← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 90

Sashe 65

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wow my daughter kinyi kyau sosai chewar Abba yayi maganar yana kallan diyana, dan ita kaÉ—ai che a chikin su tayi kwalliya, "laaaa Abba kasan me ranan ma yaya yusuf yace nayi kyau haka yaya Aryan ma da na kai masa coffee yace nayi kyau dana É—an kwali, asukwane matasan gidan suka juyo da kallan su kan Aryan,

ɗaure fuska sosai Aryan yayi kamar bai taɓa dariya ba ya chigaba da latsa wayar sa, ita kuwa diyaba ko ajikin ta sai murmushi take tana bawa Abba lbr, ganin Aryan ya ɓata rai sosai ne yasa Yusuf yace "eh mana my sister ai dole kowa yace kina da kyau, to ke ba sis ɗin mu bace idan bamu yabe ki ba, waza mu yaba, wani murmushi diyana ta saki tana faɗin "Allah yaya Yusuf idan nayi kwalli ina kyau? "kai sosai ma kuwa may sis ai duk gidan nan kin fi kowa kyau kuma kin fi kowa... Bai karisa maganar ba saka makon wani mugun kallon da Aryan ya wurga masa, irin kallon nan na ina ruwan ka da ita idan ma tafi kowa kyau, shiru Yusuf yayi a chikin zuchiya yana tunani kai yaya Aryan akoi bala'e kishi to kai kaki bayyana soyayyarka san nan kuma idan wani na ya bonta ko ya raɓe ta ka hukun tashi, yanzu da kake harara'ta ni ina ruwana ai ban che ina son taba kawai yabon ta nake ni da nake da mai baby . Juyawa Aunty farida tayi ta koma wajen zaman ta ta zauna, shiru palon yayi sai karar spoon kawai zaka ji

"Yauwa yaya Aryan wan nan jakar da ka bani nan taki buɗuwa, kullun nache zan kawo ka buɗe min sai na rinƙa mantawa, chewar diyana tayi maganar tana kallon Aryan, tab aiko gaba ɗaya palon sun zuba musu ido suna jiran amsar da zai bata, ɗago ash eyes nashi yayi ya sauke su kan face nata sai murnushi take nan take kuma sai yaji wani sanyi na ratsa zu chiyar sa, calmly ya fara magana "eh nina kulle jakar zan buɗe miki amma ba yanzu ba, tirkashi Aunty amarya ji take kamar ta tashi ta shake diyana dan bakin chiki Amma tana tsoron Abba

Ayya yaya Aryan ka buÉ—emin kaji, kaga su Aunty Zahra duk sun sa nasu tsara bar kuma wlh kayan nasu yamin kyau nima ina son saka nawa ta karisa maganar kamar zata yi kuka, zuba mata ash eyes nashi yayi sosai, ya kasa kawar da kallon sa daga gare ta, Abba dai ajiye spoon nashi yayi ya zubawa Romeo and Juliet ido kawai yana kallan su, Khalid Yusuf Aunty farida sai murnushi suke suna murna, Aunty amarya Aunty Maryam kuwa kamar zasu mutu dan bakin chiki, Ammi da Ummi kam ko ajikin su abin chin su kawai suke chi basu ma lura da Abun da ke faruwa ba, Fahad ma abinchin sa yake chi ko ajikin sa bai ma san suna yi ba haidar Umar sai satar kallan yaya Aryan suke suna mamaki, tsoro suke kar ya kama su suna kallon sa, Aunty salma Aunty mardiya wayoyin su suke latsawa han kalin su baya kan jamar palon

Da kyar ya iya saita voice nashi kasa kasa kamar mai raɗa yace "an jima ki kawo min jakar na buɗe miki yana gama faɗin hakan ya miƙe da sauri ya bar palon, dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan Abba, ta kashe masa ido ɗaya wani cool murmushi Abba ya sake mata a hankali ya motsa lips nashi, yayi ta alama da mun fara nasara, gyaɗa masa kai kawai Aunty farida tayi san nan ta chigaba da chin abin chinta.

Misalin karfe 3 :30 na rana gaba ɗaya ƴanmatan Ammi suna zaune a karamin palon sama na ɓangaren Ammi hiyana na riƙe da Alkur'ani mai girma tana karatu, diyana na buga game a wayar Zahra lamrat da amrat suna kallo Film a makeken Tv dake makale a bango, Zahra riƙe da littafin husnul Muslim tana karatu addu'oe, hankalin su yayi nisa a kan abubuwar da suke,

.... da sallama Yusuf ya shigo palon da sauri suka ɗago suna kallon sa, da gudu lamrat ta miƙe ta nufe'sa hannu ya buɗe mata ta faɗa kan faffaɗar kirjinsa ya mai da hannun sa ya rufe yana faɗin "my baby nayi kewar ki, cikin shogoɓa tace "nima nayi kewar ka yaya Yusuf, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana faɗin "my baby ina san gashin nan naki kyau yake min, lamrat zata yi magana yayi sauri raba jikinta da nashi kasan chewar yaji alamun tafiya ta bayanzu kamar mutun zai shigo palon, riko hannun ta yayi suka karisa chikin palon suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3,

da sallama Khalid ya shigo palon shima da gudu Zahra ta miƙe tanufe sa, har zata rungume sa sai kuma ta dakata, kallanta yake itama tana kallon sa "sannu da zuwa yaya Khalid ta faɗa tana sun kuyar da kai "Auta yau kam babu oyoyo ne ya tambaya yana ɗago haɓatar da hannun'sa, chikin shagwaɓa tace "Ammi che tace wai kai zan Aura kuma na daina yi maka oyoyo sai bayan Aure, wani nauyayyar ajiyar zuchiya Khalid ya sauke tare da faɗin "da gaske Auta Ammi ta faɗa miki ni zaki Aura, gyaɗa masa kai Zahra tayi alamar eh, gyara tsayuwar sa yayi kafin yace "to kina sona, juyawa Zahra tayi zata gudu yayi sauri riko hannunta sai lokachin idon'sa ya sauka kan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido, diyana kam bata ma san sunayi ba game nata kawai take bugawa hiyana ma kanta na kan qur'ani karatun ta kawai take

