← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 80

Sashe 9

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haka ne khausar yanzun abinda nake Ganin zai faru shine,fita ki kiramun yakubun mu tattauna dashi a tsakaninmu matukar akwai mafita Kuma zai rufa Mana asiri to ko nawane Zan salwantar Akan wanan shariar Dan Ganin cikar burinmu.....

*SLIMZY😍🥰* ✍🏻*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

08

"Yakubu banason a samu matsala Akan wanan aikin Dana saka ka tabbatar da kayi yadda nace baasamu matsala ba,banaso video din Nan ya fito complete idan akaje kotu"

Dan rankwafawa yakubu yayi yace "insha Allah zaayi yadda kikace ranki Shi dade,ai Dole abi umarninki ranki Shi Dade"

Wayarta ta Ciro ta Mika Masa "samun number ka a Nan sauran bayani zanyi maka aike"

"Nagode ranki ya Dade Allah ya Kara girma da arziki"

Ba tare da ta amsaba ta juya suka fice a office din,securities da dogarawa suka take musu baya har wajen motocinsu....

******
"Wanan manakisa ce babba ake Shirin shiryawa Dan anga yarinyar batada gata to wallahi karyane,wanan maganar ruwan kwando CE Babu yadda zaayi ace Ana rikon yaro a gidan marayu ace baasan da zamansa ba bayan dik wani yaro da rikonsa zai koma hannun gwamnati Sai an rubuta sunansa da komi da shekarar da aka kawosa da Wanda ya kawoshi wannan maganar banza ce barrister"

Girgiza Kai yarima yayi Sai yanzun hankalinsa ya Dan kwanta Jin wanan maganar daga bakin barrister Abdul"Ni kaina abin ya daure mun Kai domin Ni shaidane Akan zaman Fatima a gidan marayu saidai babu yadda zanyi in furta hakan tunda ga yadda shariar tazo bani nake kareta ba"

"Ai ka kwantar da hankalinka Dole ne a koma Ayi bincike tsattsaura Akan gidan marayun Nan domin idan haka ne akwai wata makarkashiya ai wanan abin da sukayi tamkar sun nunawa duniya cewa Suma maha'inta ne ,sanan Babu gaskiya a lamarin Babu Amana"

Sai yanzun yarima ya samu karfin gwiwa da kalaman Abdul,hankalinsa ya Dan kwanta yace "to yanzun barrister menene abun yi?me kake Ganin zaayi?"

"Ni da kaina zanje police station din,inyi magana da babban DPO din Akan Ni ban yarda da wanan binciken da akaje akayi ba a gidan marayu batare da dauko list din sunayen yaran dake gidan ba,ai a master list ne idan har baaga sunan Fatima da hotonta ba to shine zaa tabbatar da baa gidan marayu take ba wanan karon Dani zaaje saboda akwai binciken da nakeson yi a cikin gidan marayun"

Jinjina Kai yarima yayi cike da gamsuwa yace"yauwa barrister Abdul Dan Allah kayi kokari Akan wannan lamarin a duba al'amarin marainiyar Allah dik duniya Fatima batada kowa Sai Allah Sai Ni"

Kallonsa barrister Abdul yayi "ban gane inda maganarka ta dosa ba me kake nufi?"

"Marainiya ce kamar yadda kasani,sanan Kuma nine a matsayin gatanta na uwa da uba,sauran bayani zanyi maka Shi idan komi ya kwaranye,fatana be wuce a shiga wanan kotun da zaayi musamu cin nasara a wanan shariar"

Kalaman yarima ya daurewa barrister Kai Amma Sai ya share yace"Allah ya bamu nasara ranka ya Dade insha allahu Fatima zata kubuta"

Murmushi yayi yarima Wanda ya tsaya iya fuskarsa yace'abu na gaba shine yadda zaa Kara zantawa da Fatima Akan abinda ya faru Dan idan ban mantaba jibi ne zaa koma shiga kotu"

"Wanan ba matsala bace insha allahu,gobe da safe nakeson zuwa station din yin bincike bazan taba nunar musu da nasan cewa sunyi bincike Akan Fatima ba Yar gidan marayu bace zanyi musu tambayoyine inji me zasuce sanan in gabatar musu da bayanin da nayi maka yanzun,sanan madam zansa ta Kara neman izinin Ganin Fatima domin ta zanta da ita a Karo na biyu"

Mikawa barrister hannu yarima yayi suka gaisa hade da rike hannun nasa "nagode sosai barrister bansan da kalmar da zanyi amfani da itaba wajen nuna godiyata da jin dadina Akan wanan halarcin da kayimun nagode Allah ya saka da alheri"suka rungume juna....

