← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 90

Sashe 77

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chikin sanyin murya tace "ni ba wanda ya taɓani kawai nayi kuka ne saboda an mai da kanwata garinmu,
"Eyya to sorry kinji kije class idan an tashi break kizo muyi hira dan ina missing naki sosai, ko dai ke baki missing na ne? Ya karisa maganar yana É—an dukar da kai yana leka fuskan ta dayake ta sunkuyar da kan kasa, shiru tayi bata sake che masa komai ba, ganin bata da niyar magana ne yasa yace "to kije class É—in idan antashi sai kizo na kawo miki tsaraba
Bata jira ya karisa maganar shiba ta shige class nasu da sauri, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya juya ya nufi nasu class É—in

Sosai Bgs yake sauri kamar zai tashi sama taku yake irin na sadaukin yaki, yazo dai dai zai shiga ɓangaren Aryan, yajiyo muryan Abba daga bayan sa yana faɗin "jirani mushiga tare, batare da ya juyoba ya tsaya har Abba ya kariso, wajen a tare suka jera zuwa chikin part ɗin,

"Menene ya hana Aryan zuwa sallar asuba Abba ya tambaya yayi maganar dai dai lokachin da zasu haura stair case É—in chikin palon Aryan,

"Abba wlh nima ban saniba abun da nazo tambayar sa kenan, shiru Abba yayi bai sake chewa komai ba, har suka karisa betroom É—in, da sallama suka shiga a tare

Kwanche yake saman katafaren gadon sa,yana sharara barchin, da mamaki Abba ya juyo ya kalli Bgs wadda shima Abba yake kallo..

....Karisawa bakin gadon sukayi a tare zama Abba yayi a gefen gadon shi kuma Bgs ya haye saman gadon ya ɗan jayye bargon da Aryan ya lulluɓu, zuba masa ido Bgs yayi sosai kamar mai karantar wani abu a kan face nashi

"Abba da alama É—an uwana bai yi barchi jiya da daddare ba koda kuma yayi to kaÉ—an ne, ka duba time fa yanzu Almost 8:5am amma yana barchi ko sallar asuba bai yiba, anya Aryan yana da lfy kuwa? Dogon numfashi Abba yaja kafin yace "kila akoi abun da ya tsare sa ya hana shi barchi da wurine.

Guntun tsaki Bgs yaja sannan yasa hannu yana É—an bubbuga hannun Aryan,
"Aa Safras ka barshi mana yayi barchin sa chewar Abba "aa Abba ya tashi dai kofa sallar asuba bai yiba ya tashi idan yayi Sallah sai ya koma barchin, shiru Abba yayi bai sake Magana ba, bubbuga Aryan Bgs yake yana kiran sunan sa "my blood, my blood

Da kyar Aryan ya iya waro ash eyes nashi nan, sun chanza sunyi jaa saboda barchi chikin muryan barchi yace "Bgs lfy? ÆŠaure fuska Bgs yayi kafin yace "zaka tashi kaje kayi sallar asuba ne ko dai sai na maka 1bloo 7 die,

Wani sallar asuban kuma? I Already nayi sallar ton asuba ɗin, yayi maganar yana kokarin miƙewa zaune, da kyar ya iya miƙewa zaune, da sauri yasa hannu ya dafe kansa dan ji yake kamar kan nashi zata faɗi kasa ga wani azaban chiwo da take masa, sai sara masa kan keyi kamar zai fashe,

Ganin Aryan ya dafe kai ne yasa Bgs saurin kai hannunsa saman goshin Aryan É—in yana faÉ—in "my blood lfy? Menne? Kai É—inne ke maka chiwo? Karisa hayewa gadon Abba ma yayi ya sa hannun'sa ya riko kan Aryan yana faÉ—in

"Aryan meke damun kane? É—ago jajayen idon sa yayi yana binsu da kallo ganin yadda suka ruÉ—ene yasa ya É—an kakalo murmushi gefen fuska, da kyar ya iya motsa lallausan red lips nashi ya furta "bb komai, a tare Bgs da Abba suka chire hannun su daga saman goshin nasa,

Aryan me yasa baka je masallaci da asuba ba? Chewar Abba yayi maganar yana sauƙa daga gadon, "Abba makara nayi wlh, lokachin da natashi already an gama Sallah "me yasamu wayar ka? na kiraka da asuba ai a kashe, Bgs ya tambaya yana kallon face nashi,
"Eh Ni na kashe wayar jiya da daddare, to akan idan nazo barchi zan kunna sai na manta

Shiru Bgs ya É—an yi kafin ya chiro wayar sa daga aljihu wandon sa, ya kunna hasken screen É—in ya chire password ya shiga contact nashi, layin Fahad ya fara kira ringing É—aya Fahad ya É—aga

"Hello big bro, ina kwana, "lfy Fahad, baki buÉ—e Abba da yaya Aryan ke kallon Bgs tunani Abba yake wai daman Bgs ya iya amsa gaisuwa tab lallai Fahad yarone mai Sa'a ya chire tuta a gidan nan, kaiii

Yaya Aryan ma tunani yake anya na taɓajin Bgs yana amsa gaisuwar wani ko wata kuwa? Yayi iya tunanin sa duk bai tunano in da Bgs ya taɓa ansa gaisuwa ba kwata kwata, ko awajen Aiki yaran mu zasu gaishe sa sai dai ya ɗaga musu hannu ko kuma ya musu alamar yaji da ido, ashe daman yasan yadda ake amsa gaisuwar kenan? Lallai yaya prince sai dai nace Allah ya shirya min kai.

