← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 90

Sashe 45

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama ta dawo palon Ummi, duk datasan ba kowa, kai tsaye ɗakin'ta tawuce, tasamu diyana da amrat sunyi barchi ,"kayan jikin'ta ta chire san nan nufi toilet, after 45 mnt tafi ɗaure da towel da'alama wanka tayi, trolley ta tajawo, ta buɗe ta ɗauki kayan barchi, masu kyau da tsada farare tas masu laushin gaske, sai kamshi kayan keyi yasha turarukkan maiduguri,san nan ta ɗauko mayukan'ta masu kanshi da tsada sai dataɓi ko'ina na jikinta ta shafeshi da mai san nan,tasanya kayan barchi ta'sake feshe jikinta da turare sai kamshi take kamar anyi ɓarin turare a jikinta, "ta mai da mai da tureren chikin trolley ɗin ta rufe ta mai'dashi wajen zamansa, tadawo kan gadon ta gyarawa amrat kwan chiya, san nan ta kwanta a gefensu, tare dayin adduar barchi asuba ta gari

Yau yakama Wednesday tun safe Aunty farida ta shirya chikin tsadaddiyar lace mai Bala'i kyau baki, da ratsin ja ta zuba sarkan gold a wuya da hannunta, ta jera wasu tsadaddun zobuna uku na gold a hannunta, tayi simple make up bakaramin kyau tayiba sai kamshi take zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikinta, tasa plat shoe ja da mayafi ja san nan tayiwa yan matan Ammi kwalliya sosai, "diyana hiyana Zahra tasasu sukasa wani haɗaɗɗen duguwar riga mai kyan gaske, da pink colour an masa kwalliya da wasu duwatsu golden colour, bakaramin kyau sukayiba amrat da lamrat kuwa sun sa wandon jeans baki da yellow t-shirt," gaba ɗayan'su ta ɗaure musu gashin nasu a tsakiyar kai ta zuba musu jelar a baya, sai dai ita hiyana har yanzu ba a chire bandejin dake goshinta'ba "Aunty farida ina zamuje kika mana kwalliya haka diyana ta tambaya tana kokarin gyara mayafin rigar" wajen lalle da gyaranjiki zan kai ku, da naso namuku lalle da kaina to amma nayi tu nanin gara na kai'ku ae muku har da gyaran jiki " tsalle diyana tayi ta rungume Aunty farida tana faɗin mungode sosai" to sakeni mutafi kar lokachi ya kure mana " to diyana tafaɗi tare da sakin Aunty farida" rike hannunta Aunty farida tayi sukayi gaba, su Zahra suka rufa musu baya,
suna fita harabar gd da gudu Shahram yanufo'su " ɗan dukar da kai yayi ya gaishe da Aunty farida chikin harchen turanci" bayan yagama gaishe da Aunty farida,su Zahra ma suka gaidashi " bayan yagama amsa gaisuwar'su Zahra ne, ya tambayi Aunty farida ko zai iya kaisu inda zasuje da kanshi " Aunty farida tace badamuwa ya fito da family car dan tafisan sutafi dukkan'su a mota ɗaya " da gudu yajuya yanufi parking space na gidan," har gabansu yazo yayi parking,"zai fito yabuɗe'musu " Aunty farida ta ɗaga masa hannu, alamar yabari zasu ɓuɗe da kansu " da Kanta tasa hannu ta buɗe kofar motar," a nitse suka fara shiga sai da suka gama shiga san nan tabi bayansu " da gudu gaske Shahram yaja motar yana zuwa bakin gate ya ɗan rage gudun motar nan'take securitys dake wajen suka wangale masa gate ɗin da'gudu ya danna hanchin motar waje, gudu sosai, Shahram ke shararawa a kan mikakkiyar titi " ranki ya daɗe ina muka nufa yayi tambayar yana kokarin fita daga asalin babban gate ɗin gidan " A&S muka nufa tabashi amsa ta kokarin picking call ɗin daya shigo wayarta " miƙar hanya Shahram yayi sosai yake sharara gudu
Yana hawa kan titi dazata sadashi da gate ɗin A&S ya rage gudun motar,horn ɗaya yayi wani dattijo ya taso ya wangale masu gate ɗin da'alama shine mai gaɗin " A nitse Shahram ya danna hanchin motar chiki, parking space na wajen yanufa yana kashe motar yafito da sauri ya buɗewa Aunty farida" a hankali ta zuro kafafunta waje ta fito "su hiyana ma sukabi bayanta hannu diyana tariƙe suka nufi chiki " wani haɗadɗen wajen gyaran jikine da lalle da kitso, wajen ya tsaru sosai iya matane kaɗai ke shiga koka'kawo wani naka sai dai katsaya awajen zaman baki, suna da ma aikata sosai inkaje basai kabi layiba, " hannu bibbiyu a ka tarbi su Aunty farida " chikin ƙankanin lokachi aka fara gyara musu jiki

