← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 90

Sashe 83

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aryan idan fa baka faÉ—awa Abba chewa Son ta kake ba wlh zai iya bawa wani bare Aure'n ta"
Chika tsawa Aryan yace "No Aunty farida hakan ma ba zai yiwuba ni dai kawai yanzu kiwa Abba magana ya dawo da ita san nan kuma karki faɗa masa nache ina Son ta" to shikenan Aryan, ɗazun nan ma Aiman ya shigo" "ok to Aunty Babba kinga kwakwalwa Aiman na gab da samun matsala saboda rashin lfy Ahmad shiyasa ma muka zaɓi mu turashi wajen ki wata kila idan baya ganin Ahmad ɗin, zai iya mantawa da wasu abubuwan, pls Aunty farida bama sai na faɗa miki ba karki barshi ya rinƙa zama shi ka ɗai bare ya samu daman yin tunani gida ki mantar da shi komai, ki lallaɓa ki samo masa mata a cikin family mijin ki, ki haɗasu dan a haɗa Auren mu gaba ɗaya zanso hakan"
"Eh hakan zai yi daɗi kam zan yi iya bakin kokarina, Khalid da Yusuf su already suna da natan su, saura Shi ogan naku da Aiman da Fahad, sai wayan chan marasa jin haidar da Umar, Allah ya tashi kafadun Ahmad shima yabi sahun ku" "amin kawai Aryan yace daga nan sukayi sallama, ya kashe wayar ya ajiye a gefe guda san nan ya miƙe da kyar ya nufi toilet.

Aɓangaren Aunty farida kuwa tana gama waya da Aryan tafara Neman layin Abba, kira ɗaya Abba ya ɗaga chikin zumuɗi "tace Assalamu alaikum Abba na albishir" da faraa Abba yace "goro my daughter"
"Abba yau Aryan da kansa ya furtamin yana Son diyana kuma wlh duk hiran da mukayi nayi recordined" "wow my daughter gaskiya nafi kowa murna da hakan dole namiki kyauta mai girman gaske saboda tun bayan Aihuwar ku baa taɓa bani lbr mai dadin wan nan ba" "to Abba yanzu ya kamata diyana ta dawo gida dan wlh Aryan na chikin damuwa sosai bakaji yadda naji voice nashi ba kamar bai da lfy "
"Za'a dawo da ita my daughter amma ba this week ba sai next, dan ina son in masa surprise ne. "To shike nan Abba na sai munyi waya" tana gama faÉ—in hakan Abba ya katse kiran, sai faman murmushi yake

Washe gari tun asuba Hiyana ta lallaɓo ta fito daga part ɗin Ammi ta nufi ɗakin yaya Ahmad, kamar dai kullum yauma haka ta same'sa, gefensa kaɗan ta zauna tafara karanto masa addu'a kamar yadda ta saba, tanayi tana hawaye sosai almost 10mnt ta ɗauka tana masa addu'a bayan ta gama ne ta ɗago kai tana kallonsa yayin da shima ita yake kallo chikin sanyin murya tace
"Yaya Ahmad kanajin sauki kuwa? Murmushi yayi tare da lunshe idon sa ya sake buɗe wa, alamar Eh ba karamin daɗi tajiba ganin yadda ya chanza yanzu har hasken sa ya fara dawowa ya fara dawowa dai dai kamar da, tayi nisa chikin tunani, kamar daga sama taji tsayuwar mutun a kanta a ruɗe ta ɗago blue eyes nata taga dai babu kowa yan waige waige tafara yi still dai bata ga kowa a ɗakin ba, miƙewa tayi chikin tsoro tana faɗin "yaya Ahmad sai gobe kuma idan nazo... Bata karisa rufe bakiba wani iska mai karfin gaske ya hanƙaɗata ta faɗi ka buge da jikin gadon, da karfi ta furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil, nan take is kan ya tsaya chak wani karfi taji yazo mata ta miƙe da sauri har tana haɗawa da gudu ta nufi waje.

Tana fita tayi karo da Bgs shi kuma yana shigowa, baya baya tayi ta faÉ—i kasa chikin tsawa "yace ke me kikeyi a nan!? "Muryan na rawata tace "kayi hakuri yaya prince daman nazo duba jikin yaya Ahmad ne" É—ago hannun sa yayi yana kallon É—ankareriyar agogon gold dake manne a hannun sa, karfe 5:10Am dawo da kallonsa kanta yayi duk da chewa wajen akoi É—an duhu baya ganinta sosai hakan bai hanashi fahimtar chewa tabbas wan nan É—aya daga chikin yaran da Ammi ta É—auko daga Yola bane dan yasan Zahra dai bazata zo nan wajen at this time ba, batare da ya sake magana ba ya tsallake ta ya wuche ya shege É—akin da yaya Ahmad É—in ke kwanche

Ita kuwa jiki ba kwari ta mike ta nufi part É—in, Ammi

Yana shiga É—akin ya É—aga ido yana kallon sama a hankali ya fara magana "ya kamata na samu time na duba Camera nan fa ko kuma nasa ko Fahad ne ya duba min, dan ya kama nasan suwaye da waye ke shigowa É—akin nan, kuma meke kawosu zan yi kokari naga na binchiki Cameran gaskiya, dan ni ban yarda da kowaba.

Sauko da ido sa yayi kan Ahmad dake kwanche, a hankali ya taka zuwa wajen gadon kasa kasa yace "Allah ya baka lfy my bro, bari muje masallaci sai mun dawo yana kai karshen maganar ya juya da sauri ya fice daga É—akin.

