← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 90

Sashe 86

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani gigitachen ihun azaba Jabir ya saki, bai gama ihun nasa ba Bgs ya sauke masa wani wawan nushi a gefen chiki nan take jabir ba É—auke dif kamar an É—auke wuta nepa alamar ya suma, sakin sa Bgs yayi ya zube kasa wanwar tsallake ta kansa yayi wuche ya nufi office É—in Hm, da sauri rundunar jibga jibgan sojojin sa suka rufa masa baya.

gaba É—aya jama'ar dake waje daga kan malamai har É—alibai, kowa murna yake da bugun da Bgs É—in yawa jabir.

Bgs

Yana kokarin shiga office na Hm shi kuma Hm na kokarin fitowa karo sukayi Hm yayi baya kamar zai faÉ—i, da kyar ya iya sai ta tsayuwar sa, Bgs kuwa yana tsaye kamar wani sadaukin yaki ko motsi bai yiba "sorry sir ban san kana shigowa bane chewar Hm

Bgs dai bai tankashi ba sai ma raɓawa yayi ta gefen sa ya wuche chikin office ɗin saman sofa ya zauna jibga jibgan sojojin 4 ne suka bishi chikin office ɗin hannun su ɗauke da manya manyan bindigu (gun) suka tsaya a kanshi suna bashi tsaro,sauran Sojojin kuma suka tsaya a bakin kofar shigowa

"Sir naji ka bugi wani awaje me ya haɗa ku? Hm ya tambaya yana ƙarisowa chikin office ɗin, dogon tsaki Bgs yaja kanfi yace "kawai naga zai bugi wata yarinya ne shiyasa na bugeshi dan na lura bai da hankali bai san me yake ba" "to wan to kuma wace yarin yace kuma wani yaro ne!? Hm ya tambaya yana kokarin zama a kujera "kai Ni ban sani ba domin duk kansu daga yaron har yatinyar ban ga fuskar ko ɗaya daga chikin suba, ni ba shine ya kawo niba, Abba ne ya aiko Ni, ya karisa maganar yana ya mutse fuska

tunani Hm ya shigayi "ko wani mai karan kwanne yau kuma ya haÉ—u da Bgs domin ina da tabbacin duk wan da Bgs ya buga to fa in bai mutu ba zai yi fama da doguwar jinya ko da ya tashi kuma ba lallai ya koma kamar da ba.

"Yallaboi Abba yace na karɓawa su Zahra transfer later, da sauri Hm ya ɗago ido yana kallan Bgs chikin rawar murya ya fara magana "lfy Abba yake son chan zawa su Zahra school? Mikewa tsaye Bgs yayi yana faɗin "Ni ma ban sani ba idan ka gama ka bawa Abdol later ya kawo min ina mota yana kai karshen maganar ya fice daga office ɗin.

Yana fita jibga jibgan sojojin sa masu ji da karfi da lfy kallo É—aya zaka musu kasan sun samu training mai kyau suka rufa masa baya

Daga malamai har students din dukka kallon Bgs da tawagar sa suke kowan nan su tambayar kan sa yake wanene wan nan? Ko dai É—an shugaban kasan American ne, dan wan nan bai yi gama da É—an naija ba, awani ban garen kuma murna students keyi an musu maganin jabir yau dai kam an samu wadda ya tanka shi har ma ya sumar dashi, bangaren yan matan school É—in kuwa kowanche mutuwa take akan Bgs da bai ma san sunayi ba, ko wacce fatan samun sa amatsayin miji take ba karamin rikitasu kyan shi yayi ba

Taku yake irin na manyan jarumai har suka kai in da sukayi parking motochin su da gudu wani matashin soja ya sha gaban sa ya buÉ—e masa kofar motar, shiga yayi ya zauna ya zuro kafafun sa waje ya sunkuyar da kai kasa yana latsa waya, da alama jiran Abdol suke

Aɓangaren hiyana kuwa

Da gudu ta nufi class ɗin su Zahra sai numfashi take sama sama, Zahra na ganin ta ta miƙe ta nufeta tana faɗin "hiyana lfy kike numfashi haka!? Me ya saki gudu kuma!? "Aunty Zahra yaya prince a school namu kuma ina da tabbachin ya bugi jabir" waro fararen manya manyan ido ta Zahra tayi ta dafe kirji chikin tsoro tace "mun shiga uku hiyana me kuma ya haɗa shi da jabir!? Allah yasa dai ma bai kashe shiba ya tsaya a iya bugu" "wlh Aunty Zahra ai jabir dinne ya rikemin hannu ni kuma na mare shi, shima ya ɗaga hannu zai rama kenan sai yaya prince ya rike hannun sa"
"Wayyo hiyana munshiga uku yanzu kina nufi a akan ki yaya prince ya bugi jabir!? Kuma ya ganki yasan dake jabir yake faɗan!? "Aa Aunty Zahra bai ganni ba domin lokachin da ya riƙe hannun jabir ɗin latsa wayar sa yake da alama wani sako yake turawa shiyasa ai na gudu dan karya ganni, yace nima zai hukun tani dama ni kam ya tsane Ni" ta karisa maganar kamar zatayi kuka rungumeta Zahra tayi tana faɗin "ki dena chewa ya tsaneki kin ji Allah yaya prince bai tsane ki ba kawai shi dai haka halinsa yake ne"

"Wai ma me ya fito dake daga Class naku ne? Har kika haÉ—u da jabir É—in" "daman kai nane yake min chiwo nache bari nazo ki rakani office na Hm dan yasa amai dani gida ina tafiya a hanya ya tareni" "to shike nan yanzu muje wajen Hm É—in sai amai dake gida koh?

