← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 90

Sashe 61

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama hiyana tazo tayi awajen da ta tashi ta É—auki spoon a hankali tafara chin abinchin ta, shiru shiru DON bai zoba da har suka gama chin abinchin, Abba ya dubi Khalid rai a É—an bace yace "kai baba tashi kaje ka chewa Safras nifa na haife shi ba shi ya haifeni ba da zai ajiye'ni ina jiran sa, Khalid na kokarin mikewa, sai ga DON ya shi go sanye chikin jallabiya fari, yana taku irin na jaruman maza, fuskar san nan kamar bai san menen dariya ba sai wani kakkau da kai yake, gaba É—aya su Aunty Maryam kowa ya shiga taitayin sa, har da Aunty amaryan, kujerar dake fuskantar Abba yaje ya zauna da sauri kannen nasu suka fara É—aga masa gaisuwa, bai ko kalli inda suke ba bare ya amsa musu gaisuwar sai ma kara É—aure fuska da yayi, sai da suka gama gai suwar nasu sukayi shiru kowa ya nitsu suna sauraren suji abun da Abba zai che.

A hankali DON ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi kamar bai san motsa lallausan lips nashi, ya fara gaishe da iyayen nasu, fiska ba yabo ba fallasa Abba ya amsa haka Aunty amarya da Ummi, Ammi kuwa ɗaure fuska tayi sosai kafin ta amsa masa,Shiru yayi san nan ya sun kuyar da kai, shiru palon yayi gaba ɗaya Abban ne ya katse musu shirun da chewa "Zahra kutashi kuba mu waje, tun bai kai karshen maganar ba Zahra hiyana diyana lamrat amrat suka miƙe suka bar palon,

dawo da kallansa kan su DON Abba yayi yafara Magana "abun da yasa na taraku a nan shine, duk kanku lokachi yayi da zakuyi Aure, a sukwane DON Aryan Fahad haidar Aiman da kuma Ahmad suka ɗago kai a tare suna kallon Abba kamar zasuyi ihu musam man DON Aryan Fahad Aiman,su nasu ɓachin ran na da ban ne kamar wayan da aka chewa uban su ya mutu, Khalid Yusuf Umar kam ko ajikinsu, Aunty farida ma ɓata rai tayi sosai dan tasan wan nan maganar da Abba yayi ba karamin ɗagawa su DON hankali zai yiba, dan babu hakan a tsarin su, tafiso a barsu sunemi mata chikin nitsuwa, dan idan akache za'a tilasta musu wlh duk wadda aka aura musu tashiga uku,

"No Abba No gaskiya kabar wan nan maganar ni babu mace a tsarin rayuwa kamin wani hukunchin dai amma banda batun mace pls Abba, chewar DON, ya karisa maganar chikin wata iriyar voice wadda da kajita kasan tsantsar kiyayyar macece a ranshi,ga fiskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa, shiru Abba yayi ya zubawa DON ido har yakai karshen maganar tashi, shi kanshi Abba yasan chewa mawuya chin abune DON Aryan su yarda da batun Aure, domin babu hakan a tsarin da sukayi wa rayuwar su,shiyasa ma bai takura musu ba tsawon lokachi ya bar su, to amma yanzu yazama dole suyi Aure dan chika sunnan ma aiki, kuma yafi son su kawo matan da zasu Aura da kansu dan idan yace zai Aura musu zaɓin sane, yasan matan sun shiga uku

sosai Abba yashiga tunani, gaskiya bai kamata nayiwa DON dole ba idan yayi haka tofa akoi babban matsala tsabar tsanar mace dayayi ne jiba agaban kannen sa yau ya buÉ—e murya haka yana magana har da chewa sorry mutumin da magana wahala yi take masa, lallai bai kamata na takura masa ba idan kuwa nayi haka zanyi dana sani mai girma, addu'a kawai ya kamata na masa.

Ganin Abba yayi shirune yasa Aryan chewa "Abba pls kabar maganar auren nan wlh ba muso babu mace a tsarin rayuwar mu pls my Abba kaji ya karisa maganar yana ɗan dafa hannun Abba, chikin fushi Ammi tace "babu mace a tsarin rayuwar ku ko, to ku chiremu muma a tsarin rayuwar ku tunda muma matane tana kaiwa nan ta miƙe ta fiche daga palon chikin fushi da ɓachin rai, dafe kai DON yayi a zuchiyar'sa yana faɗin jiya nayi ɗaya yau kuma na biyu am so so sorry Ammi ammafa aure kam ba zan yi ba gaskiya sai dai duk abun da zai faru ya faru, miƙewa Ummi tayi itama tana faɗin "ranka ya daɗe idan kun gama zaman ka kira malam mai rukiyya yazo ya musu dan ga dukkan alamu aljana che ta auri ƴa'ƴan nan, a sukwane suka juyo gaba ɗayan su suna kallon Ummi, ɗaure fuska tayi kafin ta juya ta fice daga palon, kallan Aunty amarya Abba yayi tun bai yi magana ba ta miƙe ta fita tana ɓata rai dan taso jin me Abba zai che musu wani amsa zai basu, "Maryam salma mardiya kutashi ku bamu waje,chewar Abba yayi maganar yana kallon su, jiki ba kwari suka miƙe suka fita.

