← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 90

Sashe 87

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby diyana tunanin me kuma ki ke yi? "Babu komai yaya Aiman " "ya zaki chemin babu komai bayan nayi magana har sau biyu baki jiba"
"Babu komai wlh kawai kewar su hiyana nake ne shiyasa" "to ki dai na damuwa kinji? naji Abba yace jibi Aunty farida ta mai daki gida ai" "Da gaske yaya Aiman" "eh mana shiyasa ma ai zan koma ban damu ba dan nasan jibi kema zaki dawo gidan badan zaki dawo ba ai da nima bazan koma ba, yayi maganar dai dai lokachin da driver's ke parking na motochin a Parking space na Airport.

Da sauri Aiman ya fito yana faɗin "my wife saura 5mnt jirgin mu ya ɗaga sai munyi waya, bai jira amsar taba ya wuche ya nufi motar Aunty farida dai dai lokacin itama ta fito daga chikin motar, sallama sukayi ya wuche ya nufi jirgi yana tafiya yana waigo diyana mamaki ne ya kamashi tunani ya shigayi "me yasa diyana bata fito daga chikin mota ta masa bye bye ba, ɗayan ɓangaren na zuchiyar sa yace "kila kunyar ka takeji ne Shiyasa kabari sai ka koma ka kirata awaya, sai kaji dalili, da wan nan tunanin ya shiga jirgin sai da Aunty farida taga tashin jirgin su san nan ta koma chikin mota

A ɓangaren diyana kuwa tun da Yaya Aiman ya fita daga chikin motar take kuka hawaye sharɓe sharɓe, gaba ɗaya hawayen ya wanke mata fuska,surutu ta rinkayi shi dai driver yana jinta amma ko ɗago ido bai yi ya kalleta ba dan yana tsoron kallon nata saboda Aunty farida ta musu gargaɗi akan duk wanda aka kama yana kallon diyana zai karɓi hukunchi mai tsanani daga wajen mijin ta, hakan yasa gaba ɗaya masu aikin gidan suna tsoron idon su ta sauka a kan ta koda kuwa ta bayan tane.

Key driver's É—in sukawa motochin suka tayar suka nufi gida

KANO

kwanche yake saman katafaren gadon sa yana kallon sama yayi shiru kamar mai tunani hannun sa ya ɗago ya duba time a jikin dan ƙareriyar agogon gold dake manne a hannun sa, karfe 4:45pm mai da hannun nasa yayi gefe yana kwaɓe fuska karar wayar sa da ya jine alamar shigowar sako hakan ya sashi sa hannu yana lalubar wayar, chan daga ɗan gefensa ya jiyo wayar

Ɗauko wa yayi ya kawota dai dai sai tin fuskar sa,tare da kunna hasken screen ɗin ganin number da diyana ta kirashi shekaran jiyane ya bayyana akan screen ɗin hakan ya sa shi saurin meƙewa zaune tare da chire password ɗin wayar hannun sa har rawa yake wajen shiga massage

wow zafafan hotunan da Aunty farida ta ɗauki diyana ɗazun da zasu raka Aiman Airport ne aka turo masa sai dai an sanya wa hotunan backgrau an sanya wasu flower daga gefe gefe anyiwa hotunan kwalliya,ta yadda mutun ba zai gane a in da aka ɗauki hotunan ba zubur ya miƙe tsaye, tare da kurawa wayar ash eyes nashi ya kankame wayar sosai kamar wani yace zai kwache masa ita, daya bayan ɗaya yake kallon hotunan.

...nan take yaji jikin sa na rawa sai wani tsuma yake, ji yake kan sa ta masa nauyi gaskiya ina bukatar ganin matata a kusa dani dafe kan sa yayi ya koma ya zauna a gefen gadon a hankali ya fita daga wajen massage É—in ya shiga contact ya fara kokarin kiran layin diyanar amma a kashe, wurgi yayi da wayar tasa saman sofa, da karfi ya fara magana

"Wai wanene ya ke min wasa da hankali haka ne!? Abba da alama awan nan karon kashe ni kake son yi da kan ka, oh my god!! Kwan chiya yayi a saman gadon rabin jikin sa na sama kafafun sa kuma na kasa, haka yayi ta surutu har barchi yayi awon gaba dashi.

Washe gari misalin karfe 5:5Am kamar dai kullun yauma lallaɓowa tayi ta fito daga part ɗin Ammi ta nufi ɗakin da yaya Ahmad ke kwanche, da sallama ɗauke a bakin ta ta shigo kakar kullun yana kwanche saman gadon sa yau dai idon sa a lumshe kamar mai barchi

Gefen gadon hiyana taje ta zauna a hankali tafaÉ—a karan to masa addu'oe tana tofa masa jin motsin mutun a kusa dashi ne yasa ya waro manya manyan fararen idon sa akan kyakkyawar fuskar sai shekin alwala fuskar nata yake

"Yaya Ahmad ya jikin naka, abun mamaki sai taga ya girgiza mata kai alamar yana samun sauki, mikewa tayi tsaye da sauri tace "yaya Ahmad yanzu kana iya motsa jikin ka!? Hannun sa yaɗaga mata alamar ta gani yana iya motsa wasu daga chikin gaɓoɓin sa, murmushi tayi wadda yasa dimple nata ya lotsa tace "Alhadulillah kasan me yaya Ahmad? saura kwana ɗaya na gama haɗa maka ruwan addu'a ka kuma nasan kana sha In Sha Allah zaka samu sauki, amma yanzu in kawo maka wani abu ne? Ɗaga mata kai yayi san nan yamata nuni da hannun sa alamar ruwa yake son sha, da sauri ta fice daga ɗakin ta koma part ɗin Ammi ta ɗauko masa ruwan faro mai sanyi daga fridge ta fito ta nufi ɗakin.

