← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 90

Sashe 40

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan diyana tagama chin abinchinta tamike tanufi toilet wanka tayi tafito daure da towel kayan barchi tasa doguwar riga mai siririn hannu yar shafal mara nauyi kwanche ta iske su Zahra sunata yar hirarsu, dayake yanzu su amrat ma sun dawo É—akinsu, saboda suna tsoro tunda ba kowa a gidan sai suka haÉ—u suka chure waje guda
Hayewa samar gadon nasu tayi itama tana faɗin Aunty Zahra kunna mana kallo " to kawai Zahra tace tare da dauko wayarta dake gefenta ta shiga gallery tana kokarin neman film sai taga kira yashigo " da sauri tayi picking call ɗin tana faɗin yaya Khalid bakayi barchiba " eh banyi barchiba ya'za'ayi nayi barchi bamuyi wayaba " Zahra zatayi magana sukaji an banko kofar ɗakin nasu da karfi gaske " zubur suka mike gaba ɗayansu har sai da wayar Zahra tafaɗi kasa dan tsorata dasukayi " a zafafe Aunty Maryam ta shigo chikin ɗaki kai tsaye wajen diyana tanufa damkoh wuyarta tayi tafara bugunta ta ko ina " diyana tafara ihu " nizaki haɗa faɗa da ɗan uwana koh to wlh yau sai na kasheki, tun danake dashi baitaba kirana a wayaba amma yau saboda'ke sau biyu yana kirana bugunta Aunty Maryam keyi tana surutai " diyana kuwa sai ihu take " hiyana naganin Aunty Maryam na kokarin kashe diyana da gaske ta kwasa a guje tayi wajensu tana kokarin kwache diyana a hannunta " hankaɗe ta Aunty Maryam tayi da karfi ta tafi ta bugu da bango nantake kanta yafashe " ihu mai karfi Zahra tabuga tayi kan hiyana tana kiran su nanta " lamrat da amrat kuwa sai kuka suke " duk da raunin da hiyana taji bai hanata sake mikewa a zafafe tayi kan Aunty Maryam tana faɗin karki kashemin ƴar uwa dan allah " wani bugu Aunty Maryam tasake kaiwa hiyana a baki " kukan kura hiyana tayi a fusace ta damki wuyar Aunty Maryam ta baya " bashiri tasaki wuyar diyana ta juyo ta damki hiyana tashiga bugu " da gudu Zahra tazo ta duƙa takama kafar Aunty Maryam tana rokonta " dan allah Aunty Maryam kiyi hakuri ki kyalesu wlh marayune basu da uwa basu.. Zahra bata karisa ba taji saukar mari a faskar ta a zafafe Aunty Maryam tace. Kifita a ɗakin nan zahra'u kokuma na haɗa dake " mikewa Zahra tayi tana kuka takama hannun amrat da lamrat tace muje " kwache hannunta lamrat tayi tayi gun Aunty Maryam da gudu tana faɗin dan allah ki kyalemin yan uwana haka " kafa Aunty Maryam tasa ta amɓare lamrat tafaɗi kasa tana kuka " da kyar diyana tamike tana ɗingisa kafa ta karisa wajen ta duka gaban Aunty Maryam tace ninamiki laifi basuba kiyiwa Allah kisakemin yar uwata ni ki kasheni inkinaso " juyowa tayi ta damki wuyar diyana ta damkoh hiyana ta haɗe kansu ta buga da karfin gaske wani kara suka sake a tare " Zahra da amrat dake tsaye a bakin kofa da gudu suka dawo chikin ɗakin " Aunty Maryam kuwa duk da hakan bata kyalesuba sake damkar gashin kan diyana tai tana janta a kasa har zuwa wajen mirrow tasa hannu kan mirrow ta dauki wani kwalbar turaren humra zata buga mata ke nan taji anche STOP chikin tsawa da sauri ta ɗago kai idanunta suka sauka akan...✍️✍️✍️

