← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 90

Sashe 5

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Abba su uku ne awajen baban su sarki khalid awan chan lokachin, Abba shine babba sai bappa usman sai bappa Aliyu ne ƙarami kakan mu shi ya haɗa auren Abba da Ummi na alokachin, baban Ummi shine sarkin katsina ansha biki sosai, bayan auren ummi na da Abba da shekara ɗaya Allah ya albarka che da samun Aihuwa ɗiya mace kuma bakowa bace face ni, ina da shakata biyu a duniya Ummi na ta haifi Mardiya, an haifi Mardiya da wata uku Abba yace zai kara Aure da farko Ummi na taki yar da amma daga baya sai ta aminche Abba ya auro yar sarkin gombe kuma itace Aunty amarya, bayan auren su da wata 10 Aunty Maryam ta haifi ɗiya mace Abba yasa mata suna maryam,alokachin ne kuma bappa usman yayi Aure ya Auri umma'n su Khalid itama data zo ya mace ta haifa, Abba ya shiga tunani da damuwa dan yana son ɗa namiji gashi shiru shiru daga Ummi har Aunty amarya ba wan da yasake Aihuwa, wani taro dasu Abba sukaje da kakan mu garin yola a chan yaga Ammi ya dage sai ita Ammi ba fulatanan ruga che iyayen ta sunki bawa Abba auren ta amma Abba yana che haka suka hakura suka bashi Auren Ammi a kasha biki auren Ammi da wata uku tasamu chiki a tare suka samu chiki da Umma'n su Khalid chikin Ammi na da wata 3 Aunty Amarya ma tasamu chiki chikin Aunty Amarya na da wata 4 Ummi na ma tana mu chiki kamar abun haɗin baki rana ɗaya Ammi da Umma'n Khalid su aihu Ammi ta haifi ɗa namiji Umma'n su Khalid ta haifi yan biyu namiji da mace, bappa Usman yayiwa kakan mu takwara yawa ɗan sa na mijin suna Khalid,macen kuma salma, Abba kuma ya sawa prince Safras musha murna sosai a satin da a ka haifi khalid da prince a satin kakan mu mace ta rasu musha kuka da bakin chiki sosai, kakan mu tana da wata uku da rasuwa Aunty Amarya ta haifi yan biyu Abba yasa musu suna Aryan da Aiman, Aryan suna da wata uku Ummi na ta haifi yusuf daga nanne basu sake hai huwaba, Khalid da salma na da shakara biyu Umma'n su ta haifi Ahmad, shiyasa kikaga da yaya prince yaya khalid yaya Aryan yaya Aiman yaya Yusuf dakuma yaya Ahmad sun taso kamar wasu ta gwaye dan dukkan su banda Ahmad ba wan da yabawa ɗan uwan da full 1 year, shiru shiru su Safras na da shakara uku Ammi ta haifi Fahad, Fahad na da shekara uku Ammi da Aunty Amarya suha aihu a tare kuma dukka ƴaƴa maza suka haifa, Abba yasa musu suna Umar da Haidar Umar na koyan zama kakan mu da bappa Usman sukayi haɗari a kan hanyar su na dawowa daga wani taro dasuka je maiduguri munji mutuwar bappa usman wan da har gobe ma inajin mutuwar bazan taba daina jin mutuwar bappa usman ba har nakoma ga Allah, tun lokachin da aka sanar da Umma bappa Usman ya rasu ta faɗi bata sake lfy ba har itama takoma ga Allah, Ammi ta ɗauki su Khalid ta haɗa su dasu prince tariƙe, Abba ne ya karɓi sarauta bayan mutuwar kakan mu sarki Khalid Abba ya karɓi sarauta wajen da shekara 5 Ammi ta haife ki tun daga kanki ba wanda yasake Aihuwa har yanzu to kinji ta kai chan chen tarihi idan idan kina san jin komai kine kisamu Ummi taba ki lbr Aunty farida ta karisa maganar tana sauke ajiyar zuchiya*

