← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 90

Sashe 33

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye tawuche betroom batayi sallama tashige kwanche yake a kan gado idansa a lunshe har bakin gadon taje ta duƙa a nitse tace yaya Aryan shiru bai amsaba dataji shiru sai tamike ta zauna a gefen gadon tasa hannu tana bubbuga hannunsa tana kiran su nansa, shiru shiru bai amsaba baikumayi motsiba ganin hakan yasa, tasa hannunta tana kokarin buɗe idon'sa dakarfi " a zafafe ya damki hannun nata batare daya buɗe idon ba " aruɗe take kokarin kwache hannunta dan tagudu " slowly ya ware manya manya ash eyes ɗin nan nasa akan face ɗinta " sanye take chikin jallabiya baki still dai kanta ba ɗan kwali " a tsorace tasoma magana dan allah kayi hakuri allah bazan sakeba " kara daure fuska yayi sosai yafara Magana, meyakawoki ɗakin nan " Abba ne yace nakiraka tabashi amsa " jinjina kai yayi tare da mikewa zaune ya saki hannun nata, aiko kamar jira take yasaketa ta yunkura aguje zata sauƙa gadon " a zafafe Aryan ya damkoh gashin kanta ya jawota baya har saida tafaɗa kan chinyarsa " kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu da sauri ya rufe mata baki yana kallanta " girgiza masa kai tafarayi tana hawaye " calmly yafara magana wani uncle nakune yace yana sonki kuma dayace yanason naki mekikache masa yayi maganar tare da zame hannunsa daga bakinta dakuma rikon dayayiwa gashin kanta " chikin shesshekar kuka tace uncle Omar kuma ni bani yafaɗawaba Zahra ya faɗawa kuma ninache'wa Zahra tafaɗa masa soja nakeso soja zan aura " kara waro ido waje Aryan yayi yana kallanta yadda take magana a nitse yama rasa me zaiche mata " bayan tagama magana'ne " yace to tashimin a kafa" da sauri tamike tana kokarin sauka daga gadan " ai banchi ki sauka bakoh chewa nayi kitashimin a kafa kawai juyo nan ki kalleni kuma ki saurari abunda zan faɗamiki chewar Aryan " a hankali ta gyara zamanta a kan gadon san nan tajuyo tana fuskantarshi " Aryan yace sau'nawa yanzu inamiki magana a kan ɗan kwali eh, " shiru tayi kana ta sunkuyar da kai " meyasa bakyajin maganata meyasa kikesan ɓatamin raine eh " ɗago kai tayi ta ɗan kallesa taga ita yake kallo a hankali tace kayi hakuri zan rinka sawa " jinjina kai yayi yana faɗin to meyasama bakisan ɗan kwali ne " turo dan bakin nan nata tayi tana faɗin Allah yaya Aryan zafi nakeji idan nasa ɗan kwali gashinne yayi yawa shiyasafa nache ra nan ka askemin kaki " shiru yaɗanyi kafin nan yace Aunty amarya na falone " eh tana nan tabashi amsa " ok to tashi kije inazuwa chewar Aryan " da sauri tamike dan daman kamar a kan ƙaya take har takai bakin kofa kome tatuna saikuma tajuyo ta fashe da kuka" da mamaki Aryan ke kallonta" kuka take sosai gashi tana tsaye taki tafiya " alama yamata da hannu a kan tazo " ba musu tazo kusa da gadan ta duka tana kuka " meyafaru kuma meyasaki kuka Aryan ya tambayeta " chikin kuka tace innar yaya bello tafaɗamin idan nabari namiji yataba jikina to zansamu chiki shine kuma gashi kai kataba jikina " Aryan baima san sanda dariya ta kubche masaba " ganin yana mata dariya yasa tasake kara sautin kukan nata " shiru yayi yana kallan yadda take rera kuka tsakaninta da allah yama rasa me zai chemata kusan 10 tukun nan idea tazo masa, ya sa hannu ya ɗago habarta kasa kasa yace kidena kuka ni ai yayankine ko nataɓaki bazaki samu chikiba amma idan kikayiwa wani namiji magana ko kikabari yataba hannuki tabbas zaki samu chiki " da sauri tace to yanzu yaya Aryan bazan samu chikiba " eh bazaki samuba ai nafaɗamiki ni yayankine babu abunda zaki samu dan natabaki " mikewa tayi tana dariya kamar ba mai kuka yanzun nanba " zuba mata ido yayi yana kallanta chan kuma yace sannu mai kuka da dariya lokachi guda " hannutasa ta rufe fuska tajuya tanufi hanyar fita " binta yayi da kallo har tafiche wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke san nan
yamike yanufi toilet danyin wanka
A gurguje yayi wanka yafito yasa farar jallabiya yafito yanufi palan mai martaba " da sallam yashiga lokachin kuwa duk matasan sungama chin abinchinsu kowa ya watse sauran Ammi da Ummi sai mai martaba
Zama yayi tare da gaidasu " Ummi takira masu aiki sukazo suka zuba masa white rice an beans da steew yaji kaji sai wani ferfesu a É—ayan plate É—in suka tura masa gabansa " a nitse yafara chin abinchin " mikewa Ammi tayi tanawa Ummi da mai martaba sai dasafe " Ammi pls kifaÉ—awa yarinyar nan takawomin coffee dawuri dan inajin barchi chewar Aryan "to kawai Ammi tace san nan tafice

