← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 90

Sashe 10

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwanche ta samu diyana sai kuka take "ita chikin muryan kuma tace diyana kitashi mutafi mu fara aikin mu tafaÉ—i hakan chikin shasshakar kuka "wlh hiyana bazan iya tashiba jinake kamar zan mutu chikina murdamin yake saboda yinwa "to diyana ya zamuyi kinsan dai in kika zauna inna ta dazo ta sameki duka zata kara Miki, kitashi muje saiki zauna a gonar yaya bello ni kuma na É—ebo ruwan "to zoki rikeni natashi, matsowa hiyana tayi ta kama kafaÉ—arata, ta tai maka mata tamike har tangal tangal take kamar zata faÉ—i da kyar ta tsaya a kan kafafunta aruÉ—e hiyana tace "diyana yanaga jini a jikin zanin ki wai ma ina ki kaje jiya
"a tsorache diyana tafara magana hiyana bansan ya akayi naga jininba nima, daga gabana ya fito
shiru hiyana ta É—anyi kafin tace to chanza kaya muje, zamuyi magana a hanya dan in muka tsaya magana a nan inna zatazo ta same mu, da sauri ta É—auko wa diyana wani tsunmar zanin atampa yasha ruwa duk ya koÉ—e ta É—aura mata, tariko hannun ta
da kyar diyana ke ɗaga kafa da kyar take ɗin gisa kafar tana tafiya suka fito tsakar gida, suka samu su amrat kowache takama aikin ta, amma kallo ɗaya zaka musu kasan suna chikin tashin hankali ga yinwa duk sun galabaita, girgiza kai kawai hiyana tayi, ta duƙa ta ɗauki cups ɗin data ajiye suka nufi waje

Suna futa hiyana tafara tambayar diyana "ina kikaje jiya diyana "jiya na kwantane awajen da kika barni sai barchi ya ɗauke ni ina chikin barchi kawai sainaji a'na kokarin chiremin zani, nabuɗe idona a razane sainaga bubane, da nayi kokarin guduwa shine yakamani ya wanka min mari, kuma yasa kafa ya takamin wuya ya chiremin zani, inata rokansa da ya kyaleni amma yaki da kyar na samu na laluɓi wani karfe nabuga masa a kafa, shine yachire kafarsa a wuyata yafaɗi kasa ni kuma natashi da kyar zan gudu kawai naji ya bugamin wani abu a kai daga nan kuma ban sake sanin komai ba saida inna ta zuba mana ruwa ɗazun ta kare maganar chikin shesshekar kuka "to ae na ki kasamu jinin jikin kin nan kuma "nifa hiyana nache miki ban'saniba kawai ganinsa nayi " jinjina kai hiyana tayi tana faɗin yazama wajibi muneman wa kammu mafita wlh " to yanzu ya zamuyi ke nan tayi maganar dai dai lokachin dasuka isa bakin rafin"hiyana tace ki bari inmun samu lokachi iri idan inna bata nan sai muje muyi magana da bappa, yanzu dai ki ɗebo ruwa ki wanke jinin jikin ki nan, san nan muyi al'wala kinsan jiyama bamuyi sallar azhar laasar mangariba da kuma issha ba, gashi yan zu kuma ana sallar asuba sai muhaɗa dukka,muje kasar itachen chan mubiya bashin sallolin kafin mufara ɗiban ruwa "to kawai diyana tace san nan tanufi bakin rafin ta ɗebo ruwa ta koma gefe ta wanke jikinta tas san nan sukayi al'wala suka nufi kar'kashi bishiyar mangoron suka shinfiɗa ɗan kwalin su suka ta da sallah,
sai da suka biyan bashin sallar da akebin su, najiya san nan sukayi sallah asuba

addua hiyana tai sosai" ya allah kayafewasu amra ba laifin su bane innache kehanasu yin sallah Allah mun'tuba haÉ—a sallah da muke Allah kayafe mana
diyana kuwa adduar Allah yakawo musu mafita take hakadai suka gama adduar san nan su kamike " hiyana tanufi bakin rafi tana faÉ—in diyana kishiga gonar yaya bello ki zauna ki huta, ruwa ta É—eba a cups É—in ta kama hanyar gd, ta kuma diyana tashiga chikin gonar yaya bello ta zauna da yake gonar a bakin rafin yake daga chikin gonar kana iya kallan chikin rafin

har karfe 8 na safe diyana na zaune a chikin gonar bello, hiyana kuwa saifaman jidan ruwa take ammafa da cups yan zuma taÉ—ebo ruwan takama hanyar gida tanajan kafarta da kyar da kyar har takai kusa da gida zata shiga ke nan, buba ya tare mata gaba É—aure fuska hiyana tayi sosai" babu kabani hanya
hannu buba yasa ya buge cups É—in dake hannunta yafaÉ—i kasa ruwan yazube, hiyana kamar zatayi kuka ta duka kasa ta É—auki cups din har kwallah yafara zuba a idan ta batachewa buba ko kalaba takama hanya tajuya tanufi hanyar komawa rafin, tana tafiya wasu siraran hawayene masu dumin gaske ke zuba mata a'kan kunchin ta.