YOLA

Da gudu inna tafito daga ɗaki, tayi kichin, da sauri ta sauke tukunyar ɗumamen, dake kan wutar abinchin har yayi bakin'kirin, zama tayi dirshan awajen kamar zatayi kuka tafara surutai,"oh ni habiba yanzu me zanchi wayyo Allah gashi ba azumi nake ba dole naje nasake ɗaukar 1k a chikin kuɗin nan na sawo masara nazo na surfa na niƙa nayi wani tuwon, mikewa tayi ta jawo itacen wutar ta kashe san nan ta wuche ɗaki ta ɗaga katifar chiyawar'ta ta irga kuɗin taga saura 6k ta zari 1k ta mai da sauran kasan katifar ta ɗau mayafinta tafuto tanufi waje dan zuwa yin chefene

KANO

A bangaren'su Aunty farida kuwa sai gyaranjiki ake musu an gama yiwa diyana da zahra da amrat bakaramin kyau sukayiba, kamar wasu larabawa haka suka zama daman, dukkansu fararene tas jikinsu sai kyalli yake gwanin ban sha'awa,
yanzu aka fara yiwa lamrat da hiyana kuma,"Aunty farida kam already tariga da tayi nata a Maiduguri kafin tazo, " yanzu lalle za'afara yiwa diyana da zahra " sai zolayar'su Aunty farida keyi " my diyana kingan'ki kuwa kamar wata sarauniyar kyau fa kinga fatar nan taki kuwa saikace na jariri gaskiya dole..bata karisaba, wayar'ta tafara ƙara alamar shigowar ƙira da sauri ta chiro wayar kiran iphone 14 daga jakarta " laaa Aunty farida yaushe kika chanza waya chewar diyana " last week tayi maganar tana kokarin picking call ɗin " hello my bro ykk "lfy lau my lovely Aunty ykk y gd " lfy lau alhamdulillah gamu nan ma awajen gyaran jiki ae ina Prince " baya nan yayi tafiyar sirri " murmushi tayi kafin tace kai Aryan dayayi tafiyar sirri nasan yace karka faɗawa kowa, shine kuma kafaɗamin " murmushi kaɗan shima ma yayi san nan yace ae ke da kankima sirrinmu'ce ko bazamu faɗawa kowaba yazama dole ke kisani, " inasu Khalid to " suntafi kasuwa " to yau kuma da kansu sukaje kasuwar " eh wlh nima dai na ɗanyi mamaki " kodai Zahra yaje yiwa tsaraba " to waya sanin musu zaki gane kan Khalid da Yusuf ne " to shike nan bari innakima gd mayi magana " ok ya'jikin yaran nan " da sauki sosai gasu nan ma ana musu lalle " lalle kuma ya tambaya yana taɓe baki " eh lalle mana kona baku ku gaisane " eh to dai kibari sai kun koma gd zaifi tunda yanzu kince lalle ake musu " ok to shike nan sai munyi waya," ta karisa maganar tana chire wayar daga kunnen'ta " katse kiran tayi tamaida wayar chikin jaka san nan ta ɗago tana kallan'su diyana da akewa lalle " wow my sister's kunganku kuwa kaman wasu amare gaskiaya idan Ammi suka dawo bazasu gane kuba wow " diyana dai baki yaki rufuwa sai murmushi take " Zahra kuma hannu tasa ta rufe fuska tana dariya " bayan angama yiwa Zahra da diyana lalle " aka fara yiwa amrat da lamrat

