← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 90

Sashe 84

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me kake yi a nan Khalid? Sai lokachin Khalid ya É—ago kirjin sa na dukan uku uku dan shi kanshi yana fargaban ansar da zai bawa Bgs amma kuma ya zama dole ya sanar dashi dan shi gaskiya ya gaji yana son Zahra sosai.
"Hira nazo yi wajen matata ta" tirkashi waro green eyes nashi yayi waje sosai yana kallon Khalid, yayin da shima Khalid yake kallon sa "wai Khalid kaji abun da bakin ka ya furta kuwa? "Kwarai kuwa Bgs naji mana barima na mai mai ta maka hira nazoyi wajen matata kuma kanwata farinchiki na burin raina abun alfahari muradin rai na kai in ta kai che maka itache duniyata komai nawa, mutuwan tsaye Bgs yayi yama kasa chewa Khalid komai, ganin haka yasa Khalid ya miƙe ya fice daga palon ya barshi tsaye awajen.

Yana fita tun bai yi nisa ba yace "alhamdulliah alhamdulliah alhamdulliah, yau dai na gama da duk wata matsala ta, kai Bgs kai dai wlh ina maka adduar Allah ya É—ora maka soyayya wadda bata sonka inga ta tsiya yana magana yana sauke nauyayyar ajiyar zuchiya da haka ya nufi É—akin sa ya haye gado ya kwanta

To masu karatu sai mun hadu Ranar Monday idan mai dukka ya kaimu..✍️✍️✍️

Book 1 fa yana gab da karewa sauran page 3 ko 4

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)

More comments an share

*💫STAR LADY💫*34

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3️⃣6️⃣*

A fusace Bgs ya juya yama fasa shiga wajen Ammin taku yake irin na jaruman maza, ya fice daga part É—in gaba É—aya, part É—in Aryan ya nufa a dai dai wajen part É—in Ummi yachi karo da Yusuf da lamrat sun fito daga part É—in Ummi sun nufi part É—in Ammi sai murnushi suke suna hira kamar wasu kawaye, mamaki da al ajabine ya hana Bgs tafiya kuma ya hana shi magana tunani ya shigayi wai yaushe yaran nan suka dawo hakan, yayi nisa chikin tunani sai jin yayi Yusuf yayi ya É—an tafa kafaÉ—ar sa yana faÉ—in

"Big bro me kuma ka keyi a nan? Wani mugun kallo ya wurgawa Yusuf wadda sai da yasa Yusuf É—in haÉ—iyar wata yawu mai kuyar wuche makoshi, da kyar Yusuf ya iya buÉ—e baki ya sake chewa "my bro lfy kake kallona haka"? A fusache Bgs ya wuche ya nufi part É—in Aryan, batare da ya chewa Yusuf komai ba

Juyowa Yusuf yayi yana kallon lamrat dake tsaye,ta harɗe hannu a kirji tana kallon su "my baby ke kam ba kya tsoron yaya prince ɗin ne? Murmushi lamrat ta yi kafin tace "to ni yaya Yusuf in ban da kaima da neman magana ina ruwana dashi, mutumin da ko magana bai taɓa yi ba, nifa ban taɓajin voice nashi ba kwata kwata, to ai kaga ba ruwana dashi"

Murmushi kawai Yusuf yayi san nan ya jawo hannunta yana faÉ—in "zo muje mu gai da Abba tun da kin gai da Ummi, yau so nake na gabatar dake wa kowa na gidan nan, shima yaya prince É—in naso gabatar masa dake amma sai yayi tafiyar sa sunkuyar da kai kasa kawai lamrat tayi batara da ta che komai ba

Jan hannunta yayi har chikin fada, lamrat sai kokarin kwache hannun ta take dan kunyar Abba takeji amma yaya Yusuf ya riƙe ta sosai kuma yana jin, yadda take ta mutsu mutsu da hannun tana son kwache wa, amma yaki sakinta saima kara riketa da yayi sosai sai da suka isa gaban Abba san nan ya saketa ya samu waje saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna yana faɗin

"Sannu da hutawa Abba" da fara'a Abba ya amsa lamrat kuwa tsugunnawa tayi har kasa ta gai da Abba, sai murnushi yake ya amsa mata san nan ya É—ora da chewa "amarya tashi ki zauna saman kujera, sunkuyar da kai kasa Yusuf yayi wai irin kunyar nan, hararar wasa Abba ya wurga masa yana faÉ—in "au sai yanzu kasan da wani abu wai shi kunya ko"? Bari na samu Ammin ku anjima zan sanar da ita da kai da Khalid duk kar ta kara barin kushiga part nata sai ranar da aka shafa fathiha"

waro green eyes nashi waje Yusuf yayi sosai, chikin voice irin na masu shagoɓa ya fara magana "haba Abba so kake muyi chiwo ne, Allah ko kwana ɗaya ba zan iya jurewa ban ga my baby ba, da gudu lamrat ta tashi ta fice daga fadan dan ta lura shifa yaya Yusuf ɗin nan bai san kunya ba

Zuba masa ido Abba yayi yana kallon ikon Allah
"Abba kasan me wlh ina son kafin mu koma London an shafa fathihan nan sai kowa ya wuche da matar sa" "Yusuf tashi ka bani waje kuma ni ba zan yiwa lamrat Aure a yan shekarun tan nan ba kwata kwata fa she is 14 years tayi kan kanta da yawa" waro ido waje yaya Yusuf yayi kafin yace "haba Abba na pls ai zata karisa girman ta a gida na, nifa Abba banso ma a che Auren mun nan ya wuche nan da 1 week ba"