*******
Ba karamin farin ciki mama babba tayi ba samun labarin da tayi Akan Fatima baasamu wani cikakken bayani ba akanta a gidan marayu,wanan kadai ya Kara kwantar Mata da hankali ta Kara tabbatar wa da kanta hakarta ta kusa cinma ruwa Dan da zarar aka shiga kotu ta tabbatar da lauyoyin da ke Kare Fatima Basu da wata hujjar data Kai tasu,domin dik hujjar da zasu gabatar a kotu alkali zaiyi watsi da ita ne....

Bayan yarima ya baro wajen barrister Abdul direct gida yayo hankalinsa ya Dan kwanta sanan yasamu kwarin gwiwa da maganganun barrister Abdul,babban tashin hankalinsa da damuwarsa be wuce Fatima ba Allah yasa tayi magana,ta Fadi abinda tasani tayi bayani.....

A dakin mama babba yayi matsuguni yau fuskarsa Babu yabo Babu fallasa ba kamar kullum ba da ka gansa kasan Yana cikin damuwa ita kanta fuskarta a sake take sanar Masa da bayanin da akayi Mata game da Fatima ba Yar gidan marayu bace"kaga kenan munada hujja kwakkwara da zamu gabatarwa da kotu ita batare da Anja wanan shariar ba zaa gamata,Kuma gaskiya zatayi halinta"

Murmushi kawai yarima yayi yace"to alhamdulillahi wanan labarin da nasamu bakaramin dadinsa naji ba yanzun abinda ya rage shine gabatarwa da kotu hoton video din yadda aka kashe Yaya habib"

Jinjina Kai tayi a tsayen da take tace"wanan ba matsala bace domin naje guest house din dazun Kuma na roki alfarmar a bamu aron recording din mu Mika kotu Dan tabbatar wa da duniya cewa kasheshi akayi batare da hakkinsa ba"

Da sauri ya kalli mama babba ,hmm lallai wanan matar bala'i CE wato har taje guest house ta aiwatar da abinda tayi niyya,kallon tuhuma ya bita dashi sanan ya kawar da kansa gefe daya cikin dabara ya kakalo murmushi saboda kawar da reaction din da yayi lokacin,Yana jinjina Kai Yana faraa yace"alhamdulillahi nasara Tana garemu"

Itama murmushin tayi tace "insha allahu"

Dan waigawa yayi kadan yace "Ina su khausar ne?"

"Sun shiga garden Wai sun gaji da Zama wuri daya shine akayi musu rankiya don su Sha iska"

"Ok"shine abinda yace kawai yayi Mata sallama ya bar sasanta,

Sasan mahaifiyarsa ya shiga Tana zaune ta da'n ki shingida gefenta bayi ne guda biyu daya Tana matsa Mata kafa,daya Tana bare Mata fruits,

Zubewa yayi a kasa ya kawo gaisuwa,murmushi tayi Tana kallon da'n nata cike da so da kauna ta amsa,

"Yarima yadai? Yau Naga fuskarka a sake da alamu kana cikin nishadi"

Kasa da kansa yayi hade da murmushi yace"ehh mama nafara samun kwanciyar hankali ne,saboda da alamu zamuyi nasara a wanan shariar Allah zai bayyana Mai gaskiya"

Jinjina Kai kawai tayi hade da murmushi sanan tace "Allah yasa"

"Ameen,Ni Zan shiga bangarena"

"Kafin Nan Mai martaba yanason zantawa dakai,dazu ya sanarmun da hakan domin tafiya ta kamashi da gaggawa Amma dai Ina Ganin ba dadewa zaiyi ba bazai wuce sati da'ya ba"

"To Zan shiga wajensa insha allahu,ki huta lafiya"

"Allah yayi albarka"

"Ameen"ya Mike ya fice....