Palon ya rage daga Aunty farida, DON Khalid Yusuf Aryan Aiman Ahmad Umar haihar da kuma Fahad

Dawo da kallansa Abba yayi kansu DON ko'wannen su sai faman ɗaure fuska yake sai wani chi chijewa suke, ɗan gyaran murya Abba yayi kafin yafara Magana "ke farida na barki ne saboda bakin ku ɗaya dasu ke che sirrin su basu taɓayin wani abu batare da kin sani ba dan haka ku saurareni, "ni bazan tilas ta muku kuyi Aure ba, wani dauyayyar ajiya zuchiya DON Aryan Fahad, suka sauke a tare, har da ɗan sakin fuska, ganin hakan yasa Abba murmushi yachi gaba da chewa "bazan takura muku kuyi abun da baku so ba, saboda farin cikin ku nake bukata, amma dai burina shine naga kunyi aure kun haifamin jikoki shine babba burina a duniya kuma farinchiki na, ni ina san farin chikin ku ban sani ba ko kuma kunason nawa, ban sani ba ko zaku iya chika min burina tun ina raye, ɗan dakatawa Abba yayi yana satar kallon fuskokin su,a ransa yana faɗin nina haifeku ai baku kuka haifeni ba a chikin ruwan sanyi zanyi maganin ku, nan take fuskar DON da Aryan ya sauya sosai dan sun gano tarko Abba ke neman yima'su da kalaman sa, Fahad kuwa sai murna yake Abba bazai yimasu dole suyi aure ba, shiru Aiman yayi ya ɗora hannu a gemun sa yana kallon kasa yana nazarin magan ganun Abba, Khalid da Yusuf kuwa ɓata rai sukayi sosai dan su gaskiya Aure suke so kuma suna da matan da zasu aura, amma DON da Aryan suna neman watsa musu farin chiki, Aunty farida kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai jin kalaman Abba, tabbas Abba na da gaskiya yakama suyi aure amma banso Abba yabi musu ta wan nan sigar ba da an bi a hankali an bisu da addu'a inshaa Allah komai zai tafi dai dai

Ganin sunyi shiru kowan nan su yatafi tunani yasa Abba chewa, "nifa ban takura'wa kowa daga chikin kuba, burina da kuma farinchiki na kawai na faÉ—a muku, kuma ban che dole sai kun chika min burina ba koma me ni zan zama mai chika muku burin,kuma mai saku farin chiki a ko da yaushe, kuje ku zauna kunitsu kuyi tunani yana kai karshen maganar yamike ya shige betroom É—in sa,

chikin fushi da ɓachin rai DON ya furta "never Abba aure fa, wlh I cannot do it I cannot do it gaskiya bazan iya chika maka wan nan burin nakaba, a fusache ya miƙe ya bar palon, da sauri Aryan ya miƙe zai bi bayan sa "ina zakaje Aryan Aunty farida ta tambaya, "Aunty farida baki ganin ɗan uwana yana chikin ɓachin rai ne ai bazan iya zama ba, yana kai karshen maganar batare daya jira amsar taba ya fiche da sauri, a fusache Aiman ma ya mike yaja tsaki yana faɗin "nima dai ba zan iya chika'wa Abba wan nan burin na shi ba sai dai in ku zaku iya bani da lokachin mace yanzu, yana kai karshen maganar ya juya da, sauri ya nufi hanyar fita dan bai dan Aunty farida ta. dakatar da shi

Girgiza kai Khalid yayi kafin yache "gaskiya a wan nan gaɓar ya kamata mu chika wa Abba burinsa, domin duk wani abun da mukeso yana mana yanzu ki duba Aunty babba saboda bama son mulkin nan, Abba ya hakura da bamu mulkin duk dan muyi farin chiki, tun muna yara har muka girma har izuwa yanzu bamu taɓa chewa Abba muna bukatar abu kuma yaki yi mana ba, to meyasa mu kuma zamu rinƙa kin abun da yake so, yache zai bamu mulki munki ya hakura yanzu kuma kin fa ji auren mu shine kaɗai burin daya rage masa a duniya da yake san mu chika masa,to why bazamu chika masa burin sa ba. ɗan daka tawa Khalid yayi da magana yana mai da numfashi "Kana da gaskiya Khalid amma a hankali Ya kamata abi abun tun da kaga dukkan ku ba soyayya kuka taɓayiba babu wata alaka da ta taɓa haɗaku da wata mace idan ba mu yan uwan ku na gida ba, SO kaga abune mawuyache lokachi ɗaya a che zaayi muku maganar aure garama kai dasu Yusuf da sauki, amma kafini sanin halin DON da Aryan, basu san wani abu wai shi soyayya ba, bai da che amusu zuwa ɗaya haka ba a hankali za'a shawo kansu, yanzu dai zanje in same'su dan musan abunyi tana kai karshen maganar ta miƙe tanufi hanyar fita, shiru Khalid yayi yana tunani, miƙewa Fahad ma yayi yabi bayan Aunty farida, haidar da umar ma suƙa miƙe suka fita suka nufi ɓan garensu palon ya rage Khalid Ahmad Yusuf.

*💫STAR LADY💫*

👑UK Writers👑

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 2️⃣5️⃣*
Chapter 61 · 0% Book details