← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 80

Sashe 17

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kallon inda take beyiba yace"bana bukata".....Dan Jim tayi sanan ta juya ta fice a parlorn.....wata matashiyar budurwa dake zaune a gefe itama ta Mike tabi bayanta,

Shiru ne ya biyo baya sanan gwaggo rahi tace"ni zan shiga daga ciki tunda bakada wata magana Mai muhimmanci".....itama ta Mike Tana takama tabar parlorn....

Ya Dade zaune sanan ya Mike jiki babu kwari ya fice ya nufi motarsa ya tada a guje ya figi motarsa yabar gidan.....

********
Zagaye dakin kawai gwaggo rahi takeyi Tana huci deejah ma ta kalli mahaifiyar Tata tace"ni wallahi mama dama hankalina yafi daukuwa Akan Yaya Kabir dama na aminta da zancen auren Yaya habib ne saboda kince shine zai hau karagar mulki Kuma bukatarki na auri Wanda shine zai hau gadon mulki Amma zuciyata tafi kaunar Yaya Kabir Domin yafi Yaya habib haduwa"

"Ke dalla tafican maganar haduwa ake ko maganar Wanda zai hau gadon mulki?waya fada miki cewa sarautar barayar Zaki karamar sarauta ce?dik fadin kasar Nan babu masarautar da takai masarautar barayar Zaki mulki cikar mulki da sarauta dik wata mace zataso hada zuria da wanan sarautar,shiyasa banaso wani a cikinsu ya fita waje ya samo Mata nafiso ya samu a cikin gida tunda gaku,a cikin gidanma nafison yasamu a cikin yayan cikina kuda kuke jini daya"

Jinjina Kai deejamah tayi hade da sauke lallausan murmushi sanan tace"mama ni dama zai aureni ya dauko tsintacciyar magen ya kawota in maidata baiwa kaskantacciya"

"Ya aureki?ya kawo tsintacciyar mage?tabiyo dare ta kasheki?aikoda kikaji Ina wanan banm bamin inayi ne donke bawai don wani abuba Dan nasan babu makawa shine zai maye gurbin habibu a wajenki Dan nasan Shirin da nakeyi saboda haka kidaina mafarkin ya dauko wata kazanta ya kawota gidan sarauta"

Murmushi deejamah tayi sanan tace"nayi mamaki yadda kika fututtuke da Yaya yazo da bukatarsa saboda nasan dik masarautar Nan kece mutuniyarsa kece dik abinda yakeso kike Mara Masa baya Amma wanan karon Naga Nan da Nan kin rufesa da fada"

Murmushi kawai gwaggo rahi tayi batare da tace uffan ba.....

*********
Koda yarima yabar gidan gwaggo rahi bai zarce ko inaba sai gidan barrister Abdul inda ya tarada Fatima ta shirya tsaf tayi kyau abinta kamar ba itaba tanata kallon tv kallonta yayi tausayinta na ratsa sassan jikinsa,

Dik Wanda ya kallesa yasan Yana cikin damuwa Nan barrister Abdul ke tambayarsa abinda ke faruwa be boye musu komiba ya Basu labarin rikicin da akeyi Akan daukaka Kara.....

Kuka sosai Fatima takeyi harda shassheka cikin kukan take fadin "Kai cona ni Fatima,meke Shirin faruwa Dani?inama baayiniba a cikin wanna duniyar Mai cike da darrusa marasa Dadi babbar kaddara ta fadomin wadda a sanadin maraici hakan ya sameni inda inada iyayena bazasu wofintar Dani haka,bazasu barni infada cikin mummunan Hali hakaba har in aikata abinda zaisa farin ciki yayi kaura a zuciyata,na shiga ukuna.....Yaya yarima kabari kawai akaini a kasheni ka huta Nima in huta da wanan masifar"

Tunda tafara magana ya kafeta da idanuwa zuciyarsa na harbawa sauri da sauri ji yakeyi tamkar ya rungumeta a jikinsa ko zaiji sanyi.....

