← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 90

Sashe 20

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai martaba ya dubi diyana chikin harchen fullanchi wanda bai taba magana dashiba yache to yasu nanta ai basu aunty amarya kawaiba harda jarumai 5 saida suka dago suna kallon mai martaba hankalinsa kwanche yake fullanchinsa
Ammi kam ko ajikinta dan tasan ita ta koyamasa fullanchi
Chikin harche fullachin diyana tache su nanta amrat
Mai martaba yafa ra bayani nan yafadawa yan gidan matsayinsu Hiyana yakara dachewa daga yau sunzama yayansa kuma a nan zasu zauna bayan yagama maganarne yache koh akoi mai magana
Aunty farida tadanyi gyaran murya alamar tanada magana " mai martaba yache to ina jinki
Aunty farida tache dan allah Abba inasan abani wan nan natafi da ita ta zauna awajena tayi maganar tana nuna Diyana
Mai martaba yache aa bazaki rabasuba ki kyakemin yayana anan babu inda zasuje

Nantake aunty mardiyama ta hadiye maganarta jin amsar da mai martaba yabawa Aunty farida daman itama tanasan taroka abata lamrat amma jin Aunty farida da kanta an hanata yasa tai shiru

Aunty amarya kuwa tunani tashigayi ta yadda zata bullowa al amarin dan wlh bazata taba yarda su Diyana su zauna a gidan nanba dan kuwa yaddasuke kyawawan nan karsu Safras sufara sansu domin Safras zulaihat kawai zai aura

Mai martaba yache to kutashi kutafi Khalid kai kuma ranar monday kaje kamusu registration a makarantar su Zahra
Khalid yache to da É—ai É—ai mazan suka fara fita daga palan

Ummi ne tachewa Ammi yamukaji da hakuri
Ammi tache hakuri yazama dole " Ummi tache allah yajikansa Ameen Ammi tache san nan su Aunty farida ma kowa yafarayiwa Ammi taziya

Amrat na zaune kusa da mai martaba suna ta hira dashi da harchen fullanchi
Aunty amarya kuwa afusache tamike tafita daga palan kai tsaye part nata tanufa
Tana shiga ta kira hajiya sadiya tache ke aiki yakarufa domin kuwa mai martaba yana neman rusa mana shiri
Hajiya sadiya tache mekuma yafa " Aunty amarya tache Aisha che taje kauyensu ta daukoh wasu yara wai yayan kaninta daya rasu to wlh idan kikaga yaran nan kamar susukayi kansu dan kyau gasu da diri da komai kuma biyu daga chikinsu yan matane,yanzu fargabana É—aya a nan shine kar matasan gidan nan sufara sansufa
hajjiya Sadiya tache wayache maki zasu fara sonsu
Aunty amarya tache ke wlh koke kikaga yaran nan sai kinsosu saboda kyau ni tsoran danake jima karfa Safras da Aryan su fara son su idan hakan yafaru wlh angama dani
Hajiya sadiya tache angama dakene kokuma angama dani nida har na fadawa zulaihat Safras zata aura yarinya sai murnatake ai yazama dole mutashi tsaye
Aunty amarya tache to yanzu me abunyi
Hajiya sadiya . tache aiki gagarabadau zai mana ya koresu daga gidan kokuma ya haukata mana su kowa yahuta
Aunty amarya tache wlh hakan kawai za'ayi zankaramiki 500k achikin account naki yanzu ayi aiki mai karfifa wanda idan suntafi suntafi ke nan sufita daga rayuwar kowa sukoma rayuwa a bula
Hajiya sadiya tayi dariya tache karki damu aikinsan aikin gagarabadau badaga nan ba kedai kawai kizuba ido watan nan nakarewa muka shiga wata zanje enugu
Aunty amarya tache ai shiyasa nake sanki kawata sai munyi waya kekam anjima da daddare zan kiraki bata jira amsar Hajj sadiya ba ta katse kiran ta ajiye wayar a kan gado tanufi toilet