haka takoma rafin tasake debo ruwan tajuyo ta zata tafi ke nan taga diyana a tsaya a bayan ta "hiyana kawo in karɓa miki kekuma kije ki huta tunda tun asuba kike deban ruwan nan "aa diyana kingafa ke baki da lfy dan haka kije ki zauna kibari zanyi "diyana tace aa to kawo nayi ko sahu 10 ne sai ki karba " sahu 10 yayi yawa diyana ki daiyi 3 "to bani cups din, mikama ta cups ɗin hiyana tayi, tawuche tanufi chikin gonar yaya bello
diyana kuma tanufi hanyar gida kodataje itama zata shiga gida buba tagani tsaye a bakin kofar gidan su batache masa ko sannuba tazo taraba gefen'sa zata wuche, buba ba tsoran Allah yasa hannun sa yasake buge cups din ruwan da diyana take da shi suka faɗi kasa ruwan ya zuɓe "a fusache diyana ta ɗago zatayi magana kome ta tuna kuma sai tafasa ta duƙa ta ɗauki cups din tajuya takama hanyar komawa rafin, buba kuwa yana ganin ta tafi yayi murmushi mugun ta cheke da izza da iya shege yafara magana,"ai kunshiga uku dani wlh bazan taba bari ku zauna lfy ba, narinka kuntata muku san nan kuma in na Auri hiyana in maida ta baiwar kowa na kauyen nan,dariya yayi sosai san nan ya chigaba da chewa kai amma goggo habiba ma yar aljanna che wlh ta iya horaku ɗeban ruwa da kofi ai shine maganin ku, a hakanma nikuma ba barin ku zanyiba, narinƙa addaban rayuwar ku kenan ina kifar da ruwan, yau sai kafarku ta daina takawa yasake kwashe wa da dariya kamar mahaukachi

diyana kuwa juyawa tai komawa rafin ta taÉ—ebo wani ruwan tanufo gida, ko datazo kofar gida ba'tasami buba'ba ba'karamin daÉ—i tajiba alhllh ta furta san nan tanufi gidan zata shiga, kamar daga sama taji an buge cups É—in hannunta sun faÉ—i kasa ruwan yazube
a fusache ta É—ago ganin bubane a gabanta hakan yasa tarufe ido ta zabga masa mari a kumatu
diyana daman bata da hakurin jure wulakanchi

buba kuwa bai'yi wata wata ba ya kwashe kafafunta tafaÉ—i kasa kanta ya bugu da jikin wani dutse dake bakin kofar gidan, wani ihu azaba ta sake, buba kuwa bai tau saya mata ba ya hau bugunta kamar ai aikoshi
diyana sai ihu take ganin zai mata illa babu wanda yakawo mata agaji yasa tamike da kyar tana kokarin guduwa
damkoh hijabinta yayi tabaya ya shake mata wuya ya bugata da kasa wani azaba taji gashi yaki sakin hijabin nata ga wuyan'ta a shake da gyar take numfashi ,tagama sad'dakkarwa mutuwa zatayi sae kuma taji buba yayi ihu kuma ya saketa "da kyar ta iya buÉ—e ido ta sauke su a kan yaya bello dake tsaye rike da sandar kiwo,sai huchi yake kamar wani zaki, ga buba kuma sume a kasa
hannu yaya bello yasa ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗarsa yanufi hanyar rafin da ita, nan sukabar buba kwanche, bello irin mazan nanne masu karfi gashi dogo sosai kakkarfa

kai tsaye gonarsa yanufa da ita hiyana na zaune taga yaya bello É—auke da diyana a kafadarsa
da sauri tamike tanufi'sa tana faÉ—in hande miboni yaya bello me kuma yasame'ta bello bai yi magana ba sai da ya isa wajen dayake zama inyazo gonar, wajen shinfiÉ—e yake da katifar chiyawa, akai ya kwantar da diyana da sauri hiyana ta karisa wajen ta zauna a kusa da diyana, tana fadin "diyana me yasame'ki waya bugeki waya pasa maki baki "hiyana kiyi shiru mana ki kyale'ta ta É—an huta tun da kika gammu tare ai koma me yafaru zakiji chewar bello" hiyana dai hankalin ta bai kwantaba mikewa bello yayi yana faÉ—in ina zuwa san nan yakama hanyar fita daga gonar
Chapter 10 · 0% Book details