A bangarensu diyana kuwa zaune suke a ɗaki zahra da hiyana sunna karatun boko amrat na karatun qur'ani lamrat na buga game a wayar Zahra Aunty diyana kuwa tana zaune gaban mirriow, wai taga wani kwalli a wayar zahra zatayi irinsa sai faman pente pente takewa fuskarta " ba ƙarya tayi kyau sosai dan diyana daman akoi san kwalliya shiyasa ta dage takoyi kwalliya sosai awajen Zahra
Bayan tagama kwalliyar ne, tamike tanufi wajen kayansawarsu wani wandon jeans blue ta daukoh da t-shirt pink tanufi toilet jim kaɗan saigata ta fito wow bakaramin kyau tayiba ga wandon ya ɗan kamata shape nata yafito sosai yaukam tatara gashin kanta ta ɗaure a tsakiyar, high heel blue ta daukoh kalan wandon tasa a kafarta diyana akoi san high heel sosai " hiyana che ta ɗago tana kallanta kana tace diyana kwalliya da daddaren nan inazakije, gaba ɗaya su zahra ma suka ɗago suna kallanta " babu inda zanje kawai dai yau naji inasanyin kwalliyar darene " wow my diyana kinyi kyau sosai chewar Zahra " Allah aunty zahra to pls ki ɗaukeni hoto mai kyau a wayarki kinji " to zahra tace. San nan ta karɓi wayar daga hannun lamrat tafara yiwa diyana hotona " da sallama Ammi tashigo ɗakin tasamesu sai hoto Zahra ke ɗaukan diyana girgiza kai kawai Ammi tayi kana " tace ke diyana kije kikaiwa yayanku Aryan coffee yanzun nan " to kawai diyana tace Ammi kuma tayi waje tanufi betroom ɗinta " ya isa hotan haka Aunty zahra bari naje nakaiwa yaya Aryan coffee karna ɓata lokachi ya bugeni idanna dawo saiki kara ɗaukana wasu " to kawai zahra tache " juyawa diyana tayi tanufi hanyar fita hartakai bakin kofar fita saikuma ta juyo ta dawo ta daukoh dan karamin gyale pink tasa a kanta tafiche tanufi kichin " a gurguje ta haɗa coffee ɗin ta ɗaukoh tanufo bangaren Aryan
Chapter 33 · 0% Book details