"Fahad ka kawomin coffee mai zafi ka haÉ—o da hot milk, ina É—akin Aryan yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran.

..dawo da green eyes nashi yayi kan Aryan dake zaune ya zuba masa nashi Ash eyes É—in shima yana kallon sa
"Aryan lfy kake kallo na haka? Kawar da kallon sa gefe Aryan yayi zai yi magana sai Abba ya rigashi da chewa "ba dole ya kalleka ba daman ka iya amsa gaisuwa? Dawo da kallon sa Bgs yayi kan face É—in Abba yace "na iya Abba "au ka iya shine idan aka gaida ka baka amsawa "wlh Abba bawai da gangan nake kin amsawa ba, kawai ni ban son magana ne Allah harchena nauyi ya kemin idan zanyi magana

"Ba shakka Safras nima shaida ne ba tun yanzu ba haka aka haifeka baka son yawan magana amma dai karinƙa daurewa kana Amsa gaisuwar yan uwan ka, shiru yayi bai sake chiwa komai ba

A hankali Aryan ya zuro kafar sa kasa kafin ya sauko daga gadon, jiki ba kwari ya miƙe ya nufi toilet, wani irin jirine ta kwashesa batare da ya shirya ba kawai sai dai yajisa a faffadar kirjin Bgs, kara waro ash eyes nashi waje yayi, yana kallon face ɗin Bgs yayin da shima Bgs ɗin shi yake kallo

"Aryan baka da lfy ne? Abba ya tambaya yana karasowa wajen su, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi yace "aa Abba lfy na kalau kawai kai nane ke ɗan min chiwo sai jiri da nake gani, ɗan duƙawa Bgs yayi batare da yayi Magana ba ya saɓi Aryan a kafadar sa ya nufi toilet ɗin dashi,

komawa gefen gadon Abba yayi ya zauna yana tunani " lallai Aryan ai ka makara ita soyayya baa nuna mata jaruntar, ai san da zaka kawo kanka ma ba wan da ya sani, Ni kuma inshaa Allah sai na koyamaka sanin darajar mace sai kasan chewa mace halittace mai daraja Abba yayi nisa chikin tunanin sa, bai maga shigowar Fahad ba sai dai yaga mutun yana ƙoƙarin hawa gado yana faɗin
"Abba ina kwana, murnushi Abba ya sakarwa Fahad kafin yace "lfy ka tashi lfy, fuskar nan a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, da kaga Fahad ba sai an faɗa maka chewa kanin Bgs bane, zaka gane domin komai nasu iri ɗaya, kaman nin su ɗaya irin yadda Bgs ke haɗe fuska haka shima Fahad ke yi, rashin son maganar su ma irin ɗaya komai dai na Fahad sak na Bgs, dan yanzu ma da Abba yace katashi lfy Fahad, bai amsa ba sai ma kara ɗaure fuska da yayi ya zaro wayarsa yana latsawa, Abba kam ko ajikinsa dan gaba ɗaya ƴa'ƴan sa ba wanda bai san halin su ba,
Hannun su riƙe chikin na juna Bgs da Aryan suka fito daga toilet ɗin, da alama brush Aryan yayi, saman gadon suka haye, Bgs yace "Fahad ina coffee ɗin, Fahad ba tare da yayi magana ba ya sauko daga gadon ya nufi table ɗin tsakiyar ɗakin ya ɗauko kwakkyawar plate mai ɗauke da haɗaɗɗun cups guda 5 kowani cup an rufeshi da ɗan karamin plate mai kyau, bakin gadon ya dawo ya tsaya yana faɗin "gashi nan, ɗago green eyes nashi Bgs yayi yana kallon Fahad, da mamaki yace
"Fahad coffee da hot milk kawai nace ka kawomin ya naga cups har guda biyar?

"Eh to ai naji kache kana ɗakin yaya Aryan ne shiyasa na haɗo muku kai da shi ni kuma na haɗawa kai na black tea dan nima na taya ku sha, kaga cups 2 naka 2 na yaya Aryan, ɗaya'n nan kuma nawa, girgiza kai Bgs yayi yana faɗin "to ai daman Aryan nace ka haɗawa coffee ba Ni ba Ni kataɓa ganina inashan coffee ne? Kaje ka ajiye a saman table ɗin, bari mu sauko, juyawa Fahad yayi ya maida plate ɗin saman table sannan ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1, yanan jiransu
Miƙewa Abba yayi yana faɗin sai kun fito fada sannan ya nufi hanyar fita, Aryan ne kawai ya amsa wa Abba da to

A tare suka sauko daga gadon suka nufi Fahad dake zaune saman sofa yana latsa waya.

A saman sofa mai zaman mutun 3 suka zauna da sauri Fahad ya miƙe ya ɗauko cup mai ɗauke da coffee ya miƙawa Aryan, sannan ya ɗauko cup mai ɗauke da hot milk ya miƙawa Bgs shi kuma ya ɗauki black tea ɗin sa ya koma ya zauna, shiru sukayi

A hankali Bgs ke ɗan korɓan hot milk ɗin haka zalika Fahad yana latsa waya yana ɗan kurban Black tea, Aryan kuwa ya riƙe cup ɗin ya kasa kai wa bakin sa yayi shiru kamar mai tunani

"Aryan me kake tunani? Meke damunka? Bgs ya jefo masa tambaya, ajiyar zuchiya ya sauƙe kafin yace "babu komai my blood bana jin sha coffee ɗin ne bakina ba ɗan ɗano
Chapter 77 · 0% Book details