Pls more comments an like

*💫STAR LADY💫*

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 8*

Tana dago kai suka haÉ—a ido da yusuf," chikin kuka take faÉ—in dan allah hamma kayi haku...bata karisaba yadora hannunsa a kan lips nata yana faÉ—in to ya isahaka kiyi shiru bamai sake bugunki"
"Zahra'kam Mutuwar zaune tayi tashiga duniyar tunani, wai shin daman yaya yusuf haka voice nashi yake, allah yasa dai bawani aljani bane yazo musu a siffar yaya yusuf
Zahra, tayi nisa a chikin tunaninta kawai " "saitaga yusuf yamike tsaye yana rike da hannun hiyana saida sukamike," yache
Yakamata kirinka banban'chemu ni sunana yaya yusuf, wanda yamareki jiya su nansa yaya prince kinji, " cikin shesshekar kuka take faÉ—in to amma zan iyache muku hamma ," Yusuf yache meyasa kikesan kirinka chemana hakan "
"ai kunada yawane idannache dukkanku yaya zanrinka chewa bazan ganeba, amma idan ina hadawa da hamma abun zanmin sauki "
"Murmushi yayi san nan yache to shike nan nikirin'kachemin hamman kinji " to Kawai hiyana tache," dawo da kallansa yayi kansu diyana, kutaso muje mana, ba musu suka saukoh daga kan gadan "
"Zahra ma saukowa tayi suka jera yusuf narike da hannun hiyana saida suka fito palon Ammi, batare da yasaki hannun hiyanaba, yasa É—ayan hannunsa ya kamo hannun lamrat yache ke yasu nanki "
"Dawani gurbatatchen hausarta tache lamrat," jinjina kai yusuf yayi yana faÉ—in gaskiya lamrat yamin nisa awajen kira gashi su nan naku nada wahalar kira sosai dole na chanza muku suna ni bazan iya kiran sunan nan nakuba"
"Shiru sukayi kawai suna jinsa, yanuna hiyana ke daga yau su nanki sweet sis, yanuna diyana kekuma little sis, yanuna lamrat kekuma baby yanuna amrat yache my little baby ,"
"Zahra dai binsu kawai take dan ita duk tunaninta aljanine yazo a saffar yaya yusuf dan tun da take wlh bazatache, ga kalan voice na yaya yusuf ba, amma yau shine har da magana mai tsawo, kai to kodai umarnin mai martaba yabashine dan nasan mai martaba bazai tabarinsu hiyana a kunchiba

