da Bappa su basu yawan zama dashi sosai saboda aikin É—eban ruwa da tallah, wani lokachima sai sufi kwana uku basu samu damar ganin saba saboda balai inna,shiya ita amrat tafisu shiga damu dan kuwa ita kullum tana gida idan tagama wa inna aikin gida sai tatafi É—akin bappa, ta kwanta ajikinsa suyita hira.

Mikewa hiyana tai tana faɗin, bari dai na lallaba naje wajen innar yaya bello dan nasan itama batayi barchiba,tana kai karshen maganar ta fiche daga ɗakin, lallaɓawa take kamar wata ɓarau'niya ta fiche daga gd tana fita ta kwasa da gudu dan tsoro dare yayi ga duhu, sai data shiga gidan su yaya bello san nan ta ta tsaya tafara tafiya a hankali hankali dan kar wani yaji ya ganta ya faɗawa inna
Chapter 15 · 0% Book details