← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 90

Sashe 88

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru palon yayi kowa da abun da yake tunawa, hannu Zahra tasa ta ɗauki Cup ɗin ruwan dake kusa da Abba tana kokarin kawowa gaban ta kamar wadda aka bugewa hannu patal cup ɗin ya faɗi chikin plate ɗin abin chin zulaihat ruwan ya zube a chiki, chikin jin haushe da bachin rai abun da Bgs ya mata na rashin amsa hii ɗin ta da yayi ta miƙe ta zabgawa Zahra wani gigitachen mari, wani kara Zahra ta saki

Bata gama sauke hannu ba Haidar da Umar suka miƙe a tare suka wanke mata fuska da wasu gigitachen maruka a lokachi guda ta gefen dukka kuma tun ta tana kokarin sakin kara, Fahad ma ya miƙe ya mata ɗaya tamkar da dubu ta gefen kunne, wadda yasa gaba ɗaya taji duniya ya tsaya Chak kunnen ta ya dai ma ji na wunchin gadi, almost 5mnt tana tsaye tama kasa sakin ihun dan da alama bata chikin hayyachi sai da ta kara wani 5mnt san nan ta samu damar sakin wani razanannen ihu mai firgitarwa, Afusache chikin tsawa Aryan yace "get out a ruɗe ta kama hanya fita sai ihu take kamar wata mahaukaciya

Kuka Zahra take a hankali sai shessheƙa take ga shatin yatsun zulaihat kwanche akan kuma tun ta wajen yayi ja wur dashi gyaran murya Aryan yayi wadda yasa gaba ɗayan su ban da Bgs suka ɗago suna kallon sa,da hannu ya yiwa Zahra alama da tazo
Miƙewa tayi daga kujerar ta ta nufi waje sa, batare da yayi Magana ba ya mata nuni da hannun akan ta zauna kan chinyar sa, zama tayi yasa hannu ya goge mata hawayen kasa kasa yace "ya isa haka kuka kinji Auta? Gyaɗa masa kai kawai tayi alamar eh, spoon ya ɗauka ya fara ɗeban abinchi daga chikin plate na Khalid yana bata a baki.

Aunty amarya ji take kamar ta tashi ta shake Zahra dan haushi kwafa tayi a chikin ranta tana tunanin wani hukunchin ya kamata ta É—auka akan yaran nan

Khalid kam yama kasa magana saboda bakin chikin marin sis love É—in sa da akayi ajiye spoon na shi yayi yana kallon yadda Zahra ke chin abinchin da Aryan ke bata

Tunani Umar da Haidar suka shigayi daman yan uwan su suna son su haka dubi yadda yaya Aryan ke bawa Zahra abin chi a baki Alhadulillah Alhamdulliah

Duk wan nan abun da ake Bgs ko É—ago ido bai yiba bare kasa ran zai yi magana.

Haka zalika Fahad tun da ya mari zulaihat ya koma ya zauna ya chigaba da chin abin chinsa kawai

mikewa Ammi tayi ta fara magana "me yasa zaku mata irin wan nan maruka hakan eh!? "Ammi to me Auta ta mata da zata mare ta haka chewar Umar, shi dai Fahad kawar da kai gefe yayi dan bai ma son haÉ—a ido da Ammi dan bai da niyar bata amsa sai wani furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, dawo da kallon ta Ammi tayi kan Bgs dake zaune yana kallon wayar sa "kai yanzu kana ganin yaran nan suka mari yar mutane bazaka hana suba Koh? Shiru ya É—an yi na yan second ni kafin ya buÉ—e É—an karamin bakin yace "ai dai dai sukayi Ammi shiyasa"
"Dai dai sukayi ma zaka che ko? "Haba Aisha ya isa haka gaskiya ya faÉ—a miki ai dai dai sukayi mana da basu hukun tata bama to ni da kai na zan hukun tata Autan tawa guda za'a mara kuma a gaba na san nan batare da tayi laifin ko mai ba ai kam wane mutun, chewar Abba komawa Ammi tayi ta zauna tayi shiru tana tunani "nima har chikin raina naji wan nan mari da yarinyar nan tawa Zahra amma dai bai kamata su haÉ—u mata haka ba

Abba ne ya katse mata tunanin da take yace "to na tara ku a nan ne inason yin magana daku...✍️✍️

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)

*Baby*
By (Mhiz innocent)
*💫STAR LADY💫*34

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3️⃣8️⃣*

.......Jibi jumma'a ina son gaba ɗayan ku kusa kayan hausawa domin akoi taron da zaku rakani, a sukwane Bgs ya ɗago green eyes nashi yana kallon Abba "Abba nifa ban iya saka kayan hausawa ba" Chewar Fahad yayi maganar yana kwaɓe fuska "same here gaskiya Abba ka chanza dan ni ba zan iya sakawa ba, chewar Bgs, dogon numfashi yaya Aryan yaja kafin yace "Abba nima dai ba zan iya saka kayan hausawa nan ba gaskiya" chikin fushi Ammi tace "to sai kuma ku kayi rashin Sa'a iyayen ku hausa fulani ne" "Aisha kiyi shiru ki kyale ni dasu chewar Abba, yaya Khalid kam shiru yayi yana binsu da ido dan yama rasa me zai che ko shi ba iya saka kayan hausawa zai yiba amma tun da Abba ne yace abun da yake so ke nan tofa ya zama dole ayi hakan

"Abba pls ka bari musaka kayan da muka saba tun da iya raka ka kawai zamuyi chewar Fahad dawo da kallon Abba yayi kan su Ammi chikin nitsuwa da girmama juna yace "Aisha kuje ku kyale mu zamuyi magana.