More comments an share pls 🙏

*💫STAR LADY💫*27*

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 16*

Idanta ya sauka, a kan shahram dake tsaye fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa babu alamar wasa a tattare dashi " sakin diyana, tayi tana mai da nunfashi " karisa shigowa ɗakin yayi yana faɗin get out yayi maganar yana nuna Aunty Maryam " kallan raini ta tsaya take masa daga sama har katsa dogon tsaki taja, tanunashi da ɗan ya tsa tace kai karamin marakunya ni kake chewa nafita to kashirya karɓan hukunchi " shikam Shahram ko ajikinsa, dan daman bajin hausa yakeba bare yaji me tache, sai ma kallan Zahra dayayi yace all of U follow me yana gama faɗin hakan yajuya ya koma bakin kofa ya tsaya " wuchewa Zahra tayi taje ta taimakawa diyana tamike " Aunty Maryam na tsaye suka raɓa gefenta suka wuche, tanasan ta damkoh diyana tachi gaba da bugu kuma tana tsoron yadda taga fuskar Shahram ba wasa hakan yasa ta fiche a ɗakin a fusache " Shahram ganin sun mike sun nufosa yasa yayi waje, suka bi bayansa bai tsaye wajen motochin gidan suka nufa da kansa ya buɗe musu marfin family car suka shiga gaba ɗayansu " shima shiga yayi yaja motar da gudun gaske nan take security dake tsaron gate suka wangale masa gate ɗin " dagudu ya danna hanchin motar yayi waje doguwar titi yamiƙa dasu gudu yake sosai chikin ƙanƙannin lokachi suka isa wani katafaren asibitin DON dake kan titin zoo road " suna parking ya fito yabuɗe musu motar bayan sun fito yayi gaba suƙa bishi a baya " diyana daker take ɗinkisa kafa " hiyana kuwa goshi sai jini yake, gaba ɗaya jinin ya wanke mata face " kai tsaye office ɗin baban dr yanufa " security dake tsaye a bakin office ɗin suna ganin Shahram suka shiga sara masa kamar sunsan juna buɗe musu kofar office ɗin sukayi suka shiga " babban dr naganin Shahram yamike yana miƙa masa hannu, miƙa masa hannu Shahram ma yayi suka gaisa san nan yakora mara bayani a kansu diyana " da sauri dr peter ya ɗauki waya yakira nursing " nursing na shigowa dr peter yabata umar a kan ta tafi dasu diyana tabasu gado gashi nan zuwa yadubasu " har ɗakin da a ka kaisu sai da Shahram ya bisu sai da ya tabbatar sun fara samun kulawar Dr san nan yafito ya nufi motarsu yatayar yanufi gd

A bangaren Aunty Maryam kuwa tana komawa ɗaki ta ɗau'wayarta tafara kiran layin Aryan dan taji ko shiya aiko Shahram amma ba'a ɗagaba sai data kira miss call 10 amma ba'a ɗagaba san nan ta hakura ta ajiyewayar tana ta surutai wlh Aryan kazo gaɓar da bazan kyalekaba, ina ruwanka dan nabuge yaran nan toma waya faɗamaka ina bugunsu dole na binchiko ta ina kasamu lbr, haka dai take ta surutun'ta

Yadda akayi Aryan yasamu lbr Aunty Maryam na bugunsu diyana har ya'turo Shahram

Lokachin da Khalid ke magana da Zahra yaji tayi shiru sai hello, hello kawai yake amma ba amsa har zai katse kirankuma sai yaji ihu, nantake hankalinsa yatashi yamike yanajin yadda Aunty Maryam ke bugunsu, da sauri yanufi ɗakin Aryan rike da wayarsa yana zuwa yamikawa Aryan wayar " muryan Aunty Maryam sukaji tana faɗin nizaki haɗa faɗa da ɗan uwana," bai taɓa kirana a wayaba amma yau yakirani har sau 2 saboda ke " a fusace Aryan yayi wurgi da wayar Khalid yamike, nan take fuskarsa ta Sauya idon nan suka chanza sukayi jawur dasu kamar an watsa barkono, wayarsa ya ɗaukoh sai huchi yake kiran layin Aunty Maryam ɗin yafarayi Amma shiru shiru har 3 time rai a ɓache yayi wurgi da wayar, yanufi hanyar fita " da sauri Khalid yarikesa dan ya lura baya chikin hayyachen'sa inazakaje Aryan chewar Khalid " Nigeria zanje mana " dariyane sabo kuɓchewa Khalid amma sai yadanne yace ai kokatafi yanzu ba yanzu zaka isaba kafin kaje kuma duk abun da zai faru yarigada yafaru, yanzu dai kakira wani daga chikin security nan suje su kashe wutar, ai tun Khalid bai kai karshen magana ba "Aryan yanufi wayarsa da sauri ya ɗaukoh yafara kiran layin Shahram, " Shahram nayin picking call ɗin " Aryan yabashi umarnin yaje ka dakatar da Aunty Maryam daga bugun su diyana datake san nan ya ɗaukesu ya kaisu asibiti, yana gama faɗin haka ya katse kiran ya zauna a bakin gado ya dafe kai
Kusa dashi Khalid yazo ya zauna ya sa hannu ya dafa kafaÉ—arsa zaiyi magana ke nan sukaji sallamar DON
Chapter 40 · 0% Book details