← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 90

Sashe 41

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsu DON yake sosai kamar mai nazarin wani abu a fiskokinsu wuchewa yayi ya zauna a bakin gadon " calmly yafara magana me yake damunka Aryan wan nan shine tambaya ta karshe da zanmaka idan baƙa faɗaminba kasan sauran " kakalo murmushi dole Aryan yayi yana faɗin wai meyasa kakesan saka wani tunanin banza a zuchiyar kane, nifa nafaɗama kwanan nan ina yawan fama da chiwon kaine amma bari namaka mai kankat wlh Allah nikam bawani abun dake damuna, kawai jinake tamkar a takure nake banajin daɗin ƙasar nan narasa meke min daɗin banda haka wlh babu wani abun " jinjina kai kawai DON yayi batare dayache komaiba, dan yasan iya gaskiya ke nan Aryan yafaɗa masa dan bayadda za'ayi Aryan yayi rantsuwa a kan karya kuma tabbas zai iya shedan Aryan a ko ina baya faɗin maganar da ba hakaba, to amma tabbas yana da damuwar da shi da kansa baisan da itaba " ganin DON yayi nshirune yasa gaba ɗayansu suka dawo kusa dashi, dafa kafaɗarsa Aryan yayi yana faɗin baka yarda da magana ta bane " juyo green eyes ɗinsa yayi kan face ɗin Aryan tare da ɗanyin murmushi gefen fuska nayarda mana na yarda da duk abun da kafaɗa domin baƙa taba yimini karyaba matsalar ɗaya a nan shine tabbas akoi abun da kedamunka wanda kai da kanka bakasan meneneba " zuba musu ido khalid yayi yana tunani a chikin ransa gaskiyane DON kachi su nanka Safras indai wajen basirane kai karshene ba abanza mai marbata ya dage sai kai za abawa sarauta'ba, yayi nisa chikin tunani sai yaji Aryan nataɓasa firgigit yayi ya ɗago yana kallonsu duk sun zuba masa ido " lfy Khalid kodai kaima kana da damuwane DON yajefo masa tambaya " aa bani da damuwar komai nikam kawai tunanin meke damuna ɗan uwana nake " nifa babu abun dake damuna na faɗa muku " DON zaiyi magana wayarsa tafara ringing hannu yasa chikin aljihunsa ya fitar da wayar, sunan Sadiq yagani ta bayyana a kan screen ɗin wayar dogon tsaki yaja tare da jefar da wayar a kan gado " da sauri Khalid yasa hannu ya ɗauki wayar yana duba wanene yakira DON yake jan tsaki haka ganin sunan Sadiq yayi a kan screen ɗin bai yi mamakiba, dan DON yaki ɗaukar wayar Sadiq dan kuwa Sadiq yayi aure " murmushi yayi yana kokarin picking na call ɗin kiran tayanke chire pin na wayar yayi dayake yasan pin na wayoyinsu dan ba abun dasuke ɓuyewa juna
Kiran layin Sadiq ɗin yafarayi wayar nafara ringing Sadiq yayi picking call ɗin yana faɗin yau wace rana nayi sa'a an ɗauki wayata " dariya Khalid yayi san nan yace ai kasan shikam bazai ɗauki wayarkaba " my Khalid ykk " lfu lau ya amarya suhaima " first dai yanzu albishirinka " da sauri Khalid yace goro " my baby ta haifamin baby boy yanzun nan daman shi nakira nafaɗa muku " wow my man inatayaka murna bari nabawa Aryan ma yatayaka murna " Khalid bai jira amsar Sadiq ba yamiƙawa Aryan wayar " satar kallan DON Aryan yayi yaga bama su yake kalloba yasa hannu ya'karɓi wayar yawa Sadiq congrat san nan yace ga DON nan, kuma da gangan yayiwa DON ɗin haka dan yasan idan shi yamiƙawa DON wayar tofa dole zaikarɓa kuma gaskiya yanasan DON yataya Sadiq murna kodan halakchin da Sadiq ɗin yamusu, yanzu matarsa na aihuwa tun bai sanar da kowaba yafara sanar musu, aiko basaso dole zasu danne sumasa congrat " karbar wayar DON yayi badan yasoba kawai dan bazai iya kwasale Aryan a idon kowa bane

Congratulations inatayaka murna chewar DON " da murna Sadiq yace thanks ykk y gd " lfy yasu mom " alhamdulillah Sadiq yabashi amsa " ok kawai DON yace san nan ya katse kiran ya É—ago green eyes nashi yana kallonsu " zuba mishi ido Aryan da khalid sukayi sosai suna kallansa Khalid na mamakin hali irin na DON " kallon me kukemin haka " murmushi Khalid yayi san nan yace kyau kamana mana shiyasa muke kallanka " mikewa yayi yana faÉ—in to aiki yasameku kuda kukasanma me kyau yake nufi, yana gama faÉ—in hakan yayi waje " dariya Khalid yayi sosai san nan ya dubi Aryan yana faÉ—in wai gaji DON baisan me kyau ba kajimin iskachi " tsaki Aryan yaja yana faÉ—in kai ma kake biye masa ae, to daman inban da kai da neman magama ina DON yasan maka wani abu Wai shi kyau, ko kuma mara kyau ai shi inba Bom, bindiga, bullet,ba to bawani abun dayasani mai kyau " mikewa Khalid yayi yana faÉ—in good night anjima kakira Shahram kaji ya ake chiki " da sauri Aryan yafara lalubar wayarsa yana faÉ—in yanzu dai wani anjima kuma, wan nan ke nan

