← Book details Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 90

Sashe 53

Duk Karfin Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"jerowa Aryan da diyana sukayi kamar wasu taurari,sae taku suke a nitse diyana na kallan waya Aryan kuwa ya É—aure fuska yana kallan kasa sai da suka iso tsakiyar fada, Aryan ya juya yanufi wajen zaman su " da sauri diyana tace yaya Aryan wayan,kafa ta tambaya tana kallan'sa "baga É—aya jamar wajen ido kawai suka zuba musu "Aryan baiyi magana ba har sai daya kae wajen zaman'l su ya zauna kusa da Khalid san nan ya É—ago ya dubeta kije da wayar idan kingama kallan hoton sai ki kawomin,"mamakine yakama gaba É—aya family Abba musan man Aiman Aunty mardiya Aunty salma Umar haidar Ammi dakuma Ummi,
"Abba da Khalid da Yusuf kuma sae murmushi suke,"Aunty farida kam tafi kowa murna da hakan, "Aunty amarya na sanyin magana tana tsoran Abba gakuma taron jama'a kar aji kunya,Amma tachi al'washin yin maganin abun " Aunty Maryam kuwa kamar,zata mutu take ji dan bakin chiki,"kusa da Aunty farida diyana taje ta zauna tana faɗin Aunty farida ki kalla tayi maganar tana nunawa Aunty farida wayar Aryan,dake hannun'ta "ansar wayar Aunty farida tayi tafara kallan hotu nan, mamakine ya bayyana a kam face ɗin ta a hankali ta ɗago kae tana kallan inda Aryan ke zaune,"shima ita yake kallo, suna haɗa ido yama alama da ta kashe masa wayar kar tabari kowa yaga hotan, Jinjina kai kawai Aunty farida alamar to san nan ta kashe wayar ta sa chikin jakarta,"ta chiro wayar ta tamikawa diyana "da sauri diyana ta amsa tana murmushi tafara buga game " tunani Abba yashigayi ba hiyana ba DON anya lfy kuwa buɗe baki yayi zaiyi nagana sae ga DON yashigo shi kaɗai "taku yake irin na jaruman maza gaba ɗaya Jamaar wajen,sai kallansa suka dan yahaɗu sosai mazama burge'su yake bare mata, kusa da Aryan yaje ya zauna " gyaran murya Abba yayi ya dubi DON yafara magana Safras ina hiyana take " shiru DON yayi yana ɗan tunani wacece kuma hiyana,kodai wan nan yarinyar da aka aiko takirani " Abba ne ya katse masa tunani dachewa wai ba kai nake tambaya ba "da sauri yace tana ɗaki Abba yafaɗa yana turnuƙe fuska "gaba ɗaya idon kowa yadawo kansa "to meyasa kabarta a ɗakin Abba ya tambaya yana karewa DON kallo " akule yace suma tayi Abba zan zuba mata ruwa kuma na manta Fahad yaje ya'zuba mata ruwa yayi maganar yana nuna Fahad da hannu " a ruɗe Ammi tace me kamata tsorata kayi koh " ka daure fuska yayi yana faɗin tazo zata faɗine na riketa ta tsorata da yawane shiyasa ta suma, ya karisa maganar kamar zae fasa ihu dan haushi,a ransa yana chewa wlh badan iyayena,ke min wan nan tambayarba da bazanyi maganaba haba dan Allah ayita sa mutun magana, "Ammi zata sake magana,Abba ya ɗaga hannu alamar tayi shiru "mikewa Fahad yayi daniyar yaje ya zubawa hiyana ruwa "Abba yace kae Fahad dawo kayi zaman ka shi daya razana ta tasume shi zae farfaɗo da ita idan an gama taro sae kaje ka zuba mata ruwan yakarisa maganar yana nuna DON "wani kululun bakin chikine,ya tokarewa DON makoshi a ransa yake wae shin meyasa na tai'maki yarinyar nan ne, meyasa ban barta ta faɗi ta mutu kowa ya huta'ba wlh na tsani yarinyar jifa yadda Abba yake wani magana sae...bae karisa tunanin ba yajiyo muryan Abba na magana, gaba ɗaya fada tayi tsit kowa ya zubawa Abba ido yana jiran yaji wanene sarki

Ina mai farin chikin sanar da al'umma a yau ni Abubakar Khalid saraki zan sauka daga kujerar mulki na miƙawa ɗaya daga chikin ƴa'ƴana "asukwane DON Aryan Aiman Yusuf Fahad suka ɗago suna kallan Abba ido chikin ido suna jiran suji su nan wa zai kira gaba ɗayan su kirjin su sae dukan uku uku yake dukkan su kowa na adduar Allah yasa bashi,bane "Aunty amaraya kuwa sae murmushi take dan tasan abun dasuka kulla" Abba kuwa sake gyara murya yayi hankalinsa kwan che yachigaba da magana,a chikin ƴa'ƴan nawa bakowa bane face Ahmad "dam dam gaban Aunty amarya ya buga " DON da bai taɓa murmushi ba a rayuwar sa,yau sae daya saki wani cool murmushi "wani nauyayyar ajiyar zuchiya Aryan da Yusuf suka sauke a tare "Aiman kam har da faɗin alhlillah " nan take zufa yafara ketowa Aunty amarya"Aunty farida kuwa sai alhamllh munyi nasara take faɗi " zubur Ahmad yamiƙe zai yi magana, Abba ya watsa masa harara, bashi yakoma ya zauna "Abba yachi gaba dacewa " kubani hankalin ku ban gama magana ba ae,shiru sukayi suka saƙe nitsuwa yanzu ba sae anjima ba waziri kutashi ku naɗa Ahmad a matsayin sabon sarki,Abba nagama faɗin hakan yamiƙe nanfa jama'a suka fara hira masu murna sunayi masu,blach stomach sunayi, "jama'a suka fara turu ruwa wajen gaisawa dasu DON, "a kafara shigo da abin chiye chiye da shaye shaye