"Kai Aunty Zahra ni wlh idan ki kaga na fita daga class nan to sai naji fitar motochin su yaya prince daga school nan kuma ma ai kan ya warke ya daina yimini chiwo" dariya Zahra tayi tare da raba jikin su tace "kai hiyana sarkin tsoro In Sha Allah ke che zaki zama matar yaya prince ɗin nan sai naga karshen tsoron" "dan Allah Aunty Zahra ki dai na yimini mugun fata kinji wlh ko da wasa naji an kira sunan shi ji nake zuchiya ta na bugawa da karfi" hannu ta Zahra ta riƙe suka koma wajen zaman ta suka zauna suna yar hiran su, yammatan class ɗin sai kallon su suke, kamar wasu tagwaye domin kamin nin Zahra sak yaya prince haka itama hiyana kamannin ta ɗaya da shi shiyasa suke kamar ta gwaye gashi yanayin jikin su ɗaya yan sirara sai dai hiyana ta ɗara Zahra tsawo kaɗan, Zahra kuma ta girmi hiyana da shekara 1.

Maiduguri

Kyau iya kyau diyana tayi kyau har ta gaji da kyau idan ka ganta zaka che yarinyar nan da madara take wanka saboda sabulan da Aunty farida ta haɗa mata ba karamin gyara ta yayi ba gata da iya ɗaukan wanka da make up ta chanza sosai ta kara haske fatar ta tayi luwai luwai ga wani sihirtachen kamshin dake tashi ajikin ta, yauma kamar kullun ta Chi kwalliya sosai kamar ka sa che ta gaje ka ajiyeta ka yita kallon ta kamar madubi dan kyau, sanye take chikin wata dan kareriyar lace Sky Blue da zanen fulawa baki a jiki, ɗinkin riga da sket ba ƙaramin zama kayan sukayi a jikin taba kamar daman a jikin nata akan ɗin kasu, ga wani haɗaɗiyar high heel baki da ta sanya

jama'a ya kuke ganin farin kafa da bakin takallama? sai É—aukan ido kafar nata yake ga kunbar (farche) kafar ta nan yasha gyara fari tas dashi sai sheki yake ta sanya mayafi baki kalar takalmin ta ta zuba wasu É—ankara É—ankaran sarka da abun hannu na gold wadda Aunty farida ta bata, jakar ta ta É—auka ta nufi waje

Taku take a hankali sai wani yauki da yanga take kamar bata son taka kasa ta fito harabar gidan, Aiman dake zaune chikin mota tun daga nesa ya zuba mata ido yana kallon yadda take taku chikin yanga da yauki har ta iso wajen motar ba tare da ya ankara ba, fitowa wajen Aunty farida tayi daga chikin nata motar tana faÉ—in "wan nan irin kwalliya haka my diyana dole namiki" murmushi kaÉ—an diyana tayi san nan tace "ngd Aunty farida"

Chiro wayar ta daga chikin jaka Aunty farida tayi tace "to my diyana gyara na É—auke ki, gyara tsayuwa diyana tayi Aunty farida ta fara É—aukan ta hoto har kala 10 ta É—auke ta san nan tace "to ya isa haka shiga da wuri muje dan kar lokachi ya kure jirgi ya tashi ya bar yaya Aiman a nan"

"Aunty farida na shiga motar ki ne ko kuma naje na yaya Aiman? "Duk wan da kike so my diyana" "to bari na shiga na yaya Aiman, bata jira amsar Aunty farida ba ta buÉ—e gidan baya ta shiga kusa da shi ta zauna, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke wadda sai da yasa diyana juyowa tace "yaya Aiman lfy murmushi kawai yayi mata dai dai lokacin driver's suka tada motochin, da gudu baba mai gadi ya wangale musu katafaren gate É—in chikin ni tsuwa suka danna hanchin motochin waje
Sunyi nisa da tafiya yaya Aiman ya juyo da kallon sa kan diyana da kyau ya fara magana

"baby diyana in son ki bani hankalin ki magana mai muhimmanci nake son muyi" É—ago blue eyes nata tayi tana kallon sa chikin sanyin murya tace "to yaya Aiman in jin ka

"Ni ba zan ɓoye miki ba gaskiya ina son ki Auren ki kuma zanyi kuma na san kin san da hakan ko? Sun kunyar da kai kasa diyana tayi tana wasa da yan ya tsun ta "baby diyana ko baki so nane? Yayi maganar yana ɗan dukar da kansa kasa yana leken fuskar ta
"Ina son ka mana yaya Aiman kai fa yayana ne idan ban soka ba waye zan so? "Baby diyana ni fa ba irin wan nan soyayyan ba soyayya irin na Aure nake nufi ba na yaya da kanwa ba" "eh yaya Aiman soyayya irin na Aure'n ina son ka Nima.

Wani farinciki kine ya lullɓe sa ji yake kamar ya jawota ya rungume ta ajikin sa ko zai samu saukin a zuchiyarsa

A ɓangaren diyana kuwa, kuka take a zuchiyar ta tana faɗin "No yaya Aiman me yasa zaka min haka ni wlh yaya Aryan nake so ba kai ba, amma ba zan iya chewa bana son kaba kuma bazan iya chewa yaya Aryan nake So ba, Ni ban ma sani ba shin yaya Aryan yana sona ko dai kawai a matsayin kanwa ya ɗaukeni ni yanzu ya zanyi da rayuwata wayyo Hiyana ta kizo ki che cheni awan nan bala'i daman kin saba taimako na, ya Allah ka kawo min mafita
Chapter 86 · 0% Book details