← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 90

Sashe 63

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

... hakan yayi maka? mikewa BGS yayi yaje ya rungumi Abba yana faɗin "shiyasa nake son ka my Abba murmushi Abba yayi yasa hannu yana ɗan bubbuga bayan BGS kamar karamin yaro yana faɗin "nima ai ina matikar kaunar ku sosai duk wani abun da zai saku farinchiki shina ke so, "Abba muma mu ma matikar son farinchikin ka ai yayi maganar yana raba jikin sa dana Abba, miƙewa Abba yayi yana faɗin lokachin barchi yayi good night my lovely son, "good night Abba na BGS ya bashi amsa yana nufar, kaban mirrow, Abba kuma ya fice daga ɗakin yanufi part nashi, jallabiyar jikin sa, BGS ya chire ya nufi toilet dan yin wanka.

Abangaren Aryan kuwa yana fitowa daga part na BGS kai tsaye, part nashi ya nufa da sauri yana shiga betroom ɗin diyana na fitowa ta kawo masa coffee ta ajiye zata fita, karo sukayi kanta ya bugi faffaɗar kirjinsa ta fame chiwon nata wani ihu azaba ta saki tayi baya zata faɗi, da sauri ya rikota, nan take jini ya fara zuba daga goshin nata, rungumeta yayi sosai ajikin sa da kyar ya iya furta "sorry kiyi shiru, "yaya Aryan zafi ya kemin sosai "na sani nasan zai miki zafi amma ki daure ki daina kuka kinji muje na duba miki, ya karisa maganar tare da raba jikin su, ya kama hannun ta suka koma chikin ɗakin saman sofa ya zaunar da ita, ya zauna gefen ta ya zuba mata ash eyes nashi yana kallan yadda hawaye wani ke bin wani a kunchinta calmly ya fara magana "ba na che ki dai na kukan nan ba, turo ɗan karamin bakin nan nata tayi "to zafifa yake min, hannu yasa yana goge mata hawayen yana faɗin "to ki daure kinji bana son kukan naki ne ko kaɗan yana damun na idan ki nayi, ba kiga yadda ki kayi tsara kwalliyar ki ba ko so kike ya ɓachi "a'a bana son ya ɓachi "to kiyi shiru kinji, gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma ya mike ya ɗauko A box,ya dawo kusa da ita ya zauna

A hankali ya fara gyara mata chiwon nata, sai was Allah na take faɗi shi kuma yana che mata sorry, har ya kammala san nan ya miƙe ya mayar da Box ɗin ya koma gefen katafaren gadon sa ya zauna,

...ɗaure fuska yayi sosai yana kallonta "ke wai bana che kada ki sake kwalliya da daddare ba, baki da lfy ma amma sai kin zana waɗan nan abubuwa a ɗan karamin face nakin nan ko? turo ɗan karamin bakin nan nata tayi kamar biro kafin tace "kayi hakuri bazan sake ba "kullun haka ki ke chewa ba zaki sake ba amma sake... Bai karisa maganar ba ash eyes nashi ya sauƙa a kan kayan jikinta,

wasu shaggun riga da wando ne, Black jeans ne ya matseta sossi santala santalan chin yoyin nan nata kamar zasu fasa wando, sai yar figaggiyar T-shirt pink colour itama ta matseta kana ganin shap na breast nata sosai daman gasu nan masha Allah tula tula dasu, ga kanta ba ɗan kwali ta saki wan nan bakin lallausan gashin nan nata har baya,sai shekin gashin ke yi, ta zubo wani ɗan kaɗan ɗin gashi ta gaban goshin ta, tayi make up nata iya make up,ga wani shegun high heel pink da ta sa a kafar ta, mamaki ne ma yaka mashi wai wa ya koyawa yarinyar nan duk irin waɗan nan abubuwa, nan take yaji ransa ya bachi sosai chikin tsawa yace "ke kina da hankali kuwa haka daman ki ka fito,kika keto gaba ɗaya part part na gidan nan har ki ka zo nan ko? chikin tsoro ta ɗago dan jin yadda yayi maganar, ba karamin raza tayi ba data kalli yadda fiskarsa ta sauya lokachi guda, asukwane ta miƙe zata gudu,

Taku ɗaya yayi ya tamki kugunta ta baya, tsabar raza da tayine bata san, lokachin da ta fasa ihu ba, asukwane yasa hannu ya toshe mata baki, chikin tsawa ya furta "kimin shiru,shiru tayi jikinta har bari yake . zame hannunsa yayi daga bakinta ya juyo da ita suna fuskantar juna, nan take kuma sai yaji ɓachin ran nasa duk ya kau sosai yake kallon face, nata a ranshe yana faɗin "yarinya sai kyau kamar ita tayi kanta komai tayi kyau yake mata,

Ganin yayi shirune yasa diyana ɗago blue eyes nata karaf suka sauƙa chikin nashi, murya na rawa lips nata sai kerma suke saboda tsoro kamar mai jin sanyi tafara magana "yaya Aryan kayi hakuri wlh ba laifi na bane Aunty farida da che tache... Bata karisa maganar ba sakama kon fisgota da yayi ta faɗa faffaɗar kirjin sa, dan ba zai iya jure kallan yadda lips nata ke motsawa ba,mutuwar tsaye diyana tayi dan gaba ɗaya ji tayi kamar baa duniya take ba, ran kwafar da kansa yayi sai tin kunnen'ta chikin wata iriyar kasalalliyar murya ya fara magana kasa kasa "karki sake saka irin waɗan nan kayan kinji ko? idan ma kina so sakawa kisa a iya ɗaki kawai idan zaki fita waje kisa hijabi kinji ban son na kara ganin ki haka.