Harara Khalid ya wugawa Yusuf zai yi magana ke nan haidar ya shigo da gudu yana faɗin Ammi, Ammi ina kike yaya Ahmad ya mut....✍️

💖The Talent Troupe Writer's 💖

1 Duk Karfin Izzata
2 Gidan Aunty
3 Jini ÆŠaya
4 Sarki Sameer
5 Kafita Zakka

Kar kubari abaku lbr love Story's
*💫STAR LADY💫*27

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*
Star lady

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 2️⃣7️⃣*

......Ammi, Ammi ina kike yaya Ahmad ya mutu, a sukwane Yusuf ya miƙe yana faɗin "kai haidar ka dawo cikin hankalin ka, wani Ahmad ɗin? "wlh yaya Yusuf ina chikin hankalina yanzun nan muna zaune dashi a fada kawai ya fara tari, jini na fito kafin kache me ya faɗi, ai tun haidar bai kai karshen maganar ba Khalid ya saki hannu Zahra ya juya har suna karo da Yusuf wajen fita da gudu, Haidar kuwa ya nufi betroom ɗin Ammi, mikewa diyana hiyana zahra lamrat amrat sukayi suka bi bayan su Yusuf, tare Ammi da haidar suka fito suma suka nufi fada

Koda su Ammi suka isa fada gaba É—aya family sun haÉ—u awajen suna tsaye chirko chirko da kaga fiskokin su kaga alamun tashin hankali musamman Khalid da Aiman na su tashin hankali banne,

BGS daune a tsakiyar fada ya É—ora kan yaya Ahmad kan chinyar sa yana zura hannun sa chikin rigan Ahmad, Abba Aryan Fahad Umar suna tsaye a kansu, Aiman da Khalid kam sun ma kasa kariso wa wajen saboda tashin hankali daga baya suka tsaya

, shiru gaba É—aya su kayi suna sun zubawa BGS ido suna sauraron suji me zai che

.. Almost 5mnt san nan BGS ya ɗago green eyes nashi da suka sauya launi izuwa jaa sosai chikin wata iriyar voice mai kama da mara lfy ya furta "bai mutu ba suma yayi,ku bani ruwa mai sanyi sosai gaba ɗaya fada ta ɗauƙa da alhamdulliah san nan Khalid ya juya da sauri ya nufi katuwar freij dake cikin fadan ya ɗauko ruwa mai sanyi ya dawo ya miƙawa BGS, tsabar tashin hankali har ya manta ma ana buɗe robar ruwa..

...Ansan ruwan Aryan yayi da sauri ya buÉ—e bakin roban san nan ya mikawa BGS, hannu BGS ya mika wa Aryan alamun ya zuba masa ruwan, zaba masa kaÉ—an Aryan yayi a hannun nashi, a hankali BGS ya shafawa Ahmad ruwa a fuska

wani atishawa mai karfi gaske Ahmad yayi, ya fara tari da karfi karfi kamar makogoran sa zai fashe yana kokarin miƙewa, da sauri BGS ya rikosa yana faɗin "kubani ruwan, a hanzar che Aryan ya miƙa masa roban gaba ɗaya, ansa yayi ya ka fawa Ahmad a baki amma ina Ahmad yaki sha sai kokarin mikewa yake, gaba ɗaya ya sauya lokachi guda ya rame ya fita hayyachi sa,

Da karfi Ahmad ya fisge jikin sa daga na BGS zai mikewa, a'sukwane BGS ya tamke sa ya mai dashi ya zaunar gaba É—aya fada hankalin su ya tashi ganin halin da Ahmad ke chiki

faÉ—a ne ya kaure tsakani BGS da Ahmad dan Ahmad ya dage sai ya tashi, shi kuma BGS ya hana shi,da BGS ya ga dai Ahmad ba zai sarrafu ta lalama ba sai ya mike, yasa karfi ya danne Ahmad a kasa ya haÉ—a hannayen sa dukka biyi ya taka da kafa É—aya ya damki gashin kan sa ya É—ago da fiskar'sa ya kafa masa robar ruwan mai sanyi a baki, dan ruwan zata tai maka masa sabo da tarin da yake,

ba shiri Ahmad ya fara haÉ—iye ruwan, dan dole, kawar da kai Ammi da Ummi su kayi daga kallon Ahmad suna kwalla, da gudu Aunty mardiya ta juya ta bar fada tana kuka, bazata iya kallon halin da Ahmad ke chiki ba, kuka Aunty salma keyi sosai rungumeta Aunty farida tayi tana É—an bubbuga bayan ta alamar rarrashi,ita ma dai Aunty farida hawaye take, shi kansa Khalid daure wa yake amma ji yake kamar zai yi kuka, sosai hiyana ke kuka kamar ranta zai fita daman ita sarkin tausayine, haidar Umar duk kwalla suke, Fahad ma idon sa ya chika tab da kwalla amma basu zubo ba, Abba kuwa idon sa ta sauya tayi jaa sosai, ga tashin hankali nan karara a bayyane a kan fuskar sa, Aiman kam ba'a magana dan yafi kowa shiga damuwa saboda tare suke komai da Ahmad ko Aryan da suke yan biyu bai shaku dashi kamar yadda ya shaku da Ahmad ba
Chapter 65 · 0% Book details