← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 90

Sashe 34

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye betroom É—in tanufa basallama tashiga babu kowa a chiki dan haka tanufi kan table É—in ta ajiye coffee É—in har zata juya tafita saikuma idanta ya sauka kan hotunan Aryan dake kan drowar gefen gado ansasu chikin freme kanana,
zagayowa tayi tawajen ta zauna a bakin gadon tasa hannu ta É—aukoh hotu nan dukka ukun É—aya shida don ne sunsa kakin sojoji É—ayan kuma shi kaÉ—ai ne sanye da jeans baki da white t-shirt É—ayan kuma shida don da yusuf ne dukkansu da wandon sojoji ajikinsu da green t-shirt, shiru tayi tana kallansu chankuma tace kai ashe da gaskenefa hiyana nakama da wan nan mugun tayi maganar tana nuna don kai kuma yaya Aryan inshaa allah soja zan aura wanda zaimin maganinka da kai da bindigar taka, allah sarki yaya yusuf wlh a gidan nan shida yaya Khalid ne kawai mutanen kirki hakadai diyana tayita surutun ta ita kaÉ—ai har ya isheta san na ta ajiye hoto nan tamike tajuyo zata nufi waje idanta ya sauka chikin nashi tsaye yake abakin kofar shigowa betroom É—in ya harÉ—e hannu a kirji ya zuba mata ash eyes nashi kallanta kawai yake yakasa É—auke kai
Murya na rawa tace ina wuni yaya Aryan " ajiyar zuchiya Aryan ya sauke san nan yakarisa shigowa É—akin yazauna a bakin gado " diyana naganin ya matsa a hanya yazo ya zauna a bakin gado ta watsa a guje zatayi waje saidai tamanta high heel tasa bazata iya gudu sosaiba,
taku biyu Aryan yayi ya damki kugunta ta baya tsabar tsoro da razana yasa nunfashinta É—aukewa É—if " jin jikinta ya sakine yasa ya riketa da kyau kana ya juyo da ita yana kallan fuskarta da alamar ta sume fa É—aukan ta yayi ya kaita kan faffaÉ—ar gadansa ya kwantar da ita, zubamata ido yayi sosai yana kallanta from head to toe wow ya furta a filli kana yace masha allah koba komai yaudai ansa É—an kwalin nan shafa gefen fuskarsa yayi tare da sauke ajiyar zuchiya yajuya yanufi inda ta ajiye masa coffee É—in
Daukan cup ɗin yayi yabar plate ɗin yanufi saman sofa ya zauna yafara sha a nitse sai dayaga sha san nan yamike yanufi freig ruwan faro ya ɗaukoh yadawo kan gadan zama yayi a gefen gadan san nan yabuɗe robar ruwan ya tarfa a hannunsa ya shafa mata a fuska dogon numfashi taja tareda sauke nauyayyar ajiyar zuchiya a hankali tafara buɗe idanta karaf ta saukesu a chikin nashi dankuwa shima kallanta yake " da sauri ta rufe idan ta tana faɗin dan allah yaya Aryan karka bugeni natuba bazan sake taba maka komai na ɗakin kaba " wai ma menamikine dakike chemin mugu akoda yaushe chewar Aryan " batare data buɗe idoba tace natuba bazan sake chewaba " to idan kikasakefa " da sauri tace kamin duk abun da kakeso " kintabbatar inkinsake namiki kome nakeso chewar Aryan " eh nayarda kamin kome kakeso amma dai yanzu kayi hakuri wlh barchi nakeji " Aryan ya jinjina kai yana faɗin to buɗe idon ki, ki kalleni " slowly tabuɗe idon still dai ita yake kallo ganin bazata iya haɗa ido dashi bane yasa ta juya idonta tana kallansama " murmushi kaɗan Aryan yayi a'zuchiyarsa kuwa yana faɗin a shedai tanajin kunya " jin yayi shirune yasa tace yaya Aryan intafi ɗaki " kinasan tafiyane chewar Aryan " da sauri tace eh " ok to tashi kije dasafe zamiyi maganar danake san muyin " da sauri tamike har takai bakin kofa sai taji Aryan yace ke, da sauri ta juyo tana kallansa " a hankali yafurta kinyi kyau sosai dakikasa ɗan kwali " murmushi tayi san nan tace to yaya Aryan tunda nayi kyau pls kamin hoto idan kamin ni kaɗai sai kuma kamana mubiyu " ok to zokitsaya namiki " da sauri ta dawo chikin ɗakin wayarsa ya ɗaukoh yafara daukanta hoto duk san hotonta sai da, da kanta tace to ya isa yaya Aryan saura nida kai kama ko guda ɗayane tare " Aryan yace ok to zoki zauna yayi maganar yana nuna mata gefensa " zama tazo tayi a gefensa " ɗan karkatowa kaɗan yayi yarage tsawonsa ya haɗe kansu ya saita wayar yafa ɗaukansu hoto sai daya musu kala 10 tukun nan yace to jeki kwanta " to tache masa san nan tamike tafiche daga ɗakin " ajiyar zuchiya mai nauyi ya sauke san nan a fili yace Aryan waishin meyake damunkane shiru yayi yana tunani dayaga tunanin nan bawata mafita dazata bashi sai ya karisa hawa gadon kawai ya kwanta ya ɗauki remote ya rage gudun AC yayi shiru kamar mai tunani yana fuskantar sama har barchi ɓarawo ya ɗaukesa