Ji su kayi daga bayan su ana faɗin ae basai tazo waje naba wan nan lbr dakika batama ya isa, murmushi sukayi gaba ɗayan su Khalid yace "ina wuni ummi "lfy lau baba saukar yau she Ummi tayi maganar tana kokarin zama saman sofa mai zaman mutun 1 "ɗazun mu kazo Ummi "to ina sauran ko kai ka ɗai kazo "Aunty farida tace aa Yusuf ya shigo kina bar chi ai daman shida yusuf ɗin da Aiman da Ahmad ne sukazo ƴa'ƴan basu zo ba,Aunty farida ta karisa maganar tana dariya, murmushi nasu irin na manya Ummi tayi tana faɗin " kawai Ummi tayi batare datayi magana ba "Aunty tashi kije ki kiramin Haidar da Umar kinji chewar Aunty farida, miƙewa Zahra tayi jiki ba kwari ta fice daga palo, fita tayi daga ɓangaren Ummi gaba ɗaya, ta ɗan yi tafiya kafun tashiga ɓangaren su Haidar, da sallama a bakin ta ta shiga palon, babu kowa, shiru ta tsaya tana waswasin taje betroom na su ne, kokuma tajuya taje tachewa Aunty farida bata gansuba kamar daga sama taji anche "what are you doing here ɗago ido,tayi tana kallan sa yana sanye chikin 3cuter wando ruwan kasa da farar riga mara nauyi, saurayi ne dan shekarun sa zasu fi 25 ba kyakkyawar gaske ne kaman nin sa ɗaya da DON ban ban chin sa da DON shi idan sa fari ne DON kuma light green, murya na rawa Zahra tafara magana "Aunty farida che tache nakira mata yaya Haidar da Yaya Umar "daman Aunty farida ta zone ya tambaya yana chiro waya daga aljihun sa "eh tazo tana part ɗin Ummi, shiru yayi bai sake chewa komai ba, itama Zahra shiru ta tsaya almost 10 mnt a hankali ta ɗago kai dan taga wai ya tafine ko yana nan, yana tsaye a jikin stair case ɗin yana latsa wayar sa chikin tsoro da fargaban amsan da zai bata tace "yaya Fahad ina su yaya Haidar ɗin, shiri yayi bai tanka ba kamar ma bai san akoi mutun awajen ba ko sai latsa wayar sa yake, chikin tsoro Zahra ta sake mai mai ta tambayar "tayi yaya Fahad ina su yaya Haidar, wani dogon tsaki Fahad yaja chikin tsawa yake faɗin "wai kin bani ajiyar sune abeg get out, tun bai kai karshen maganar ba Zahra ta fita da gudu dan daman kamar a kan kaya take

Da gudu tashiga palon Ummi kan chin yar Aunty farida ta faɗa tana Kuka "subhanallah Auta meyafaru wa ya taɓaki chewar Aunty farida Zahra dai kukan ta take batayi magana ba "ai kema Aunty farida kinsan halin su banso kika aiki Zahra wajen suba, yanzu kilama ta haɗu da Yusuf ne a hanya ya daka mata tsawa, chewar Khalid Aunty farida tasa hannu tana shafa kan Zahra tana faɗin "sorry my lovely Auta kyalesu duk abun da suke miki kitara saiki rama akan ƴa'ƴansu in sunyi aure sun aihu kinji koh share hawayen ki,
dariya khalid yayi sosai san nan yace wai wa yaga yara, tab waƴan'nan akoi zan chen aure ma a'lamarin sune, ai wlh ko zan chen mace ban taɓaji sun yiba, mutane kamar dutse basu da shauki ƴanzu haka maganar danake miki friend mu hisham zai yi aure bakin san Hisham ba Aunty farida ta gyaɗa kai alamar eh "to Hisham dan yayi Aure Aryan da DON suka raba gari dashi "what? Kana nufin saboda Hisham yayi aure ne DON da Aryan zasu raba gari dashi, abotar kufa tun yarinta kai ina hakan ba zai yuba " to gashima yayuwu kuwa dan ba yadda bamuyi dasu ba akan suzo bikin sunki zuwa,shima Aiman damuka samu muka lallaɓashi yazo yaki halaktar daurin auren, shi kuma Yusuf ɗaurin aure kawai yaje yaki zuwa wajen walimar " tab to wlh basu isaba dolene su zauna tare da Hisham kilama sanadiyar zaman nasu suma sufara sha'awar auren yanzufa kusan 30 years kuke dashi kun zauna ba abunda kuka iya daga mai rike bin diga sai mai rike sirin jin Allura sai mai fama da laptop wai da sunan zane, Khalid ya dukar da kai kasa dan anzo kansa shima dan shine mai fama da laptop, aunty farida tachi gaba da chewa "sai mai fama da rigar lauyoyi gamasu tasowa nan yanzu duk kun lalata musu tunani dan suma ba mai wani maganar aure chikin su, duk kun chika mana gida, to mun gaji da ganin ku ƴaƴa muke san gani, su Ammi suna bukatar jikoki gashi ni tunda nayi aure ɗa 1 Allah yabani karamin Safras har yanzu shiru kakeji ban samu kariba to gwaranima, mardiya ko ɗayan bata samuba dan haka muna bukatar ƴaƴa agidan nan, yanzu haka Fahad shekarun sa inban mantaba zasukai 25 ga Haidar da Umar suma sun kai 23 ga Zahra Auta an zama yan mata yanzu haka Zahra nada 16 years to mekuke bukata dayawuche aure Allah ya hore muku komai,to yazama dole kuyi aure yan zu kam takarisa maganar da alamar ɓachin rai a face ɗinta, Ummi dai ido ta zuba musu tana kallon su dan ita ba mai yawan magana ba che " laaa ni Aunty farida kin tunamin ma inasan muyi wata magana, chewar khalid ɗin "ok to inzo muje waje ke nan, Khalid ya ɗan sachi kallan inda Zahra da Ummi suke san nan yace eh to muje palan Abba zai fi tunda nasan yanzu baya nan yana fada "to muje amma kafin nan bari nayi waya da yan uwan kan nan dan inasan gabaɗayan mu muhadu a palan Abba bayan sallar issha "to kawai Khalid yace tare da mikewa yanufi hanyar fita "Ummi tache adawo lfy Baba tunda abun sirri ne "murmushi yayi yana shafa kansa batare da yache komai ba yafiche daga palon

To

(Garin yola ✈️🛬
Chapter 5 · 0% Book details