← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 90

Sashe 9

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty farida Ammi Ummi da Aunty amarya sai Khalid da Zahra zaune suke awani katafaren palo mai girman gaske, mai ɗauke da manya manyan Sofa masu matikar kyau da tsada ga laushi set biyu launin milk colour, ga wata makekiyar Tv daga gefe, sai table ɗin chin abinchi mai ɗauke da gujeru 12, idan nace zan tsaya zayyana muku kyan palon nan tofa zamu kwana a nan, zaune suke shiru,sallama Fahad yayi ya shigo palon zama yayi a saman 1str yana gaidasu Ummi, da sallama haidar da Umar ma suka shigo da alamadai family meeting zasuyi Almost 20 mnt suna zaune ba wanda yake magana kowa da abun da yake daga masu latsa waya sai mai daddan na laptop "wayar Aunty farida che yayi kara alamar shigowar kira, ɗaukar wayar tayi tana bin screen ɗin da kallo,ganin sunan my prince, yana tamiƙe da sauri tayi waje,daga gefen bakin kofar ta waje ta tsaya san man tayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnenta tace "hello prince daga ɗayan bangaren DON yace "kun gama meeting ɗin ne "aa yanzu dai zamu zamu fara Abba muke jira yafito "to amma kina ganin zamuyi nasara kuwa "kai prince kabari dai idan mungama mayi magana, naji muryan Abba yafito bata jira amsar'saba da sauri ta katse kirar, ta koma chikin palan, wajen zamanta takoma ta zauna
Abba kyakkyawar dattijo ne mai chike da kalama, kallo É—aya zaka masa ka gane duk yaran gd ka'maninsa suka yo farine tas mai dogon hanchi ga manya manya ash eyes yana da dogon gemu da lallausan saje, gashin kansan nan a kwanche kamar na larabawa zama yayi saman sofa mai ma zaunin mutun1 bin yayan sa yake É—aya bayan É—aya da ido yana kallan su shiru palon yayi Almost 5mnt san nan Abba yayi gyaran murya, yafara magana ina Aliyu yake,yayi tambayar bai kai ga rufe baku ba uncle Aliyu yashigo da sallama sanye yake chikin wata dakakkiyar shedda fara tas mai kyau da tsada, kaman'nin sa É—aya da Abba, gaba É—aya palon har suna haÉ—a baki wajen amsa masa sallamar da gudu Zahra tamike ta nufe sa tana faÉ—in "oyoyo uncle Aliyu oyoyo ta faÉ—a jikin sa, rungumeta yayi shima tana faÉ—in "oyoyo autar'mu oyoyo autar'mu san nan ya zare daga jikinsa ya rike hannunta suka nufi wajen Abba saman sofan dake kusa da Abba uncle Aliyu ya zauna tare da zaunar da Zahra a gefen sa, a nitse uncle Aliyu yace ina kwana yaya da fara'a Abba ya "amsa lfy, juyowa yayi ya gaida su Ammi, suma da fara'a suka amsa masa san nan matasan gidan suka fara gai dashi yana amsa musu É—aya bayan É—aya da murmushi a face nashi
A nitse Abba yafara magana to ku bani hankalin ku nan,duk suka nitsu suka zubawa Abba ido suna saura ren sa chigaba da magana Abba yayi "nataraku a nanne dan inasan magana daku gaba É—ayan ku amma baku gama haduwa'ba dan haka farida ki kiramin sauran yan uwan naki awaya kifada musu duk Abun da suke subari nan da rana ita yau ina bukatar kowa a nan,"
Aunty farida zatayi magana Abba yaÉ—aga mata hannu aa farida umarni'ne kuma banasan É—aya daga chikin ku yamin wata magana kutashi kuje zamu sake magana rana ita yau
sai yanzu nagane aina su DON suka É—au koh idan sunyi magana basa chan zawa ashe awajen Abba ne tab aiko akoi kallo wayyo

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

💖 The talent troupe writer's💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 4*

YOLA

Almost 11 na dare hiyana na waje tana neman diyana amma shiru shiru ba diyana ba lbrn'ta hiyana tayi kuka har ta godewa Allah kamar zatayi hauka, ta juyo ta dawo gida jiki a sake ba kwari, yanzu tama daina jin yinwar da takeji burin ta kawai taga Æ´ar uwar'ta
tana shiga gida É—akin su tanufa kwanche tasamu lamrat da amrat manne da juna sunyi barchi, ga hawaye nan abushe a fuskar su da'alama sunyi kukan yinwa har sun gajine barchi ya dauke su
zama tayi akasa kusa dasu su,ta zuba musu blue eyes nata, wasu siraran hawayen takai'ci nabin kunchinta duniyar tunanin inda diyana take tafaɗa, kamar daga sama taji an bude kofar zanan ɗakin nasu an shigo, zubur tamike tana kallan sa ɗauke yake da wani abu a'kafadarsa kamar mutun hasken fitilar baya haska su sosai shiyasa bata gane me yake ɗauke dashi ba, murya na rawa "tace yaya bello kaine, kasa kasa bello yafa magana "eh nine kana ya raɓa ta gefen su lamrat ya kwantar da diyana, a ruɗe hiyana tace "yaya bello me yasame'ta'? aina kagan'ta? Ta mutune'? Naga bata numfashi
"hiyana kinitsu mana bata mutu ba suma tayi, kinga yanzu dare yayi zanje gida da safe in kunzo É—eban ruwa saimuyi magana,in bahaka ba kinsan idan inna ta ganni to nashiga uku, dan haka kiyi shiru karma taji wani motsi, yana gama faÉ—in haka yajuya ya fiche daga É—akin
itakuwa hiyana ta gyara zaman ta, tana kallan fuskar diyana tana kuka, haka ta kwana kamar yadda taga rana haka taga dare

