← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 90

Sashe 30

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GabaÉ—aya family sun haÉ—u a palo dan chin abinchin dare amma banda don, dakuma yan matan Ammi subasu zoba , " mai marbata yace waishin ina yan'matana'ne mesukeyi basu fitoba, ko dai daga buÉ—a baki shike nan bazasuchi abinchin dareba" Ammi zatayi magana sai sukajiyo sallamar'su nanfa kallo yadawo kansu banda Aryan da fahad kowa na palon kallansu yake, "

diyana na sanye chikin dogon wando baki da rigansa zuwa guiwa pink colour still dai ba É—an kwali a kanta ta zuba gashin nan har baya sai kwalli gashin yake nakinkirin dashi har tsakiyar bayanta, dan karamin bakin nan nata yasha janbaki pink ga blue eyes yasha kwalli ta gyara sagenta ga zarazaran gashim idanta, tasa high heel pink kalar rigarta

" hiyana ma dogon wando baki tasa sai riga sky blue zuwa guiwa ta ɗaure gashin Kanta, tayishi kamar donut ta yafa gyalen kayan akanta paki kalan wando dan bakin nan nata yasha ret janbaki tayi kyau sosai kamar kasacheta ga blue eyes yasha kwalli sai'yaƙara kyau sosai yana kyalli sajenta kwanche a gefen kumatun'ta gashin geranta kamar tayi caving tasa flat shoe sky blue kalar rigar

Zahra ma dogon wando baki tasa sai riga yellow tayafa gyalen kayan akanta shima bakine É—an karamin bakin tan nan tasanya masa janbaki pink colour tayi kyau sosai itama daman zahra kama take da don sosai wan nan dalilinsaya suka zama kamar tagwaye da hiyana sai dai banbanchin kwayar ido dan zahra idanta bakine kamar nawa

Lamrat kuwa dogon riga baki tasa mai shegen kyau,
Tasa flat shoe fari, tayi rolling É—in karamin farin gyale a kanta Zahra tamata make up sosai kamar wata balarabiya tazama

Amrat kuwa dogon wanto fari dasa sai yar farar t-shirt navy blue itama batasa É—an kwaliba amma zahra tamata pakin na gashin a tsakiyar kanta tazuba jelar gashin a' baya har tsakiyar bayanta booth navy blue tasa a kafarta

Yusuf ne yache wow my baby zo " gaba É—aya kallo yadawo kan Yusuf, a' sukane Aryan yaÉ—ago yana kallan Yusuf É—in shi ko ajikinsa kallan su diyana ma yake baisanma jama'a na kallansaba " bin inda Yusuf É—in ke kallo Aryan yayi " "Aryan kasa kawar da kannasa yayi daga kallanta ?

Karisawa wajen table É—in sukayi sukayi kowa tasamu waje ta zauna lamrat zata zauna kusa da Ammi " yusuf yache zo nan kizauna kusa dani my baby " bamusu lamrat takoma kusa dashi ta zauna " haidar da umar sai gulma suke kasa kasa " Ammi da Ummi kam ko ajikinsu abinchinsu kawai sukechi " Aunty amarya kuwa sai chika take tanata harararsu " É—aukoh fura ki damamin hiyana chewar mai marbata " da sauri hiyana tamike tanufi kichin, kwarya ta É—aukoh san nan ta daukoh fura, tanufi freig ta É—auki ruba É—aya na nono tajuya takoma palan mai martaba, da sallama tashigo palan ta dawo wajen zamanta ta zauna tafara dama furar

Sai'hira suke jefi jefi mai marbata yache banso a che muntafi umrah nan mun barkuba amma makaranta basu baku hutuba " Ammi ne tache sai suje hajji kawai kokuma subari sai wata shekarar " mai martaba zaiyi magana " Ummi tace Fahad tashi ka kaiwa yayanku abinchi " da sauri Fahad yamike yana faÉ—in ina abinchin " yana kichin Ummi tabashi amsa , " fichewa yayi daga palan

