← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 90

Sashe 78

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ajiye cup É—in hannun sa Bgs yayi sannan ya juyo da kyau yana kallon Aryan "Aryan wai nikam yaushe kadawo ragon namiji ne? Waro manya manyan ashe eyes nashi waje Aryan yayi a sukwane ya juyo da kyau shima yana kallon Bgs, da mamaki "rago ya mai mai ta kalmar chike da jin haushin dan gantashi da kalmar da Bgs yayi, nan take kuma yaji wani karsashi yazo masa, ji yayi duk wata damuwa ta gudu domin ba abun da ya tsana arayuwa iri amasa kallon ya gaza ko kuma yana da rauni ko dai ache masa rago.
Ganin yayi shirune yasa Bgs yace "me ya sauya kane Aryan? da alama fa yanzu kafara zama... da sauri Aryan ya sa hannu ya rufe masa baki bai bari ya karisa maganar ba domi ba zai iya jin taba, zuba masa green eyes nashi kawai Bgs yayi yana kallon face É—in sa

A hankali Aryan ya zame hannun'sa daga bakin Bgs san nan ya ɗauki cup ɗin coffee sa ya fara sha, juyawa Bgs ma yayi ya ɗauki hot milk nashi ya chigaba da kurɓa a hankali, shiru sukayi ba wanda ya sake magana

YOLA

da sallama Inna habiba ta shiga gidan su buba, da kyar take iya jan kafarta, har ta karisa tsakar gida, inna yaya Bello da innar buba suna zaune saman tabarma guda, inna yaya Bello tana shafawa innar buba magani a kafarta daya kumbura sosai yayi wani green kamar ya ruɓe,

Saman ta barman Inna habiba taje ta zauna "sannun ki da zuwa habiba Chewar Innan yaya Bello, wani harara inna ta wurgawa inna yaya Bello, tana faɗin "to ai ba wajenki na zoba munafuka sai ki tashi ki bamu waje, ajiye robar maganin hannun ta innar yaya Bello tayi tana kokarin miƙewa,

Da sauri innar buba ta riƙe hannun ta tana faɗin "aa innar bello dalla kiyi zaman ki, ki rabu da habiba, bata da hankali ne, waro ido waje inna tayi chikin tsawa tace "ke larai ni zaki chewa bani da hankali eh, au yanzu da wannan munafukar kika haɗa kai,kenan? "habiba ki daina zagin min yar uwa wlh idan ba haka ba zamusa yaranmu su miki duka tsiya,

Wani dariya Inna tayi har da shewa kafin tace yanzu ne kika san dachewa ita yar uwarki che ko? to wlh idan baki dawo chikin hankalin ki ba Allah sai na tona asirin duk abu da kika aikata wa yaron ta Bello, dariya Innar buba tayi kafin tace
"Ki tona mana, dan Allah habiba ki tona ni bani da wata damuwa idan kin tona saboda nasan bello da innar sa, zuchiyar su ba irin na dabbobi bane wlh duk kauyen nan babu mutanen kirki kamarsu ki duba duk kuntatawa rayuwansu da nayi hakan bai hanasu taimako na lokachin dana shiga halin mutuwa ko rayuwaba, alhamdulillah kuma ni nasamu na roki gafarar su kuma sun ya femin, ke ma wlh idan dai baki tuba ba to karshen ki ba zaiyi kyau ba, ko da yake ko kin tubama dole sai kin karɓi azaba da hukunchi, domin Allah baya yafe hakkin wani bawan, sai dai idan bawan shiya yafe maki da kansa, to kuma aina zaki ga bappa ki roƙi gafarar sa ina zakiga su hiyana da mahaifiyar su, duk babu wlh habiba kekam kinshiga uku

A fusache inna ta miƙe ta ɗaga hannu zata zabgawa innar buba mari, chikin tsawa Bello dake tsaye a bayan su tun ɗazun yace "wlh kina marin ta sai na shemeki da sandar nan, a tsorache inna ta juyo da sauri dan tasan Bello akoi shi da zuchiya sosai kuma idan yace zaiyi abu tofa zai yi ne "zo ki fita mana a gida Bello ya faɗa yana nuna mata hanyar fita da hannun sa, ba musu ta kama hanya fita tana jan kafa a hankali hankali har ta fice daga gidan

Karisawa yaya Bello yayi wajen su inna ya zauna gefen innarsa yana faÉ—in "innar buba kinsha maganin ki kuwa? "eh bello nasha ni dai ba abun da zanche muku sai dai in muku fatan alkhairin kuna da kyakkyawar zuchiya
"Ki daina faÉ—in haka Inna ai duk abun da muka miki yiwa kaine kuma ai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya faÉ—a chewa idan kana tare da mutun yana aikata abun da ba dai dai ba to karka kyamachesa karka gujesa ko da ka masa wa'azi bai jiba karka damu ka jashi a jiki kana masa alkhairin a hankali kana nuna masa abun da ya keyi ba mai kyau bane sannan kana binsa da addu'a, sai kiga Allah ya shirya shi ya chanza hali ya dai na, ba wai idan kaga mutun yana abun da bai dache ba sai kaje ka zauna kana zaginsa kana tsine masa a chikin mutane ba, yanzu ba gashi da muka jaki ajiki bamu je wajen kowa mun zage kiba bamuyi gulmar ki da kowa ba bagashi Allah da ikonsa ya shirya mana ke ba, kin gane gaskiya