Saukowa yayi daga saman kujera ya matso inda take a durkushe Tana faman rizgat kuka,Dan towel ya Ciro a aljihunsa fari Kal yasa Yana share Mata hawaye Yana fadin "ki kwantar da hankalinki ko duniya zata juya Miki baya ni kabiru bazan juyawa Fatima bayaba,sanan wanan shariar da zaayi Dani zaayita nine zan tsaya Miki babu gudu babu ja da baya"

Zumbur ta Mike Tana girgiza Kai tanaja da baya Tana fadin"banaso ka jefa kanka cikin matsala Yaya yarima ,akaina bazan Zama sanadiyyar wargaza zamantakewar rayuwarka da iyayenka ba ka kyaleni kawai akaini a yankemun hukuncin daya Dace dani a matsayina na wadda tayi kisan Kai"Tana Gama fadin haka ta shige daki da gudu Tana kuka Mai tsuma zuciya......

Shi kansa baisan lokacinda hawaye suka fara zuba a idanuwansa ba yayinda yabi bayanta da kallo harta shige.....

Girgiza Kai kawai barrister hauwa keyi cikin al'ajabi da tausayi tace"ranka ya dade ka kwantar da hankalinka,kuka ba naka bane jajircewa zakayi ka kwatarwa marainiya yancinta tunda ka yarda ka amince Kaine gatanta to Allah ya Zama gatanta kaima ka Zama gatan nata Amma ba kuka zakayiba"

Dafa kafadarsa barridter Abdul yayi Yana bubbugawa yace"be A man Mana prince wanan ba abin tada hankali bane I am sure zakayi winning saboda haka ka kwantar da hankalinka yaki ne a gabanka ba kuka ba"

Hannu yasa ya goge hawayensa sanan yace"nagode sosai da karamcinku a gareni Dan Allah ku cigaba da ajiyemun Fatima a wajenku zuwa mu Gama wannan shariar da zamu fara"

Jinjina Kai barrister hauwa tayi tace"kafi karfin komi ranka ya dade"

"Nagode"....

*******
"Barrister ninasa a kiraka saboda na daukaka Kara inaso abiwa Dana hakkinsa zan biyaka ko nawane ka bajemun basirarka a kotu ka tabbatar da an yankewa wanan shedaniyar yarinyar kisan gilla kamar yadda tayiwa Dana kisan gilla"

Jinjina Kai Wanda aka Kira da barrister yayi yace"insha Allahu ranki ya dade zaayi yadda kikeso"

"Ko nawane zan biya Domin Inga bayan wanan shariar barrister ,ko dukiyata zata Kare wallahi sainaga bayan shariar Nan"

Dan rankwafawa barrister yayi yace"angama ranki ya dade dik wani abinda ya Dace ayi anyi ranki ya dade takaddar sammacin ma yanzun haka an rubutata ranki ya dade jibi zaa fara shiga kotun"

Jinjina Kai mama babba tayi cike da gamsuwa tace"nagode barrister "

"Nagode Allah ya baki yawan Rai"

********

Afnan ce fuskarta babu walwala tace"mama ya kamata ki Kira yaayah kiji inda yaje"

"Nakira wayarsa a kashe Amma dik inda yake dole ya kwana a gida sanan dole in sanar Masa da inhar ya kuskura ya shiga shariar Nan to ban yafe Masa ba.......

*Muje zuwa*🏃🏻‍♀

*SLIMZY🥰✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

15

Yana shigowa gidan direct dakin hajiya babba ya shiga da jiki a sanyaye ya yi sallama,ciki ciki ta amsa Masa Tana zaune Tana kada kafafuwa fuskarta babu annuri tamkar Bata taba dariya ba,

Gefen makekiyar daddumar dake dakin ya nemi waje ya zauna ya tankwashe kafafuwansa hade da sunkuyar da kansa....