*******
Washe gari kamar yadda barrister yayiwa yarima alkawarin zuwa police station hakan kuwa akayi,shiryawa yayi tsab shida madam dinsa suka nufi police station din,

Gabatar da kansu sukayi sanan suka bukaci Ganin DPO din wajen,sanin kosu din su waye yasa akayi musu iso zuwa office din DPO

Bayan sun gaisa ne barrister Abdul ya bukaci Jin ko sunje gidan marayu sunyi bincike Akan yarinyar?

Cike da gamsuwa DPO ya yiwa barrister bayanin yadda bin ciken ya kasance da ya tura jamian tsaro sanan an tabbatar musu da baa gidan marayu take da zamaba,

Murmushi barrister Abdul yayi yace"ranka ya Dade kada kace nayi maka katsalandan akan aikinka,Amma sorry to say gaskiya ba haka ake bincike ba"

Kallonsa DPO yayi ta cikin glass Yana mamaki,

"Ehh saboda a sharia babu inda akace idan anje bincike gidan marayu,maaikata zaabi a bincika sanan a bincika yara Ana yawo da hoton yarinya,meye amfanin registarer na gidan da ba zaa bincikeshi ba Akan sanin yarinyar?inace ko wani gidan marayu dake cikin jahohin Nan kafin rikon yaro ya koma hannun gwamnati Sai an yi mishi register da gwamnati?da hotonsa da Wanda ya kawosa sanan da shekarar da aka kawosa da sa hannun Wanda ya kawota da sa hannun gwamnati cewa ta amsa,dik bakubi wannan matakan ba kawai akaje akayi bincike a sama akace Wai baasanta ba,to gaskiya bincikenku beyi ba Dole a sakeshi,Dan abinda ya kawoni kenan inji ko kunyi bincike don insamu abinda zan rubuta in mikawa kotu"

Shi kansa DPO din ya gamsu da bayanin barrister abdul Dan tabbas wanan shine binciken kwarai,gyara glass din idonsa yayi yace "to yanzun barrister menene bukatarka?"

Gyara Zama barrister Abdul yayi yace"yanzun inaso a hadani da Yan sanda kamar mutum hudu Dan komawa gidan marayu mu gudanar da binciken ainihi ba irin Wanda sukayiba Dan ba bin cike bane"

Jinjina Kai DPO yayi ya Danna kararrawa saiga wani Dan sanda ya shigo ya Sara masa, DPO yace "a shirya mota yanzun Dan zaa koma gidan marayu tare da barrister Dan gudanar da bincike a Karo na biyu"

Sara masa yakarayi yace "yes sir"ya fice ,

Barrister Abdul ya Mika Masa hannu suka gaisa sanan suka fito shida barrister hauwa,

Yan sanda hudu suka shirya kansu a motarsu yayinda barrister Abdul da matarsa suke tasu motar suna biye dasu har gidan marayun.....

Koda suka Isa basusha wahala ba wajen isar dasu office din manager n gidan gaba daya Wanda hade suke da registerer na gidan marayun,

Barrister ne ya gabatar da kanshi sanan sauran Yan sanda kowa ya gabatar da kanshi da abinda sukazo yi,

Nan da Nan sukayi naam da bukatarsu aka shiga bincike file by file na yaran dake gidan,ko wace shekara da files din dinta,a haka har akazo shekarar 1999 aka Fara bude sunaye da hotuna anyi file na hudu a na biyar saiga hoton Fatima Zahra a jiki da sunanta rad'a rad'a FATIMA ZAHRA.... Nan aka bude file dinta aka tabbatar da tabbas a gidan marayu take da Zama sanan ga hotonta Nan kamaninta tun na yarinta Babu abinda ya canja.....

Hajiya ce zaune a jikin bishiya a kofar kitchen Tana Shan iska gefenta maaikatan kitchen ne duk suna zagaye da ita,kallon wadda ke gefenta na dama tayi tace"Wai nikam uwaliya tun dazun nake hangen motar Yan sanda da wata karamar mota a office din oga Wai meke faruwa ne"
Chapter 9 · 0% Book details