Abba yache su Ammi su tafine ba dan komai ba sai dan yasan halin Ammi yanzu zata ɗau zafi tafara yiwa su Bgs faɗa kuma shi Abba baya son hakan lallaɓasu yake son yi yana son su saka kayan hausawa dan idan yace zai bisu ta karfi tofa abun ba zai musu daɗi ba zasu iya shirya masa wani kitimurmuran da zai hana su zuwa wajen taron dan haka gara ya bisu a hankali su rabu lfy

Gaba ɗaya matan suka miƙe suka fice daga palon Aunty amarya sai chika take tana batsewa dan haushi dawo da kallon Abba yayi kan su Bgs ya fara magana

"Wai me yasa duk abun da nake so baku son shine? Me yasa baku san sakani farin chiki ne? Yanzu fa chewa nayi kusaka kayan hausawa iya na rana É—aya amma shine kuke tamin wani kame kame, idan ba kumin abun da nake soba waye zai min? Eh" shiru su kayi ba wanda ya tanka Abba chigaba da magana Abba yayi "wai ni wani laifi na muku ne? Da kuke min hakan, chikin jin tausayin Abba Khalid yace "Abba kayi hakuri zamu saka ina dai kayan hausawa kawai kake son ka gammu da shi? To zamu saka koda na shekara kace musa zamu sa bare kuma na kwana É—aya" murmushi kaÉ—an Abba yayi kafin yace "to Allah ya muku albarka" Khalid da Yusuf ne kawai suka amsa da amin

Miƙewa Abba yayi ya nufi hanyar betroom nashi yana faɗin "Khalid kai da Yusuf an jima kusa me ni a fada san nan akoi wani Babban likita da zai zo daga madina dan duba jikin Ahmad idan ya iso sai kuje Airport ku ɗauke sa ya kai karshen maganar tare da shigewa chikin betroom ɗin sa

Miƙewa Bgs yayi yana hararan Khalid rai a bachin ya nufi waje chikin zuchiyar sa yana faɗin "kayan hausawa kuma Ni never Abba ni ba zan iya ba kai taron ma kwata kwata ba zan jeba gaskiya, da wan nan tunanin ya nufi part nashi

"Aiman ya ka baro Aunty farida? Chewar Aryan yayi maganar yana miƙewa "suna lfy suna gai sheka wuche wa Aryan yayi ya nufi hanyar fita batare da ya sake chewa Aiman komai ba, Aryan na fita kiran diyana ya shigo wayar Aiman miƙewa yayi tare da picking call ɗin ya nufi waje yana faɗin "Hello daga ɗayan bangaren diyana tace "yaya Aiman dan Allah ka haɗani da yaya Aryan ɗin mana" "baby diyana yau ko sallama babu ke dai kawai a haɗaki da yaya Aryan to ma wai me zaki faɗawa yaya Aryan ɗin nan ne? "Babu komai yaya Aiman kawai zan gai da shi ne dan tun da nazo yanzu 3 weeks ke nan bamuyi Magana ba"
"Ok karki damu yanzu zan haɗaku ɗan riƙe wayar yana magana yana tafiya part ɗin Aryan ya nufa suna hirar su, dai dai zai shiga part ɗin kiran Aunty amarya ya shigo wayar sa "baby diyana bari na ɗauki call ɗin Aunty Amarya kinji? Amma ba sai kin katse kiran ba, batare da ya jira amsar taba ya ɗaga kiran Aunty amarya ya sa diyana a hold

Chikin sauri Aunty amarya tace "Aiman kazo yanzun nan ina jiran ka" "to daman ina son inzo nima dan akoi magana mai muhimmanci da nake son yi dake" "to kayi sauri"

chikin sauri ya juya ya nufi part na Aunty amarya,tare da katse kiran Aunty amarya "my diyana ki bari zamuyi waya an jima yanzu Aunty amarya na kirana, ba tare da ya jira amsar diyana É—in ba ya katse kiran dai dai lokacin ya shiga part É—in Aunty amarya

Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga palon babu kowa kai tsaye betroom ɗin ta ya nufa zaune take a bakin gadon sai wani ɓata rai take tana kwaɓe fuska saman manya manyan throw pillow dake tsakiyar ɗakin ya zauna tare da faɗin "barka da hutawa Aunty amarya" "batare da ta amsa ma saba tace "ina Aryan ɗin kuma!? "Yana part nashi, bai karisa rufe baki ba Aryan ya shigo bakin sa ɗauke da Sallama
Chapter 88 · 0% Book details