Nigeria DON hospital

Washe gari misalin karfe 8 dinaya na kwanche a gado da drip a hannu " hiyana ma kwanche a nata gadon ansamata bandeji a goshi " sai lamrat da amrat dake zaune gefen gadon hiyana, zahra kuma tana kan kujera plastic dake chikin ɗaki " shiru sukayi gaba ɗayansu na tsawon lokachi " sallama sukaji a bakin kofar ɗago kai sukayi gaba ɗayansu Shahram suka gani tsaye shida Dr Peter karisa shigowa chiki ɗakin sukayi suna tattaunawa " mikewa Zahra tayi daga kan kujerar ta koma gefen gadon diyana tana kana tacewa Shahram, uncle have a seat " thanks dear san nan ya zauna a kujerar " miƙamasa takardar magani Dr Peter yayi san nan ya juya yanufi waje " Shahram kuwa wayarsa ya ɗaukoh daga aljihun wandansa yafara kiran layin Aryan, har saida wayar takusa tsinkewa tukun nan a ka ɗaga
Chikin girmamawa Shahram yafara magana hello sir good morning " morning how are U " am fine sir " where is she da sauri Shahram ya mikawa diyana wayar " hannu tasa ta amsa ta ƙara a kunne hello yaya Aryan ina kwana " lfy y jiki " da sauki ina Ammi dan Allah yaya Aryan kafaɗawa Ammi ta dawo dan Allah wlh tsoran Aunty Maryam nakeji, nikam Ammi tazo taje tasayar da shanun Bappa gaba ɗaya tasaya mana gida mukoma " shiru kawai Aryan yayi yana sauraron'ta har ta kai karshe " chikin sanyin murya yafara magana karki damu ae munkusa dawowa saura 9 days ne kawai kuma kinga nafaɗa miki Aunty farida zatazo next week idan Aunty farida na nan babu abun da Maryam zata muku, yanzuma bazan barku hakaba kinji bazata sake taɓakuba " to shike nan Amma pls yaya Aryan ka haɗani da Ammi da Abba mana " mezakiche musu idan na haɗaku " zanfaɗamusu abun da Aunty Maryam tamana " aa to bazan haɗakuba gaskiya " ayya yaya Aryan kayi hakuri ka haɗamu tunfa shakaranjiya da Ammi ta kiramu ta wayar Aunty Zahra bamu sake maganaba, jiyama ina wanka naji su hiyana na magana da ita, kafin nafito kuma sungama magana pls ka haɗani da ita takarisa maganar kamar zatayi kuka " to zan haɗaku amma saikin min alƙawarin bazaki faɗamusu komaiba gaisawa kawai zakuyi " da sauri tace eh namaka alƙawari wlh bazan faɗaba " ok to yanzu bawasu Zahra wayar bari naji yanasu jikin idan mungama magana sai na haɗaki dasu " to kawai tace san man tamiƙawa zahra wayar " karɓa Zahra tayi suka gaisa san nan tamiƙawa hiyana " ansa hiyana ma tayi suka gaisa ya tambayeta jikinsu tace da sauki san nan yace to tabawa diyana wayar, miƙamata wayar hiyana tayi " da sauri diyana ta ansa tana faɗin hello " idan ruwan da a'kasamiki yaƙare Shahram zai maidaku gd, dan na chanza shawara zan ƙira mijin Aunty farida na faɗamasa ya bar Aunty farida tazo goɓe kinji " to shike nan yaya Aryan amma kuma, kuyi sauri ku dawo dawuri tayi maganar a shagwaɓe " meyasa kikesan mu dawo dawuri kodai kina san ganina' ne " eh ba kai kaɗaiba dukkan kuma inasan ganinku, gd babu daɗi dabaku nan " shiru yaɗanyi kafin yace ok inshaa Allah munkusa dawowa ae " to Allah ya dawo daku lfy tana gama faɗin hakan bata jira amsar shiba tamiƙawa Shahram wayarsa " koda Shahram ya ansa wayar yasa a kunnensa, sai yajiyo Aryan na faɗin nima inakewarki my sister ina kewar coffee ɗinki mai daɗin nan" a sukwane Shahram ya miƙa mata wayar kallansa diyana ta tsaya take damamaki batare da ta ansa wayar'ba " mikewa Shahram yayi yazo har kusa da ita yasa mata wayar a kunne " muryan Aryan taji yana faɗin sister ba kyajinane " hannu tasa ta ansa wayar tana faɗin inajinka yaya Aryan "to ae naji inata magane kinyi shiru " eh dazun banji me kafaɗa'bane " ok to shike nan Shahram zai jira idan ruwan da a'ka ƙaramiki ya ƙare zai mai daku gida, nurse ɗaya zata biku tachigaba da kula daku " to yaya Aryan makaranta'fa " makaranta sai kunji sauri ba naji kun gama exam bama " laaa waya faɗamaka to " zuchiyata mana itace tafaɗamin " to zuchiyar'ka tafaɗi gaskiya mungama " to bazaku sake zuwaba sai ranar da za'ayi hutu yanzu kam ku huta kuyi jinyar jikinku " to ka haɗani dasu Ammi mana " sai da daddare idan kun koma zankira layin Zahra na haɗaku amma karki karya alƙawari'fa " to bazan karyaba " ok sai munyi waya anjima koh, yana gama faɗin hakan ya katse kiran " jin ya katse kiran yasa ta mikawa Shahram wayarsa,
Chapter 41 · 0% Book details