← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 90

Sashe 12

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

wajen su diyana yanufa,suna zaune suna yar hirar'su bello yazo kusa dasu kamar mai sayan nono kasa kasa yafara magana "duk wanda ba zai sayi nono a nan ba sai dai abari, karku kuskura ku sake kai ma wani sai dai ya hakura san nan kuma ki damamin fura da nono na 100, da sauri hiyana ta bude kwaryar nono ta É—auko roba biyu ta juyesu a chikin wani dan karamin kwarya tasa fura biyu ta dau ludayi tafa damawa, tagama ta juye masa a leda ta mika masa,hannu yasa ya ansa, yasa É—ayan hannun sa a aljihun ya chiro kuÉ—i naira 500 ya juya gabas da yamma dan yaga akoi mai kallan sane ko babu, dan bai san inna tasani, mikawa hiyana kuÉ—in yayi, Kin ansa tayi, tana girgiza masa kai alamar ya bar kuÉ—in kawai, kan pai pan dasuka rufe kwaryan nono ya ajiye musu kuÉ—in kasa kasa yache kichere 100 na nono kibawa inna, sauran 400 kisaya muku rogon 100 ki ajiye 300 kuma zai muku am fani gobe, bai jira amsar suba yajuya da sauri, dan ya lura hankalin mutane yafara dawowa kansu kar wata matsalar tazo tafaru

wuni zumbur su hiyana sukayi awajen ban da bello daya saya nonon bawan da yasake saya, shima mutumin da diyana ta kai wa nono bai basu kuɗin ba, haka sukayita zama da nono har karfe 6 na yamma, san nan hiyana ta miƙe tana faɗin kutashi mutafi gida, mikewa diyana da lamrat sukayi suka ɗauki kwaryar nono suka ɗora akansu suka kama hanyar gida
Suna tafiya ne diyana tache "wai lamrat waya saye furan ki na jiyane lamrat tace "ae dayake kinga jiya kasuwane akoi baki,ni kuma kinga ai idona ba irin naku bane ba wanda yake chemin mayya shiyasa bakin suka rinka sayan nonon
Hiyana ta girgiza kai tana faÉ—in "ae kema da idon ki yayi irin namu babu wan da zai saya koda bakin nema, suma chewa zasuyi ke mayya che
Diyana tache "yanzu ya zamuyi da inna, É—aure fuska hiyana tayi tana faÉ—in "ya zamuyi kuwa dukane dai kamar yadda muka saba shi zamusha "Allah kakawo mana mafita chewar diyana, dukkan su suka amsa da ameen

Da sallama suka shiga gidan sai faman rakuɓe rakuɓe suke, muryan inna che ta daki dodon kunnen su daga ɗaki, tana faɗin "ae shiyasa nakesan hiyana ta Auri buban kinga ita hanyar mutuwar ta mai sauki ne, sukuma sauran zamusan yadda zamuyi dasu
amma bazamuyi kisa a chikin gidan nan ba dan kinsan al adar kauyen nan, amma na chi al'washin duk dabbobin nan nine zan gajesu wlh dukkan'su nizan zama sanadiyar mutuwar su , wata murya mara daÉ—in ji sukajiyo daga chikin É—akin inna tana faÉ—in "ae wahalar da kike ba suma habiba am zata iya zama ajalin su, Wani dariya inna tayi san nan tace ae yanzu ma kara nin'ka musu wahalar zanyi, kuma sati nan mai zuwa za'a É—aura Auren buba da shigiyar nan .

Baya baya sukayi suka fita daga gidan suna fita suka rushe da kuka,suna kuka suna tafiya har suka isa kasan itachen mangoro dake É—an bayan gidan su zama sukayi awajen,suka sauke kwaryan nono dake kansu suka chi gaba da kukan su, sai da sukayi kukan mai isarsu san nan sukayi shiru dan kan su, dan duk chikin su ba mai rarrashin dan uwansa