Kwafa Abba yayi yace "to ka faɗawa babban yayan kune? dan kasan ni dai ba zan maka maliyi ba shine zai maka waliyi ni kuma waliyin lamrat" a sukwane Yaya Yusuf ya miƙe ya nufi hanyar fita yana faɗin "lallai Abba baso kake nayi aure ba a wannan rayuwar, in dai sai na fadawa Bgs ya zamo waliyina to wlh nama hakura da Aure har abada ya kai karshen maganar tare da ficewa daga fadan

Dariya sosai Abba yayi kafin yace "dukkan ku nasan maganin ku ai tun É—azun nake chewa ka tafi kabani waje kaki ka zauna kanamin surutai ba gashi yanzu chikin ruwan sanyi ka tafi ba"

Aɓangaren Bgs kuwa

Kwanche ya samu Aryan saman katafaren gadon sa, idon sa biyu yana kallon sama da alama yayi nisa chikin tunanin da yake, dan ko sallamar da Bgs yayi bai jiba.

Hayewa samab gadon Bgs yayi ya kwanto da fuskarsa dai dai face É—in Aryan É—in, ya kwaro green eyes nashi sosai, a chikin idon Aryan, a sukwane Aryan ya yunkura zai tashi tamke wuyar sa Bgs yayi ya mai dashi ya kwantar, yana faÉ—in "yan zu kuma tunanin me ka keyi?

Chikin fushi ta jin haushin tadda Bgs ya tsoratashi yace "wai dan Allah Bgs me na maka ne? bazaka kyaleni naji da damuwa taba sai ka karamin naka? komawa gefe Bgs yayi ya zauna kamar bai ji me Aryan ya faÉ—a ba, shiru suka zauna Almost 10mnt kafin Bgs ya juyo da kallon sa kan Aryan ya fara magana

"Ina kaunar ka Aryan duk duniya idan ka chire iyaye na ba wanda nake so kamar kai ba zan iya ganin ka a chikin damuwa ba, duk lokachin da ranka ya ɓachi ko kashiga damuwa tofa nafi kowa shiga tashin hankali, dolene na rinƙa yawan tambayar ka meke damunka, dan kai ne mutun na farko da nake kauna bayan iyaye na, daga kai sai Fahad sai Zahra Aunty Farida da kuma Khalid Yusuf Ahmad, ba zan iya ganin damuwar ku, na yi shiru ba"

Da mamaki Aryan ke kallon Bgs "wai wace Zahra kake nufi" Aryan ya jefo masa tambaya yana tsare sa da ido, guntun tsaki yaja kafin yace "daman muna da wata Zahra ne a wan nan gidan bayan Auta "amma lallai Bgs ka iya iskanchin kala kala yanzu daman kasan ana kiran Zahra da sunan Auta, eyee wato duk abun da ake a gidan nan kana sane, amma sai kayi kamar baka san komai ba ko?

"Kaga Aryan ni yanzu ka faɗamin tunanin me kakeyi ban che kamin wasu tambayoyin ba" "yanzu idan nache maka tunanin mace nake me zakache? Dogon tsaki yaja kafin yace "ka hauka che mana me kuma zan che sai na tashi na kama kai na dan ba amfanin na zauna ina magana da wanda bai da hankali, tsaki Aryan ma yaja san nan yace "hmmmm Ni bari naje nayi wanka kana nan ne ko dai in same ka a part naka? Shiru Bgs yayi kamar bai ji abun da Aryan ɗin yace ba, ganin bai da niyar magana yasa Aryan ya miƙe ya nufi toilet ya barshi awajen, Shiru yayi kamar mai tunani jim kadan ya fara magana

"Khalid yana son Auta wow nayi farin chiki da hakan gaskiya domin ko ba komai zata samu farinchiki, amma dai dole Khalid ya chanza kasa dan ba zai zauna damu waje É—aya ba, shi ma Yusuf transfer zan masa ya koma, Us ko India duk kansu bazasu zauna kusa damu da mata a gefen suba"

"Gaskiya ko ni nayiwa Auta murna da samun Khalid a matsayin miji, chewar Aryan dake tsaye a bakin kofar toilet ɗaure da towel a ƙugun sa. Wani hararar Bgs ya wurga masa tare da miƙewa yace "idan ka gama shiri ka same ni awajen Ahmad, yana gama faɗin hakan yayi waje Aryan kuma ya juya ya koma chikin toilet

AUNTY AMARYA

Zaune take saman sofa mai zama mutun biyu tana waya da Aunty Maryam, yaya Umar da yaya Haidar suna zaune a gefen ta saman sofa mai zaman mutun 3, da gudu wata bigaggiyar budurwa ta shigo ko sallama babu tana sanye chikin wasu shaggun riga da wando, wadda kana iya ganin komai na tsurar jikinta, ta zuba gashin doki akai kamar wata aljana, ga wani dogayen gashin ido da ta sanya yarinyar tana da kyau ba laifi farache sosai amma farin mai ne, a shekara bazata wuche 21 year's ba
Chapter 84 · 0% Book details