Bayan hiyana tagama dama furan tamikawa mai marbata " karɓa yayi yana murmushi kana yace duk gidan nan hiyanata tafi kowa iya dama fura " turo baki diyana tayi tana faɗin wlh nafita abun dama nina ko.... bata karisa maganaba sakamakon wani mugun kallan da Aryan yake wurga mata " shiru tayi

Mai martabane kuwa sai kallansu yake yana murmushi yana farinchikin burinsa yafara chika aishi haka yakeso kodama hararanne Aryan kewa diyana daÉ—i zaiji dan daga harara sai kallan mutunchi " Ammi che ta katse masa tunani dache ranka ya daÉ—e sai da safe " hararar wasa mai marbata ya wuga mata kana yace inada magana dake " to kawai Ammi tache " jin mai marbata yace. yana da magana da Ammi yasa kowa yatashi suka fiche

Mai martaba yadubi Ammi yafara magana jiya Yusuf yasame damaganar akan Khalid da zahra, Khalid yafaÉ—awa Yusuf yanasan Zahra tun tana karama ina faÉ—amiki hakanne bawai dan kifaÉ—a mataba sai hakkinki a matsayin uwa da'kuma kisamata ido karkibari tawa Khalid kishiya, danni tun da Yusuf yafaÉ—amin nariga nabawa Khalid auren ta, kokina da wani abun faÉ—e " ajiyar zuchiya Ammi tayi san nan tace, nikaina inakaunar Khalid nina renesa a hannuna yagirma babu halinsa da bansaniba bawani abun da zanche saidai inmusu fatan alkhairi kawai " to masha allah Amma fa kinsan yau a É—akin'ki nake amma kikechemin sai da safe koh " murmushi Ammi tayi tana tace tubanake wlh nagajine a'zumin yau É—in nan ya wahalar dani " haryanzu dai lallanchinki bai raguba Aisha, to muje chiki namiki tausar koh " mikewa Ammi tayi tana faÉ—in mujedai ninamaka " dariya mai martaba yayi san nan yamike yabi bayanta sukayi chikin betroom

