← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 90

Sashe 32

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ammi tace sukuma sungadone daga wajen kakanmu namiji kuma duk family mu ma sukaɗai sukayi saar samun blue eyes ɗin kakanmu namiji shi ɗan asalin kasar sudanne yazo nageria, a garin jimeta yola, yahadu da kakamu mace yana santa sosai iyayenta sukache bazasu bashi itaba, sai dai idan zai zauna a rugarasu haka yayarda ya auri kakanmu kuma suka zauna a ruga harsuka haifi babana, da kanwarsa ɗaya allah yayiwa kakanmu rasuwa, kakanmu mace kuwa babana yayi auri umma'ta Kuma duk a'ruga ɗaya suke kuma a chan suka zauna an haifenima bajimawa kakanmu tarasu itama, kanwar babana kuwa bayan an haifi kanina Ahmadu babansu hiyana ke nan itama tarasu daga nan babanmu ya ƙaura daga rugar chikin yola yakoma rugar jimeta, a nan mukachigaba da rayuwa
Rayuwar farinchiki muke sosai kanina da babana suje kiwo nikuma naje tallar nono a wajen tallar nono na haÉ—u da Mai martaba yabini har gida, da kyar babana yabasa aurena to na bayan aure ba jimawa innata tarasu, yarage saura baba da Ahmadu haka mukachi gaba da rayuwa bayardda mai martaba baiyi dasuba akan sudawo nan kano sunki har gida yasaya musu Amma sunki wai babu inda zasuje da waÉ—an nan uban shanaye babanmu yana da shanu dayawa kusan 700 ga awaki da raguna kaji da zabbi hakadai sukachigaba da zama a ruga
Kolokachin dana haifi yayanku sunki zuwa mota mai martaba yatura a É—auko su amma sunki zuwa, babana ko yaki zuwane saboda niche yar fari Ahmadu kuma yaki zuwane saboda shine mai zuwa kiwon dabbobinmu kai intakaichemuku har babanmu yarasu Ahmadu yayi aure basu taba zuwa wajena ba saidai ninaje
Nidinma kunsan yanayin gidan nan sainafi shekara uku banjeba nanma saina matsa da kyar mai marbata yake barina, akoi lokachin dana É—auki tsawon shekara 6 banje naduba Ahmadu ba a shakara ta 7 É—inne nayita rokar mai martaba da kyar ya'yarda yabarni naje"
Danajene masamu fati matar Ahmadu ta haifi ƴaƴa har uku hiyana diyana dakuma lamrat san nan ga chikin na hudu ajikinta nasha mamaki sosai shine nachewa Ahmadu tunda yanzu bamuda iyaye yadawo kano kusa dani yaki yarda, wai inyadawo yazaiyi da dabbobinsa, nachemasa musayar yaki yarda wai bazai bar garin iyaye da kakanniba haka na hakura na kyalesa nasaya' waya nabashi amma yaki karɓa wai baiso bayadda na iya haka nadawo na kyalesa
Sai danasake É—aukan shekara 4 kafin nasake komawa kauye alokachin danaje nasamu mamansu hiyana tarasu wajen aihuwar amrat Ahmadu kuma ya auri habiba dan tachigaba da kulamasa da yara alokachinma saidana roki Ahmadu daya dawo kano amma yaki narokesa yabani hiyana da diyana nanma yaki ninasan halinsa da kafiya shine na kyalesa kuma tundaga wan nan lokachin dana dawo bansake zuwa kauyeba sai zuwan nan danayi na samu Ahmadu yarasu na daukoh su hiyana " dogon numfashi yusuf yaja san nan yace. Tab lallai Ammi kina da hakuri sosai wlh allah dai yajikansu da rahma " gaba É—aya palon suka amsa da amin " duba time yusuf yayi san nan yace. da Khalid muje koh mangariba ta kawo kai " mikewa sukayi a tare yusuf narike da hannun lamrat sukayi wajen " Ammi tace'wa su hiyana kutashi kuje kufara shirye shiryen kayan buÉ—a baki tare suma sukamike suka nufi palon kasa" Ammi ma tamike tayi É—akinta

Misalin karfe 7 na dare gaba ɗaya family suna palo dan yin buɗa baki amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali shiru ba mai magana saidai karan spoon " diyana tace. Abba kasan me " sai dakowa yaɗago yana kallanta da mamaki " mai martaba kuwa chewa yayi aa diyana ta bansaniba sai kinfaɗa " dariya diyana tayi tace wai uncle Omar na makarantar mune yace yana sona " what chewar mai marbata " a'sukwane Aryan yaɗago manya manyan idan nan nanshi yana kallanta a jafafe yabuɗe baki.....✍️✍️

Amin afuwa masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kaimu more love

Pls more comments an share

*💫STAR LADY💫*

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 12*

A zafafe Aryan yace ke kima mutane shiru a nan "idon kowa na palon yadawo kan Aryan ya turnuke fuskar nan tamkar an aiko masa da sakon mutuwa " Yusuf da Khalid kuwa sai murnushi suke "Abba ya dube'sa kana yace "ina ruwan ka, kai takewa hirane, chigaba da faÉ—amin Æ´ata ya kukayi kasanima ko dashi zaayi bikin " Aryan zai sake magana idonsa yasauka kan aunty amarya dake wurga masa mugun kallo ganin hakan yasa yamike yabar palan

.....dariya diyana tayi san nan tace "Abba nifa matar sojane soja zan aura irin mugayen sojojin nan masu manya manya bindiga " Ammi ganin diyana tafara sakin layi yasa tamata magana da harchen fullanchi tache tatashi suje suyi sallar mangariba " ba musu suka miƙe suka nufi ɗakin su " Aunty amarya mikewa tayi tafiche sai huchi take " mai martaba yace dasu Yusuf kutashi mutafi masallachi mikewa sukayi gaba ɗaya matasan suka fiche " Ammi ta dubi Ummi tace yakamata muma muje muyi sallah Koh, atare suka mike suka fita

Misalin karfe 8 na dare gaba ɗayansu sunhadu a palo dan chin abinchin dare amma banda DON da kuma Aryan basuzoba " yusuf ne yakalli diyana yace sister jiki dubo yaya Aryan a daki kiche yazo muchi abinchi " to diyana tace tare da mikewa zata fita " kamar daga sama sukaji Aunty amarya tana faɗin ke dawo kizauna Umar tashi kaje ka kirashi " kallo mai martaba yusuf yayi kana yajuya ya kalli Khalid zaiyi magana ke nan Abba yarigasa da chewa "jeki kirasa diyana da sauri ta fita daga palon dan ganin mugun kallon da Aunty amarya ke mata " farinchikine ya lulluɓe Khalid da Yusuf sai murnushi suke
Chapter 32 · 0% Book details