....da kyar ta iya ɗago kanta daga kirjin nashi dan ta samu iskan da zata yi numfashi kasan chewar ya matseta sosai,bata iya wani numfashi da kyau, a hankali ta buɗe ɗan ƙaramin bakin ta muryar har rawa yake tafara magana "to yaya Aryan ai Aunty farida che tache na rinka sawa idan zan... Bai bari ta karisa ba ta ɗora ya tsan sa a saman lallausan lips nata yana girgiza kai kafin yace "a'a koda Aunty farida ta sake chewa ki saka kiche mata na hana ki kinji? kuma ai ita Aunty farida gobe ma zata koma ni dai kar na sake ganin ki da irin wan nan kayan bana so, to kawai tace masa tana numfashi da kyar saboda matse ta da yayi,

Shiru sukayi dukkan su shi yana kallanta ita kuma tana kallon kirjinsa, Almost 5mnt a haka, san nan diyana ta É—ago blue eyes nata slowly ta sauke su kan face nashi, karaf suka sauka chikin ash eyes nashi, dan kuwa ita yake kallo, da sauri tayi kasa da kanta dan bazata iya kallan chikin idon sa ba, "yaya Aryan na gaji da tsayuwa wlh jinake kamar zan faÉ—i "to ni kuma ban gajiba, da sauri ta É—ago blue eyes nata tana kallonsa ganin yadda ta É—ago ne yasa yashiga tunanin me ya faÉ—a ne, dan shi kwata kwata bai ma san me ya faÉ—a ba, sauko da ash eyes nashi yayi kan É—an karamin bakin ta, yana kallan lallausan lips nata, da sauri ya sake ta yana furta a'uzubillahi minasshe É—anin rajim, a chikin zuchiyar sa "ke wuche ki tafi É—aki dare yayi kuma karki sake fitowa da irin kayan nan, yana kai karshen maganar ya juya yanufi toilet da sauri wai danma kar ya sake kallonta,

Kwas kwas kwas diyana ta juya jiki ba kwari ta nufi waje,

Aryan kuwa wanka yayi ya fito a gurguje ya shirya cikin kayan barchi riga da dogon wando masu kyau da tsada farare tas masu laushi, ganin dare yayi sosai yasa shi hayewa katafaren gadon sa batare da yashi coffee É—in ba ja blanket yayi zuwa chikin sa ya sage gudun A.c ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba dashi

*💫STAR LADY💫*

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 2️⃣6️⃣*

Misalin karfe 7 na safe Ammi na zaune a bakin katafaren gadon ta sanye take da wata ɗankareriyar lace baki mai zanen flower manya manya ajiki jaa, ɗinkin bubu gawn, ta sanya wani dan kareren sarkan gold a wuya ka wasu manya manyan abun hannu masu kyau da tsada a hannunta, sai kamshi take zubawa,kamar anyi ɓarin turare ajikinta

da sallama É—auke a bakin sa BGS ya shigo, kauda kai gefe Ammi tayi tana amsa sallamar, ganin hakan yasa BGS ya kariso chikin É—akin da sauri a gaban ta ya zauna saman lallausan karpet na alfarma dake shinfiÉ—e a É—akin, chikin sanyi murya ya fara magana "ina kwana Ammi, kara É—aure fuska sosai Ammi tayi kasa kasa ta amsa masa da lfy, kwantar da kansa yayi kan chinyar ta ya riko hannunta cikin ladabi da girmamawa yafara Magana "kiyi hakuri Ammi na, kinji nasan nayi laifi dayawa amma pls ki daina fushi dani kinji, kin fa san idan ki na fushi da ni, ina cikin fushin Ubangiji kuma kome nasa a gaba bazan yi nasara ba pls my Ammi for give me, É—an daka tawa yayi yana sauraron yaji me zata che

..... Hannu Ammi tasa ta fara shafa lallausan gashin kansa kafin tace "ni ba fushi nake da kai ba kuma ba zan iya fushi da kai ba saboda na san idan iyaye suna fushi da ƴa'ƴansu, wache bala'i mai girma suke jawa ƴaƴan nasu, kawai dai abun da ka keyi ne baya da chewa, "zan daina Ammi na duk wani abun da baki so ki faɗa min zan dai na "kayi alkawari "na miki alkawari Ammi na keche fa farin chikina lokachin da bana kasar nan kin ta ɓa ganin nayi 2 hours ban kira ki ba, kome aikin da nake sai na daka tar na kira ki koda na 5mnt ne, saboda kawai inji ya kike, "eh hakane na sani kuma kana da gaskiya

.... yanzu dai abu biyu ne kake yi a gidan nan yake ɓatamin rai, kuma nake son ka daina yi, da sauri BGS ya ɗago kai yana kallan ta, murnushi kaɗan Ammi ta sakar masa, shima wani cool murmushi wan da bai ta ɓayi ba ya sake har sai da dimple nashi ta lotsa, chigaba da magana Ammi tayi "ina son ka rage tsawar da ka kewa su hiyana abun yana damuna kaga marayune ba uwa ba uba pls ku jasu ajiki dan ku mantar da su marai chin nasu, kannen kane kai yaka mata kafi kowa sakar musu fuska da jansu ajiki,
Chapter 63 · 0% Book details