Kallon gefen da yake zaune tayi a fakaice sanan ta tabe baki tace"kazo ne yau ma ka zazzagamun masifar da kayimun saboda marainiyar Allah kamar yadda kake fada?.....Kabir kenan ka bani mamaki ka nunamin iyawata dik tunkaho da nakeyi da Kai ka dibi kasa ka watsamun ka kasa bani goyon baya Akan kudirina"

Dago fuskarsa yayi wanan karon idanuwansa sun kada sunyi jajir cikin sassanyar murya yace"ki gafarceni mama wallahi tallahi ba goyon bayan Fatima nakeyiba don Tana marainiyar Allah,ba ita kadai nakewa wanan yakin ba harda Dan uwana,ki duba kiga ta hanyar ya mutu,sanan ki tunada cewa shariar Nan da akayita tunda aka farata babu wata maaikata ta tv kota gidan radio da aka Bari ta dauki wannan shariar tasa a kafafen yada labarai saboda gudun tozarci da bacin suna,na tabbatar da cewa ranan da aka kammala shariar Nan da mun kuskura wata maaikata ta yada labarai ta dauka da mune zamuji kunya,sanan mune sunan mu zai lalace a idon duniya,aga cewa babban Dan siyasa kamar Yaya habib Kuma babban Dan sarki Mai jiran gado shine yake neman aikata mummunan aiki ba karamin surutu zamuji ba a cikin gari.....ko a cikin masarautar Nan ba kowa yasan abinda ya faruba saboda gudun tsegumi da Cece kuce irin na mutane Dan Allah mama na rokeki ki janye Akan daukaka karar Nan"....

Shiru tayi Tana sauraronsa har ya Gama magana tamkar wadda ruwa ya cinye,tafi minti goma a haka har ya fidda ran zatace wani Abu sanan tace"dik wadanan maganganun da kakeyi kake rara gefe basu ne zasusa in janye kudirina Akan abinda nayi niyya ba wani surutun mutane da bacin suna baya gabana babban burina shine dik wani Mai ruwa da tsaki da yayi amfani da wanan yarinyar taje har aka kasheshi to idan taji wuya zata fito dashi Dan ni ban yarda da wadanan maganganun ba na yazo lalatatane ta kasheshi kawaidai abinda nasani abiwa Dana hakkin jininsa"

Gauron numfashi ya sauke yace"to shikenan ni Kuma insha Allahu zanyi iya bakin kokarina wajen marawa yarinyar baya a shariar zanyi amfani da basirata da kwarewata a wanan shariar wajen kwatarwa Mai gaskiya hakkinsa"

Murmushi hajiya babba tayi tace"kamar yadda kake takama da gwamnati tasan da zamanka da kwarewarka da basirarka haka akwai wadanda suna zaunene zaman kansu sunayi don kudi da dukiya,zanyi hayar lawyoyi wadanda zasu fafata dakai,sanan dik wanan takamar da kakeyi zasu baka Kashi a wanan shariar sanan duniya datasan da zamanka tasan da kwarewarka a shariah wanan karon zaaga kasawarka ai Mai laya kiyayi Mai zamani"

Dariya maganarta ta bashi don Harga Allah bezo akan suyi sainsa ba yazone ya fada Mata ainihin manufarsa Akan na rashinso a daukaka Kara Amma ta bullo Masa da haka dariya kadan yayi yace "hajiya dik wani lauya da ya kwana ya tashi a fadin Nigeria yasan da zamana,Kuma babu Wanda yake fatan shariah ta hadani dashi Dan babu Wanda baisan kwarewar da Allah ya baniba alhamdulillah Koda wannan nasan nayi zarra Allah ubangiji yaga zuciyata Akan wanan Abu da ke Shirin tunkarowa insha Allahu bazanji kunyaba idan an rubuta takaddar daukaka karar da sammaci akawomin Domin nine gatan Fatima a yanzu"......

Jinjina Kai tayi batare da tace komiba zuciyarta tafarfasa takeyi tamkar zata Huda kirjinta ta fito ji takeyi inama ace Kabir shine zai bugi kirji ya tsaya a supreme Court da tasan tabbas babu makawa sukeda nasara Dan ita kanta tasan yaron mayene be taba tsayawa a shariah an kadashiba har hayarsa akeyi daga wurare da dama tasan da wuya tasamu Wanda yakai Kabir basira da kwarewa wajen shariah Amma zatayi amfani da kudi tasan babu abinda kudi basayi.....

Tayi Nisa cikin tunani dik ta dauka ya fuce saida ta bude idanuwanta daga kishigiden da take ta gansa a zaune ta ce cikin sarkakkiyar murya "ka tashi ka ficemun"......

Mikewa yayi ya fice a dakin ya nufi dakin mahaifiyarsa......
Chapter 17 · 0% Book details