Ajiyar zuchiya Innar buba ta sauke kafin tace "hakane Bello zancheka gaskiyane to Allah dai yasa itama habiba ta gane Allah É—aya ne, a tare innar yaya Bello da yaya Bello suka haÉ—a baki wajen chewa Amin,
Miƙewa innar yaya Bello tayi tana faɗin bari naje na ɗora mana girkin safe dan yau naga kamar hasana batajin daɗi,
miƙewa yaya Bello ma yayi ya nufi ɗakin sa dan ya duba jikin matar tashi, suka bar innar buba ita kaɗai,

Maiduguri

Da gudu junior ya fito daga É—akin su diyana na biye dashi a baya tana faÉ—in "wlh idan na kama ka zakayi bayani da harchen larabchi, kai tsaye É—akin Aunty farida suka nufa,

Aunty farida na kwamche saman katafaren gadon tana shararan barchinta chikin kwanchiyar hankali, kamar daga sama taji diran mutane a kanta, a sukwane ta farka ta miƙe zaune, ganin Aunty farida ta miƙe zaune ne yasa junior ya faɗa jikin ta yana faɗin "na ɓuya ai, dafe kai Aunty farida tayi tace "my diyana zonan ki zauna, ba musu diyana ta zauna kusa da ita ta zuba mata ido

"My diyana kina jina, gyaÉ—a mata kai diyana tayi alamar eh chigaba da magana Aunty farida tayi, "my diyana yanzu fa kin girma bai kamata kina wasan guje guje ba kinji ko? GyaÉ—a mata kai diyana tayi alamar taji, "good yanzu dai kutashi kuje palo ku fara breakfast ina zuwa, bari nayi wanka "Aunty farida yaushe zaki mai dani gida? Diyana ta tambaya
"My diyana ki saurareni da kyau kiji me zan faÉ—a miki, gida ba yanzu zaki koma ba, anjima dady'n junior zai dauke ki kuje yamiki registration a school nasu junior, ki fara zuwa school kinaji na ko? Turo baki diyana tayi kamar zatayi kuka tace "Aunty farida nikam ina son komawa gida Allah, ina son ganin yaya Aryan dasu Ammi,

"My Diyana yaya Aryan fa ya koma London, dan haka ki daina tunanin sa gida kuma zamuje nan da wata 3 kinji yanzu dai kuje Aunty jummai ta zuba muku abinchi kuyi breakfast ina zuwa,

Jiki ba kwari diyana ta miƙe ta riko hannu junior suka fito daga ɗakin, ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke kafin tace "gaskiya ina da aiki babba kafin na sauya ki my diyana, dan ba abun da kika sani sai shirme da wasa
A hankali ta zuro kafar ta kasa sannan ta miƙe ta nufi toilet

KANO

Misalin karfe 3:10 dankareriyar family ka dake É—auko su hiyana daga school che ta kutso kai ta chika katafaren gate É—in gidan, kai tsaye parking space driver ya nufa, tun bai gama gashe motar ba hiyana ta buÉ—e kofar ta fito da sauri ta nufi part É—in Ammi,
Da sallama ta shigo palon betroom É—in Ammi ta wuche kai tsaye, da sallama É—auke a bakinta ta shiga

Ammi na zaune a bakin gadon ta, tana riƙe da littafin addu'oe, gaban ta hiyaba tazo ta tsugunna ta sunkuyar da kai kasa
da wanna zazzakar kuma sanyayyar muryan nata tace "barka da rana Ammi,

"Hiyana lfy bakije kin chire uniform ba eh? Ammi ta tambaya tana ɗago haɓar hiyana da hannun ta, "Ammi daman nazo in roke ki ne dan Allah ni ki mai dani kauye sai ki dawo da diyana nan, kinji ni zan iya jure duk wata wahala, kuma zan iya hakuri da halin inna da buba, na san diyana bazata iya hakuri ba kome buba ya mata zata che zata rama kuma wlh Ammi dukan mutu buba yake mata tsoro nakeji kar su kasheta shiya gara ni ki kai ni chan sai ki dawo da diyana nan.

tsabar tausayi Ammi batasan lokachin da kwalla ya chika mata ido ba har yana kokarin zubowa, gaskiya hiyana mutunche, wadda samun irinta a duniyar yanzu akoi wahala ya Allah kasa ta zama matar É—aya daga chikin Æ´aÆ´ana

"Ki kwantar da hankalin hiyana kinji, diyana bata kauye, tana chan wajen wata kawata hajj fatima dake zaune a saudia, ammafa karki faÉ—awa kowa kinji ko an tambaye ki, kiche tana kauye

É—ago blue eyes nata tayi ta É—an saki murmushi har sai da dimple nata ya bayya, tace "to Ammi bazan faÉ—aba "yauwa my hiyana koke fa kinga yadda kika kara kyau da kikayi murmushi nan kuwa? To yanzu dai ki tashi kije ki chire uniform kiyi wanka kuzo kuchi abinchi, karki kara saka wata damuwa a ranki, "to kawai hiyana tace sanna ta mike da murnar ta har sauri take tanufi kofar fita

Tana tura kofar zata fita shi kuma yana shigowa karo sukayi kanta ya bugi faffaÉ—ar kirjinsa nan kasan chewar ya fita tsawo sosai, waro blue eyes nata tayi nan take tafara ganin jiri, baya baya tayi tana kokarin faÉ—uwa..

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

More comments an like pls

*💫STAR LADY💫*33

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3️⃣3️⃣*
Chapter 78 · 0% Book details