To kwanche tashi babu wuya awajen Allah yau dai diyana na da 2 week's a Maiduguri wajen Aunty farida dan ta

Yauma kamar kullun sanye take chikin doguwar riga abaya pink colour ta tsantsara make up ɗin ta kamar ka sache ta dan kyau, ta goge tayi kyau sosai takara haske da chika fatar jikin tannan kuwa kamar kitaɓa jini ya fito, sai ɗaukan ido take kamar madubi, taku take a hankali ta sauko daga stair case ɗin ta shigo chikin palon a tsakiyar palon ta tsaya kamar mai tunani, da ɗan karfi tace "yes yauwa na tuna jiya ai yaya Aiman ya sayamin sim card ya kamata na kira yaya Aryan tun da na san number sa, da sauri ta juya ta koma ɗakin ta

ÆŠauko wayar ta tayi ta fito palo ta zauna saman sofa mai zaman mutun 3 kunna hasken screen É—in wayar tayi, sauri sauri ta shiga contact É—in ta babu number kowa awajen daga na yaya Aiman sai na Aunty farida, shiru ta É—anyi na yan second ni da sauri kuma tafara rubuta number sa tana gamawa ta danna call wayar tayi ringing har ta katse bai É—agaba, sake kira tayi nanma bai É—aga ba sai a garo na uku ya É—aga chikin faÉ—a ya fara magana

"Wai wanene ke neman ta kuramin ne? Chike da zumuɗi tace "yaya Aryan ni ne fa" zubur ya miƙe tsaye muryan sa har rawa yake yace "ke ina ki ke ina Abba ya kai..... Bai karisa maganar ba yaji an katse kirar, da sauri ya chiro wayar daga kunnen sa yabi kiran Amma ina layin akashe sau uku yana gwadawa amma a kashe wani irin raɗaɗi yaji zuchiyar sa na masa na dama ya farayi yana faɗin " dama ban ji voice nata ba da yafi min yanzu zata sake jefani chikin tashin hankali, wurgi yayi da wayar gefe guda ya dafe saitin zuchiyarsa a hankali ya koma ya zauna a gefen gadon.

Aɓan garen diyana kuwa wani wawan mari Aunty farida ta sakar mata bayan ta ansa wayar tata ta kashe chikin tsawa tafar magana "ke bakyaji ko? eh wato ni ban isa in sa ki abu ko in hana kiba koh? Sokike Allah ya isan Abba ya kamani ko? Chikin kuka diyana tafara magana "kiyi hakuri Aunty farida na kasa mantawa da yaya Aryan ne shiyasa amma namiki alkawarin bazan sake ba" nan take Aunty farida taji jikinta yayi sanyi kuma tayi na damar marin'ta da tayi Allah sarki So kenan

Zama tayi gefenta ta rungumo ta tafara magana "ya isa my diyana kinji kiyi shiru, ni banche ki manta da yaya Aryan ba ki chigaba da tunanin sa In Sha Allah next week ma zamuje gida sai kiga yaya Aryan É—in naki kinji ki share hawayen ki ya isa haka" chike da zumuÉ—i da farinchiki diyana ta goge hawayen ta tana faÉ—in "amma Aunty farida idan mukaje gida a chan zaki barni ko? "Eh mana my diyana ai daman mai dake zanyi" dariya diyana tayi kamar ba ita bache mai kuka yanzun nan, a wan nan yanayin Aiman ya shigo ya same'su

Saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna yana faɗin "to baby diyana me kuma ya faru naga sai murna kike? "Yaya Aiman zan koma gida mana shiyasa nake murna, miƙewa Aunty farida tayi ta ɗauki wayar diyana ta wuche ta haye sama ta barsu awajen,

"Baby diyana yau kinyi kyau sosai, sun kuyar da kai diyana tayi saɓanin da, idan an che mata tayi kyau sai tafara dariya, tana farin ciki.

"Yaya Aiman nagode kuma kai ma ai kayi kyau sosai" "to taso kizo na mana hoto kinji my baby chikin nitsuwa ta miƙe ta karisa wajen da yake zaune saman hannun kujerar da yake zaune ta zauna, chiro wayar sa yayi ya rinƙa ɗaukan su pic masu kyau sai murnushi suke su dukka, bayan ya gamane ta miƙe ta koma kujerar ta ta zauna suka chigaba da hirar su

KANO

Sis Love yana ga kin rame ne kwana biyun nan Zahra dake zaune kusa dashi ta ɗago kai zatayi magana kenan dai dai lokachin Bgs ya shigo palon da sallama ɗauke a ɗan karamin bakin nan nashi, fuskar nan tashi kamar wani hadari a ɗaure take tam, sanye yake chikin wando jeans baki da t-shirt blue ba ƙaramin kyau kayan suka masa ba, asalin halittar jikin sa ya bayyana faffadar kirjin san nan a tsaye take tam, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fasa rigar saboda chika

nan take Zahra ta miƙe jiki na rawa tace "sannu da shigowa yaya prince ina wuni, shiru ya ɗanyi yana kallon Khalid dake zaune ko kallon in da Bgs ɗin yake bayyi ba dan baya son su haɗa ido chikin tsawa yace "ke wuche ki bamu waje, ai tun bai kai karshen maganar ba Zahra ta nufi hanyar ɗakin su da gudu har tana tuntunɓe
Chapter 83 · 0% Book details