SAUDIA

Ammi che kwanche a kan chiyar Abba a ɗakinsu tana shafa fuskar'sa yayinda shikuma yake shafa gashin kanta " ranka yadaɗe nayi kewar yanmata'na sosai, " hannu Abba yasa yaɗan ja dogon hanchin nan nata yana faɗin to kwana nawa yarage mukoma, ɗazun ma munyi waya da farida take chimin zasuje wajen gyaran jiki " Allah sarki feeda baiwar Allah, Allah yamata albarka na mata adduar samun aihuwa sosai jiya danaje masallaci " kullun sainayiwa farida adduar bama ita kaɗaiba har da maryam da mardiya ba garama faridan tasamu ɗaya ba sauran kam aiko ɗayan basu samuba,chewar Abba " wlh tausayi suke bani tayi maganar tana kokarin mikewa " da sauri Abba ya rikota yana faɗin ina zakije kuma " so nake naje nayi magana da yaron nan " kallan chikin kwayar idonta sosai Abba yayi san nan yace wani yaro kuma, da gangan yamata tabayar, dan yanasan yau yaji takira sunan Safras da bakinta " yaron Ummin nan mana tabashi amsa tana mai kawar da kai gefe " to shi yaron bai da sunane " juyo da kallan'ta tayi kansa san nan tasa hannu taja gemunsa chikin wasa take faɗin, bazadai kaji su nan a baki'naba " murmushi yayi yana faɗin to idan inasan inji kumafa " sai na kira maka mana ae duk abun da kakeso matikar bai saɓawa Allah da manzon'saba dole namaka " rungumeta Abba yayi chikin farinchiki yafara magana ina kaunarki Aisha'ta nima bazan saki yin abun da baki so ba, tunda ba kyasan kiran su nan bazan saki kiraba aje a yaron kinji " chusa kanta tayi kirjin'sa tana faɗin nima ae ina kaunarka sosaima " nasani Aisha nasan kina kauna'na sosai nasani wlh " to shike nan kamin izzini naje na dubo'shi dan jiya banganshi'ba kwata kwata kuma inasan magana dashi a kan yaran nan " aa Aish ba yanzuba dan yanzu bansan ki raba jikinki danawa kibari sai anjima " to kawai Ammi tace takara shigewa jikinsa ta lafe

Da sallama Khalid da Yusuf suka shigo palon hannun'su ɗauke da manya manyan jakun'kunar sayayya Aiman da Ahmad dake zaune saman Sofa suka amsa sallamar suna binsu da kallo " daga ina kuke haka Aiman ya tambaya yana ɗaure fuska " to dakake ɗaure mana fuska, saiyasa muji tsoranka mufaɗa'maka inda mukaje ne chewar Khalid " dariya Ahmad yayi yana faɗin nidai babu ruwana " tsaki Khalid yaja yawuce yanufi hanyar ɗakin'sa " da sauri Yusuf ma yabi bayansa " miƙewa Aiman yayi yana faɗin lokachi yayi da zan gano mekuke kullawa kuma sai nayi maganin'ku " Ahmad kam binsa kawai yake da ido har yafice daga palon ,yana ganin Aiman yafita " ya kwashe da dariya, chikin dariya yake magana wlh nidai nawa ido kawai zanga wan nan game ɗin yasake kwashewa da dariya yana mai kwanchiya a kan kujerar

NIGERIA
Chapter 45 · 0% Book details