Dasallama sukashiga palan mai martaba," kowa yadago ya zubamusu ido amma banda don da tager Aryan"
"Umar'ne ya taba haidar kasa kasa yake faÉ—in kai anya kuwa yaya yusuf ne, kadubafa har da rikemusu hannu," haidar yaÉ—an kallai gefe da gefe yaga bamai kallansa kasa kasa shima yake magana kaidai kabari muje É—aki mayi maganar, kar'ajimu amana hukunchi"
"Yusuf kuwa yana shigowa palan ya ɗaure fuska kamar baitaɓa dariyaba sakin hannunsu yayi yakoma wajen zamansa ya zauna"
"Mai martaba ne yadubi su diyana dake tsaitsaiye, kuzokuzauna yache dasu chikin harshen fullachi"
"Diyana da lamrat da amrat sukazo suka zauna sukabar hiyana tsaye tana rakuɓe rakuɓe, dan ita harga allah kallan fuskar don tsoro yake bata, yanzu babban damuwarta ma kujera ɗayane yarage a table din kuma kusa dashi kujerar take, dankuwa kowa bayansan zama kusa dashi shiyasa mafi yawanchin lokuta kujerar kusa dashi zaka sameta babu kowa, yanzuma ita kawai tarage tunani hiyana tashigayi sosai tache to wai ina sauran kujerun ai kujerunma sunfi haka yawa, saboda jiya ai aunty farida da aunty mardiya suna nan kuma duk a nan mukachi abinchi dasu to yaukuma basu nan kuma table din yachika to ina sauran kujerun ke nan , tayi nisa chikin tunanani saitaji muryan mai martaba yanachewa
Kai Safras jekatawomin da ita dan tsoranka yahanata zuwa, " da sauri don yaÉ—ago kai yana kallan mai martaba " dauke fuska mai martaba yayi yache abun dagaji shinafaÉ—a dan idan bakaikamata maganaba bazata daina tsorankaba"
"Nantake fuskar don ta sauya idansan nan suka chanza launi zuwa jaa sosai jijiyoyin kansa duk suka mike sai wani huchi yake kamar zaki," kannensa naganin haka suka kama hansu, dagudu suka bar palan yarage daga Ammi Ummi Mai martaba Aryan Yusuf Fahad " Khalid ma guduwa yayi dan yasan halin mutuminnasa Ida ransa yabachi" aunty amarya'ma ba abarta abayaba ta'tsere " itama hiyana tana ganin sungudu tajuya itama tabisu"
"Mikewa don yayi sai wani huchi yake yanufi hanyar fita," da sauri Aryan ya taresa yana faɗin don bakada hankaline mai martaba nefa yake maka magana " hannu don yasa ya ture aryan gefe guda yanufi hanyar fita haryazo tsakiyar palan " aryan yasake taresa yana faɗin don kadawo chikin hayyachinka kasan mekake kokarin aikatawa kuwa" dunkule hannu don yayi yakaiwa Aryan bugu a Kirji " Aryan bai bari bugun ta sauka ajikinsaba yasa hannu ya tare hannun don," afusache don ya damki wuyar Aryan da ɗayan hannunsa yayi sama dashi kana yayi wurgi dashi gefe gida " rai a ɓache Aryan yamike yayi kansa shima wani bugu yakaiwa don a bayan wuya " da sauri don yajuya yasake tamkar wuyan Aryan ya shakesa sosai " Aryan kuwa dayaji azaba sai dunkule hannu, ya kai don bugu a bayan kunne saiga jini ta hanchinsa," afusache don yayi wurgi da Aryan kana yanufesa gadan gadan ya damki kafarsa yasake wurgi dashi gefe guda duk dahaka bai kyalesaba yasake yinkansa " "da gudun gaske Ammi tasha gabansa tana faɗin nizaka fara kashewa ba dan uwankaba "
Mai martaba kam harde hannu yayi yana kallan Iko god " yusuf ma bai damuba dan yasan indai irin wan nan faɗane sunsaba idan taɓachimusu "
Don saiwani huchi yake yache Ammi kibani hanya pls zuchiyata zafi takemin idan ban bugi Aryan'ba mutuwa zanyi " rai abache Ammi ke magana kamutu kamutu nache Ammi bata karasa maganaba yayanke jiki yafaÉ—i kasa sumame " Yusuf yamike yana faÉ—in alhamdulillah alhamdulillah tunda yasuma ai shike nan "
"Ummi che tayi kansa ita da Fahad da sauri " Ammi kuwa juyawa tayi tabar palan tanufi bangarenta abinta " mai martaba yamike da sauri yayi kansa yana faÉ—in, yusuf kukira sojojinsa a kaisa asibiti " aa Abba basai ankaishi asibitiba idan yasamu barchi zai watsake karka damu kaje kawai kayi shirin zuwa fada dan anajiranka,kaga lokachi yatafi chewar yusuf "
juyawa mai martaba yayi yanufi É—akinsa jiki ba kwari, yana ta tafiya ya tunanin ,anya ba aure zanwa yaran nanba ko nasami zuchiyar nan tasu ta ragu kai inganin hakan za'ayi nan da bayan sallah dole zanche kowan'nensu yafito da mata da wan nan tunanin yashige É—akinsa

Ummi to yanzu yazamuyi mukaisa daki daman Aryan É—inne kawai mai É—aukansa idan abunnasa ta motsa, to yau kuma yayiwa Aryan rauni yusuf baigama rufe bakiba " "sukaga Aryan ya tattare dukkan karfinsa ya dauki don a kafaÉ—arsa yayi waje dashi "
"Ummi tache allah sarki allah yakara haÉ—amana kanku allah yakaramuku kaunarjuna " ,jinjina kai yusuf yayi kafin yafuta ameen Ummi ai kulluma idan sukayi faÉ—a don ke bugun Aryan amma kuma Aryan ke taimakon don akoyaushe " murmushi Ummi tayi san nan tamike tanufi nata bangaren " yusuf yadawo da kallansa kan fahad dake tsaye to muje koh " Fahad yajuya kawai yayi batare dayayi maganaba yanufi hanyar fita
Chapter 20 · 0% Book details