Tun daga nesa ta hango Bgs yana kokarin shiga ɗakin yaya Ahmad ɗin, ɓata fuska tayi alamar bata ji daɗi ba dan taso tabawa yaya Ahmad ruwan addu'ar nan ya sha zai tai maka masa, amma babu hali dan kuwa bata isa ta shiga ɗakin Bgs na chiki ba juyawa tayi jiki ba kwari ta koma part ɗin Ammi

Ƙarfe 7 dai dai suka gama shirin zuwa school suka zauna a palon sama suna jiran yaya Khalid, sai ƙarfe 7:10 yaya Khalid ya shigo palon Ammi da Sallama ɗauke a bakin sa har suna haɗa baki wajen amsa masa Sallamar zama yayi saman sofa yana kallon su ɗaya bayan ɗaya chikin sanyin murya ya fara magana

"Yau ba zuwa school domin Abba ya karɓa muku transfer later za'a Chanza muku makaranta Amma sai ranar Monday yanzu dai kuje ku chire uniform ɗin ku shirya muje muchi abinchi" to kawai su kache san nan suka wuche suka nufi ɗakin su, shi kuma ya miƙe ya fice daga palon ya nufi palon Abba dan zuwa yin breakfast

Karfe 8:20 gaba ɗaya family Abba sun haɗu a palo dan yin breakfast ban da Aryan da Bgs, abin chi suke chikin nitsuwa da kwanchiyar hankali ɗan gyarar murya Abba yayi ya dubi Fahad da hiyana ya fara magana "kai Fahad je ka kuramin babban yayan ku, ke kuma hiyana je ki kiramin yaya Aryan kusan tare suka miƙe suka nufi waje hiyana ta nufi part ɗin yaya Aryan Fahad kuma ya nufi part ɗin Bgs.

Da sallama Fahad ya shaga betroom nashi zaune ya same'sa saman sofa yana latse latse a laptop "yaya prince Abba na kiran ka" shiru Bgs yayi kamar bai ma san da shigowar mutun ɗakin ba aikin dake gaban sa kawai yake, zama kusa dashi Fahad yayi ya sake mai mai ta maganar "yaya prince Abba na kiran ka" nan ma shiru yayi kamar bai jiba Almost 10mnt Fahad na zaune yana jiran amsar Bgs har ya fidda rai da samun amsa yana kokarin miƙewa sai yaji Bgs yana faɗin "ae na Abban yake? nauyayyar ajiyar zuchiya Fahad ya sauke kafin yace "yana palon sa kuma ya che kayi sauri" shiru Bgs yayi bai sake magana ba, Fahad dai da yaga Bgs bai da niyar sake yin magana sai ya kama kan sa ya fice daga ɗakin dan in da sabo ya saba da rashin maganar Bgs

Abangaren hiyana kuwa da sallama ta shiga part É—in yaya Aryan babu kowa a palon kasa haurawa tayi palon sama nan ma babu kowa, kofar betroom nashi ta nufa a hankali ta tura kofar tare da yin sallama ta shiga, tsaye yake gaban mirrow yana gyaran gashin kansa, sanye yake chikin wando jeans fari da bakar t-shirt chikin sanyin murya tace "yaya Aryan Abba na kiran ka" a sukwane Aryan ya juyo dan jin irin voice na diyana ganin hiyana che yasa yace "jeki ina zuwa, da sauri hiyana ta juya ta fice daga É—akin tana yabon irin kirkin yaya Aryan a zuchiyar ta.

Shi kuma juyawa yayi ya chigaba da gyaran gashin sa yana tunanin diyanar sa

Kusan tare Bgs da Aryan suka shigo palon taku suke da kagan su kaga jaruman sojoji Bgs na gaba Aryan na bin sa abaya, zulaihat dake zaune kusa da Aunty amarya ta zuba musu ido tunani ta shigayi "ashe ma hoton sa da na kalla ban ga komai ba, asai a fili yafi kyau wow gaskiya guy É—in nan ya hadu iya haÉ—uwa ba karya, har naji na kara son shi ga wannan faffadar kirjin nashi zai yi daÉ—in kwan chiya wlh kai gaskiya ayi sauri a É—aura mana Aure in ba haka ba zan kai masa kai na, dan ba zan iya hakuri ba.

Tayi nisa chikin tunanin sai ji tayi Aunty amarya ta taɓa ta a ɗan firgiche ta ɗago ido tana kallon ta alama da ido Aunty amarya ta mata akan ta gaishe dasu Bgs, dawo da kallon ta kansu tayi chikin rawan kai ta yanga tace "hiii prince y kk tirkashi gaba ɗaya jamaa palon sai da suka ɗago suna kallon ta banda Aryan Bgs da kuma Fahad.

Murmushi Yusuf yayi a zuchiyar'sa yace "tab aiko ga wadda zata bi sahun yar sarki Zaria, Khalid kuwa dariya ma taba shi amma sai ya danne dan yasan idan yayi dariya tofa tabbas Bgs zai iya ɓaɓɓalla yarinyar nan, Haidar Umar mamaki ne ya kama su, ko su dasu kannen sa basu taɓa che masa wani hii ba bare ita da basu ma san daga in da ta fitoba kwashe kwashen Aunty Amarya ta kwaso ta, Abba kam tunani yake gai suwar mutunci ma akayi wa Safras yau she yake amsawa bare wani hii lallai su hii anji jiki
Chapter 87 · 0% Book details