Suna zaune awajen har aka kira sallar mangariba, tukun nan suka mike, suka ɗauki kwaryar nono jiki ba kwari suka nufi gida ko da suka shiga, a tsakar gidan suka samu inna jiki a sanyaye suka karasa chiki gaban ta sukaje suka tsugun na, suka sauke kwaryar,sukayi jugum jugum gwanin ban tausayi suna jiran hukunchi, inna naganin haka tagane basu sayar ba miƙewa tayi tanufi ɗaki ta dauko wani katan bulala tafito, tafara bugun su dashi
Diyana da hiyana suka hadu suka rufe lamrat bulala na sauka ajikin su, bugun su inna take baji ba gani abun tun suna iya kuka ma har kukan nasu ya daina fita duk sai da tamusu ruÉ—u ruÉ—u da jiki, ta kyale su ta kuma fiche daga gidan tana ta mai da numfashi, Amrat na ganin inna ta fita, itama tafito daga É—akin bappa tayo wajen su da gudu tana kuka haka suka haÉ—u a tsakar gida suka rungumi juna sunata kuka, sai da sukayi kuka mai isar su
San nan su kamike jikin dukkan su jikin su sai karman yinwa da wahala yake, suka nufi dakin bappa da sallama suka shiga amma bai amsa musu ba, akusa dashi suka zauna yana kwanche idon sa AbuÉ—e yana kallan sama
chikin shesshekar kuka hiyana tace "bappa ina wuni shiru bai amsa ba " bappa bakada lfy ne diyana ta tambaya a ruɗe, nan ma shiru bai amsa ba Hiyana tasa hannu ta taɓa shi ko motsi bai yiba a firgiche tafara jijjigasa tana ihu tana kiran sunansa Amma shiru
Chikin kiÉ—ima hiyana tafito daga É—akin tayi waje tana ihu

London United Kingdom

Tsaye yake a tsakiyar babban palon su hannun'sa ɗaya na rike da trolley ɗayan hannun kuma yana rike da wayarsa yana latsawa, sanye yake chikin black jeans da blue t-shirt ya rage tsawon gashin kansa, yanzu gashin bata wuche zuwa iya wuyar'sa ba, yana sanye da booth black colour a kafarsa dakuma p-cap shima baki hannun sa na ɗaure da wani haɗadɗen agogon daimon mai kyau da tsada fiskar nan kuwa babu alamar annuri akanta a taure take tam kamar an aiko masa da sakon mutuwa amma yayi kyau sosai laɓɓansan nan kuwa kamar yasa jan baki jaa sosai ga sajen sa a kwanche yasha gyara bakaramin kyau yayiba, faffaɗar kirjin san nan kuwa a tsaye dam dam kamar zai fashe ga damtsen hannun sa a chike kamar zasu yaga hannun rikar, almost 10mnt yana tsaye

A hankali Aryan ke sauko daga saman stair ɗin shima shigarsa iri ɗaya dana DON abun mamaki shima ya yanke gashin kansa ya rage mata tsawo, rike da trolley shima yana ja sauko wa yayi yazo dai dai inda DON ke tsaye, da wan nan sexy voice nashin ya furta sorry bro,DON bai tanka saba yaja trolley sa yanufi kofar fita, da sauri Aryan yabi bayan sa sukayi waje tare, da gudu rundunar jibga jibgan sojojin masu ji da lfy da karfi sunsha trenin suka nufosu, da sauri abdol ya karɓi trolley hannun DON, Shahram kuma ya karɓi trolley hannun Aryan, suka samu su a chikin haɗaɗɗun motachin, da akajera musu dan tafiyar

Aryan yadubi DON yace "muje a mota É—aya koh,DON batare daya amsa ba yace "wai ina Aiman da Ahmad ne "ae tunjiya suka wuche naija Aryan yabashi amsa yana kallan fuskar sa kama hanya kawai DON yayi batare daya sake magana ba yanufi motar, da sauri abdol yabuÉ—e masa kofar motar, slowly ya shiga ya zauna, É—aga hannu Abdol yayi ya sara masa san nan ya rufe kofar motar, zagayowa ta É—ayan kofar motan Aryan yayi, da sauri Shahram ya buÉ—e masa kofar a nitse ya shiga ya zauna Shahram ya sara masa san nan yarufe kofar motar
Da gudu sojojin suka hau nasu motochin su suka tadasu, da matsakai chin gudu suka nufi gate É—in tun basu kariso ba security suka wangale masu gate É—in, da gudu suka danna hanchin motochin waje,motar sojoji 2 a gaba sai motar su DON a tsakiya sai motochi 2 na sojoji a baya gudu suke shararawa a kan mikakkiyar titin

Aryan ya dubi DON yace sai dai fa mutafi da jet ɗinka dan kuwa nawa yana naija dashi su Ahmad suka tafi "Ok kawai DON yache, chikin kankanin lokachi suka isa Airport Already angama shirya komai su kawai a ke jira, batare da ɓata lokachi ba suka fito daga chikin moton su suka nufi kyakkyawa kuma haɗaɗɗen privet jet ɗin DON mai ɗauke da tambarin sunan'sa PRINCE SAFRAS suna shiga batare da ɓata lokachi ba jirgin yaɗaga sai malam Aminu Kano international Airport Kano Nigeria

More comments and share pls

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

💖 The talent troupe writer's 💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 5*

DON
Chapter 12 · 0% Book details