washe gari tun asuba inna ta shigo ɗakin nasu hannu ta riƙe da tulu mai ɗauke da ruwa da karfi ta zubawa diyana nan take diyana ta farfaɗo tana ihu, inna bata bi ta kanta ba ta juya ta zubawa amrat da lamrat a razane suma suka farka, juyawa inna tayi ta zuba sauran ruwan a awajen Kwan chiyar hiyana a tunanin ta hiyana na ɗakin,Amma sai taga akasin haka ba hiyana a wajen a fusache ta juyo gun su diyana zatayi magana taji diyana na sambatu, tana faɗin "dan girman allah buba ka kyale ni kayi kahuri, wayyo allah hiyana ta ina kike kizo ki chech..bata karisa maganar ba taji saukar duka ta ko ina ajikin ta, ihu diyana ta fasa wayyo Allah na shiga uku hiyana kizo ki tai makeni buba zai kashe ni, wani bugu inna ta kai mata a baki sai da bakin nata ya fashe, ihu a zaba diyana ta saki, shake mata wuya inna tayi tana faɗin "me buba na yamiki da za kiche ya kyale ki, ko kinga buba a nan ne eh, kodai wani mugun abun kuke shirya masa, jin maganar inna yasa diyana ta dawo chikin hayyachin ta, da kyar ta iya faɗin "inna kiyi hakuri zan mutu dan Allah ki sake min wuya, naushi inna ta sake kai mata a baki tana faɗin "ki mutu mana ina ruwana daman uban me kuke tsinanamin a gd ba gara ku mutu kowa ya huta ba, kara shake diyana inna tayi sosai sai dataga blue eyes nata sun fir fito waje sosai tana kokarin mutuwa da gaske,da sauri ta sake ta tana mai da numfashi, juyawa tayi tana kallon amrat da lamrat in da suka takure waje guda suna hawaye chikin tsawa tace "ke lamrat kitashi kije ki ɗoramin girki idan kin gama kizo kitafi talla, ke kuma amrat ki wuche kije kimin wankin kayana kiyi shara da wanke wanke, itakuma wan nan shai ɗaniyar ni zata sa na zubar da ruwa a kasa koh to wlh gaba ɗaya ruwan gidan nan sai na zubar dashi ku ɗebo wani, ke diyana ki tashi ki ɗauki kofin ki nemo wan nan shai ɗaniyar kufara ɗebomin ruwa kuma wlh daga nan zuwa karfe 10 ku chika komai na gd nan, dan dole yau ku jemin tallah ba zanyi asara ba, tana gama faɗin hakan,
ta juya tayi nufi hanyar fita har ta kai bakin kofa sai kuma tace wlh idan kuka bari na kai tsakar gd baku fito ba na lahira sai yafi ku jin daÉ—i, jiki ba kwari lamrat da amrat suka mike suka fice suka bar diyana kwanche baki na jini sai kuka mara sauti dake

Inna na fitowa tayi karo da hiyana a tsakar gida hannun ta rike da cup guda biyu da alama ruwa take É—ebowa "ke ni zakiwa iskanchi to wlh barikiji duk ruwan dake gidan nan saina zubar dashi a kasa kun É—ebo wani, san nan kuma ke kafin kifara zubawa a randu nan nan, sai kinyi sahu 10 kina É—ebowa kina zubar wa a kasa har sau 10 tukun nan, kifara zubawa a tulu, ni zakisa nayi a sara ruwa ba nashiga É—aki zan tashe ki ashe ba kinan ki kasani na zubar da ruwa a kasa koh, ke gaki mai wayau tun asuba kintafi É—ebo ruwa, kuma barikiji duk yadda zakuyi kuyi nan da karfe 10 dole kuchika ko ina na gidan, nan san nan ku jemin talla dan yau bazanyi asaraba, tana kaiwa nan ta wuche tanufi kichen, tafara zubar da ruwan dake chikin randu nan da kuma tulu nan,sai da ta tabbatar babu wani tulun daya yage da ruwa a chikin sa san nan tafito tawuche É—akin ta ta haye gado, babusallar asuba
Dur kushewa kasa hiyana tayi ta rushe da matsanan chin kuka, mai tsuma zuchiyar mai sauraro, kuka take kamar ranta zai fita sai datayi kukan, mai isar ta san nan ta É—ago kai tana kallan su amra dake tsaye a bakin kofar dakin su, alama ta musu da hannu aka sutafi sufara aikin su kar inna tafito ta gansu, ganin babu diyana a wajen ne na yasa ta mike da kyar tanufi É—aki dan tadubo ta
Chapter 9 · 0% Book details