Karfe 10 na dare

Rike take da cup ɗin coffee tanufi bangaren Aryan jikinta sanye da kayan barchi riga da dogon wando pink colour still dai kanta babu ɗan kwali tafiya take tana kunkuni" ni wlh barchi nakeji nagaji saikayitaba mutun wahala dan mugunta " da sallam tashigo palan baya palo kai tsaye ta wuche betroom ɗin " kwanche yake akan makekiyar gadansa yana latsawaya jin shigowarta yasa ya ɗago kai yana kallanta " sai turo baki take tana magana kasa kasa " from head to toe ya karemata kallo san nan ya ɗauke kansa da sauri " karisa shigowa chikin ɗakin tayi tazo gaban gadan ta duka san nan tace. Ina wuni yaya Aryan " shiru yayi bai amsaba kuma bai motsaba " itama shiru ta zauna har kusan 15 mnt, san nan tache yaya Aryan dan allah ka karɓi coffee ɗin mana wlh nagaji " banzah Aryan yayi da ita kamar baiji metake faɗe ba shiru shiru baiyi maganaba ganin bai daniyar magana yasata tamike, tanufi indayake wai dan taga yayi barchine
Aji cup É—in coffee É—in tayi akan dan karamin table É—in dake tsakiyar É—akin san nan tanufi kan gado hawa gadan tayi taga idansa a lunshe , ta turo baki tana faÉ—in shine dan mugunta kabarni ina duke kan guiwowina har kafata namin zafi kaikuma kayi barchinka koh, to banyafe... Bata karisa maganarba taga ya waro manya manya ash eyes É—in nan nashi akan fuskarta " a'sukwane ta juya tana kokarin sauka gadan wani damka yayiwa gashin kanta wandayasa tadawo baya tafaÉ—a kan kirjinsa " kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu yarufe mata baki " kasa kasa yace kina buÉ—emin baki ina harbinki da bindiga meya hauwar dake gadona yayi maganar tare da chire hannunsa daga bakinta " murya na rawa tace dan allah yaya aryan kayi hakuri kasakemin gashina wlh zafi yakemin " banche karna sake ganinki ba É—ankwali ba eh " kayi hakuri zanrinka sawa chewar diyana tayi maganar chikin muryar kuka " harchikin ransa yaji voice nata na karshe kayi hakuri zanrinka sawa a hankali yazame hannunsa daga kannata, yana faÉ—in to tashinmin ajiki " da sauri tamike tana faÉ—in to ga coffee É—in " mikewa yayi shima kana yace bazanshaba ki mayar kije kisa É—ankwali saiki kawomin " a shagwabe tace ayya dan allah kayi hakuri kasha allah gobe zan daura dan kwalin kafin nakawoma wlh yanzu nagaji kuma barchi nakeji " kallanta yayi from head to toe san nan yache nikam, kekam kinada hankali kuwa kinsan chiwon kanki kuwa " turo baki diyana tayi tana faÉ—in mekuma nasakeyi " wlh azim idan kikasake fitowa a haka batare da hijabi ko kayan arziki ajikinkiba allah zakiyabawa aya zakinta " binjikinta tayi da kallo achikin zuchiyarta tana tunanin to me laifin kayan nan tayi nisa chikin tunani taji ya daka mata tsawa " wai badake nake magana bane nache kifitamin a É—aki koh, da sauri tajuya tabar É—akin binta yayi da kallo har tafita
san nan yamike yanufi inda ta ajiye coffee É—in ya É—auko cup É—in yadawo gefen gadansa ya zauna yafara sha,

Bangaren diyana kuwa tana fita bangaren Aryan kai tsaye part nasu tanufa da sallama tashigo palan, da sauri taja burki tana faÉ—in ya yaya Yusuf kaima bakayi barchiba " murmushi yusuf yayi yana faÉ—in eh ina hira da baby's nawane suna koyamin fillanchi " karisawa indasuke diyana tayi tana faÉ—in kema amrat hardake yau bakiyi barchiba sai kije school kiyita barchi a class koh " lamrat tace ainikam ma yanzu zanje na kwanta " zama diyana tayi kusa da Yusuf zatayi magana " Yusuf yace kuje ku kwanta dare yayi kunsan akoi tashin asuba ga zuwa school yayi maganar yana mikewa yanufi hanyar fita " suma mikewa sukayi suka wuche É—aki

Karfe 4 dai dai na asuba gaba É—ayansu sun haÉ—u a palon mai martaba danyin sahur amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali " Ammi tache hiyana da Zahra kuchi abinchin nan dawuri ku'É—auki na yayanku ku kaimasa zahra najin Ammi tache sukaiwa don abinchi tafasa kara sai da kowa na palan yaÉ—ago yana kallanta " lfy auta ta chewar Abba " Zahra dai taki magana sai kukanta kawai take " hiyana kam datariga da tasan me Zahra takewa kuka ko kallanta batayiba, su Ammi sunyi tambayar duniyar nan amma Zahra taki magana sai kuka take " Aryan ne ya daka mata tsawa zakimana shirune kosaina babballaki a nan " tsit tayi kamar ruwa yachita "
Aunty amarya ne tamike tana faɗin kai umar kaje ka dauki abinchin yayan naku ka kaimasa kuma daga yau kai zaka rinƙa kai masa abinchi tana kaiwa nan tafiche tana tunanin aranta ai bazan taɓa barin yaran nan surinƙa kusantar samarin gidan nanba daga yau har ranar da gagarabadau zai musu aiki ido zan samusu sosai da sosai ɗakinta tawuche ta haye gado babu ko sallah takama barchi
Chapter 30 · 0% Book details