"sauri sauri gudu gudu Aunty amarya ta bar fada tanufi chikin gida ɓangaren ta tawuce tana shiga ɗaki tafashe da kuka mara sauti ta ɗaukoh wayar ta tana kuka tafara kiran layin sadiya,"bugu ɗaya sadiya ta ɗaga "chikin kuka Aunty amarya tafara magana sadiya mun shiga uku aikin gagarabadau baiyiba sadiya ba Aryan ko Aiman a kabawa sarautaba, Ahmad akabawa "dan Allah hajiya hajara kiyi shiru kidai na kukan nan,mubi komai a sannu,dan anbawa Ahmad sa rauta sae akache maki bazamu iyasawa a chan zashi bane,chewar hajj sadiya" Aunty amarya ta goge hawayen ta tana faɗin to dan Allah sadiya kikoma wajensa gobe inkinje ki tuna masa da batun aikin yaran nan kinji,dan suma yanzu sun fara wuche gona da iri a gidan nan,bakiga yadda samarin gidan nan suka fara shisshige musu bane har da Safras fa wai yanzuma ɗayar yarinyar tana ɗakin'sa ga shigiyar ɗayar kuma ta makalewa Aryan harda bata wayar sa gashi uban su shi ya ɗaure musu gindi yahana kowa magana a kan yaran takarisa maganar chikin ɓachin rai "kai, kai, abun har yakai haka to wlh dole mutsaya muyi maganin karki damu ae wan nan ni aka taba ba keba dan Safras na zulaihat che dole gobe zan tafi Enugu idan ma gagarabadau bazae iya aikin ba zan tsallaka niger dan ayi mana sha yanzu magani yanzu " to shike nan sadiya badamuwa bari naturo miki kuɗi yanzu batare data kira amsar Hajj sadiya ta katse kiran ta zauna a bakin gado tachi gaba da kukanta

Sai misalin karfe 1:30 a kagama taro jama'a suka fara watse'wa

diyana kuwa sae chin chocolate suke itada Zahra da amrat "lamrat kuwa tana zaune kusa da yaya Yusuf suna hira kamar wasu kawaye,hiyana kam har yanzu bata farfaÉ—o ba tana É—akin DON
Diyana ta É—aukoh wani carton na chocolate zata buÉ—e karaf idon ta ya sauka chikin na Aryan dake zaune kusa da Aunty farida suna hira, wani mugun kallo ya wurga mata da sauri ta ajiye chocolate É—in tana turo baki " diyana lfy kika ajiye chocolate É—in ki buÉ—e mana musha mana chewar Zahra "ni Aunty Zahra bana sha sai dai ku kusha tafaÉ—a tana kunbura kumatu "Aryan daga inda yake zaune bai san san da yayi murnushi ba dan yadda tayi maganar "
Daga bayansu sukaji a na faɗin, meyasa bazakisha ba yammata da sauri suka juya dan suga wanene wani hadadɗeb saurayine kyakkyawa mai chikar sura "lfy malam Zahra ta tambaya tana kallan face nashi "zama yayi a ɗaya daga chikin kujerun wajen yana faɗin lfy wajen sister ki nazo" wace sister nawa daga chiki Zahra ta tambaya "gata nan yayi maganar yana nuna diyana da hannu "ɗago fiska diyana tayi zatayi magana caraf suka haɗa ido da Aryan, " da mamaki diyana ke lallan yadda ya chanza lokachi guda ta shiga tunani wae Bayanzu naga yaya Aryan na ɗan murnushi ba to me aka masa kuma naga idon sa sun sauya sunyi jaa gashi yawani ɗaure fuska"Zahra che ta katse mata tunanin datake dachewa diyana ana miki magana "firgigit tayi tare da sake kallo inda Aryan yake sae taga bashi a wajen dawo da kallonta tayi kan saurayin,dake zaune gabanta "kallon shi tayi from head to toe a gatsale tace waye kai "ajiyar zuchiya ya sauƙe san nan yafara magana nidae sunana walid ni ɗane ga sarkin zaria,kuma maganar gaskiya son ki nake kuma so irin na aure ba wasaba " wani dariya diyana tayi kafin tace ni kake so amma dai baka da hankali koh to ni matar soja che sojan ma mai manya manyan bindigu "da sauri walid yamike yana faɗin kiyi hakuri wlh ni bansan ke matar aure bace "baki diyana ta taɓe tana mamakin kowaye yafa ɗa masa ni matar aure che daga chewa ni matar soja che to ae ban auri sojan ba tukun nan tayi nisa chikin tunani taji, Zahra na faɗin tashi muje chikin gd muyi wanka muyi sallah "Aunty Zahra wae har yanzu hiyana bata dawoba diyana ta tambaya tana kwaɓe fuska "eh bata dawo ba amma kar ki damu bakiji yaya prince yace tana ɗakin saba "mikewa diyana tayi jiki ba kwari suka nufi chikin gd
Chapter 53 · 0% Book details