Diyana kuwa tana fita tayi bangarensu basallama kawai tafaÉ—a É—akinsu zaune tasamu zahra a kan gado zahra naganinta tamike tana " faÉ—in diyana lfy kika Jima allah dai yasa yaya Aryan bai bugekiba"guntun tsaki diyana taja san nan tace eh bai bugeniba" Alhadulillah zahra tace san nan takoma ta kwanta " itama diyana kayan jikinta tachire tasa na barchi ta haugado tana faÉ—in hmmmm wato hiyana kam barchinta ma tayi koh " to me zata zauna tamiki barchita zatayimana chewar zahra " diyana bata sake magana ba saima juyawa datayi tana fuskantar yamma har barchi ya É—auketa

Misalin karfe 4 na asuba gaba É—aya family sun haÉ—u suna sahur ban da don " Aryan ya dubi diyana yace ke jeki kawomin coffee " diyana na kokarin mikewa " aunty amarya ta dakamata tsawa ke yizamanki bazata kawoba kuma daga yau nahana maganar coffee idan kannenka maza bazasu kawoma ba to kahakura da sha " shiru palon yayi babu wanda ya tanka diyana kuwa tsayuwa tayi tarasa maganar wazata bi, idan taje takawo coffee aunty amarya zata hukuntata, idankuma bata kawoba yaya Aryan zai hukuntata kawai sai tafasa ihu " gabaÉ—aya jamaa'ar palon suka É—ago suna kallonta " a nitse Aryan yace kukan ya isa zokiyi zamanki kyale coffee É—in " ai tunbai gama maganaba ta zauna abunta takuma yi shiru " dogon tsaki fahad yaja san nan yace darabon wlh nizan babballa yarinyar nan yanzu dan iskanchi me aka.... bai karisa baganarba sakamakon mugun kallon da Aryan ya wurgamasa " aunty amarya kuwa mike tayi tana faÉ—in kai idan kagama kazo É—aki inada magana da kai tayi maganar tana nuna Aryan san nan ta fice " dogon tsaki aiman yaja san nan shima yamike yana faÉ—in dole nabar kasar nan gobe yayi waje " mai marbata kam ido kawai yake binsu dashi " Ummi tace ba akaiwa prince a'binchinsaba'fa " Ammi tace to su tashi sukai masa mana " fahad yamike yana faÉ—in barinaje na kaimasa san nan yayi waje

Mikewa aryan yayi zaiyi waje " Mai martaba yace inazaka " alwala zanje nayi Aryan yabashi amsa " ok idan mundawo masallahchin kasameni a É—aki chewar mai marbata " ok kawai Aryan ya amsa dashi san nan yayi waje " mai martaba ma mikewa yayi yana faÉ—in to yakamata kuje kuyi alwala dan sauran 20 mnt afara kiran Sallah yana gama faÉ—in haka yanufi É—akinsa " mikewa sukayi da É—ai É—ai sukabar palon

Misalin karfe 9 zaune take a chikin class nasu uncle nasu yashigo yana tambayat wacece fateema abubakar saraki " da sauri zahra tace nine" oh to kifito zakuje duba uncle nakune bai da lfy kowani class zamu É—auki mutun É—aya " to kawai zahra tace san nan ta É—auki jakarta tafito sukayi waje da uncle nasu yan mata 7 tasamu tsaye a wajen tare suka jera har wajen motar makarantar suka shiga da gudu motar tabar makarantar " suna tafiyane Zahra ke tambayar yanmatan wani uncle ne bai da lfy
Sukache mata wlh suma basu saniba " shiru zahra tayi batasake maganaba har suka isa gidan uncle É—in driver na parking suka fito uncle Aminu yamusu jagora zuwa chikin gida ga mamakinta saitaga uncle Omar nefa nan tafa tunanin wai ba jiya suka rabu lfy'ba kodai accident yayine ga kafarsa duk bandeji gashi har goshinsa, tayi nisa chikin tunanin sai taji muryan uncle Omar yana faÉ—in fateema har dake a kazo " eh uncle inawuni yajiki zahra tabashi amsa " lfy fateema jiki da sauki " to allah yakara sauki chewar Zahra gaba É—aya suka amsa da amin san nan suka mike suka masa sallama yana musu godiya har suka fice sukaje sukashiga motar makarantar ta maidasu
Chapter 34 · 0% Book details