← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 80

Sashe 57

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zabura hajiya babba tayi tai Kan yarima ta cakumo malum malum dinta bakinta har rawa yakeyi "wallahi saika saki Fatima baka isaba kabiru nagaji da wanan cin Kashi da cin fuska da akemun uban waye yace kasa a daura ma aure da tsintacciyar mage?wanan auren be dauruba wallahi Dole a kwanceshi"....ta shiga jijjiga yarima tamkar wadda ta zare a guje tayi cikin dakinta ta dauko mayafinta ta yafa ta fito kafa babu takalmi ta nufi hanyar fita Tana fadin "wajen Mai martaba zani wanan munafurcin da aka kulla Dole a kwance shi Dan aga bayana anyi haka ne a nunawa duniya cewa kabiru shine Dan gata Dan so,an mance da shegiyar yarinyar itace tayi silar mutuwar dana daya tilo,....nayi hakuri dikda abubuwan da yaron Nan yakemun Dan ya bakantamin Rai Amma yau Dan a nuna Mana iyakarmu shine aka Mana wanan tozarci"

Hajiya karama wadda ta fito sanye da lafaya Mai shegen kyau kqlar ja,itace ta rike hajiya babba Tana fadin "karkice zakije fada Akan wanan abinda Allah ya Riga ya kaddara kekinsan bamu Isa mujada hukuncin Mai martaba ba"

Hankade hajiya karama tayi "karki kuskura kice Zaki gayamun maganar banaza Samira dan na Dade da sanin ke muna fuka ce kece kika kulla komi saboda anga banida da banida sauran gata banida da namiji shiyasa ake wulakantani a idon duniya"kawai sai hajiya babba ta rushe da kuka Tana fadin "wallahi koni ko ku a cikin gidan Nan"

"Dakata safiya ba inda zakije karma kice Zaki bangaren Mai martaba Akan wanan maganar sakarmun yata kawai zaiyi"

Yarima Wanda ke tsaye kamar an dasashi sai a sanan ya samu damar magana"mahaifina be bani damar sakin ko wace mace ba ya mun umarni da dik macen Dana aureta to na aureta ne sai mutuwa"

Hajiya rahina dakyar take Tako kafafuwanta wadanda sukai Mata nauyi ta kasaro gaban yarima tana binsa da kallo Tana zagayesa "lallai ka cika Kai babban munafukine shiyasa kukai munafurcin da Saida aka yantata daga baiwa kaida hajiya zainab ko?to mu zuba wallahi summa tallahi saika gwammaci kida da karatu daga Kai har matsoraciyar yarinyar Kuma kasani ya'ta Yar halak ce ba shegiyaba alhamdulillah kowa yasan Yar asalice Dan haka Allah ya bada zaman lafiya kabiru Amma zakayi danasani"

Juyawa hajiya rahina tayi taja hannun galadima kafarta ko takalmi Babu suka fice daga parlorn sukai waje,

Fitarsu yayi daidai da faduwar deejahmah kasa sumammiya,a guje jamaaar gidan sukai kanta harda yarima Wanda ya cire malum malum dinsa yayi jifa da ita ya ciccibeta yayi waje da ita,bangarensa ya nufa da ita....

*********

Tunda ta daga Kai ta duba agogo taga karfe goma na safe ta tabbatar da an daura auren yarima da deejahma kifa Kai tayi a Kan pillow ta shiga kuka Mai cin Rai Wanda batasan dalilinsa ba,hajiya zainab ta Dade da shigowa dakin tai tsaye ta rike kugunta Tana kallon Fatima wadda ke kuka kamar wadda akayiwa mutuwa,murmushi tayi a hankali ta taka har wajen gadon ta dafa kafadar Fatima ta furta a hankali "kuka ya Kare diyata kin samu yanci a yau din Nan,tashi ki share hawayenki alkawarin Allah ya cika kedin dai da baaso kece uwar gida a wajen kabiru Domin aurenki aka fara daurawa kafin na Khadija"

Cakkk Fatima ta tsaya da kuka gabanta ya tsananta faduwa,dakyar ta yunkura ta Mike a hankali ta zauna fuskarta sharkaf da hawaye ta kafe hajiya zainab da idanuwa ko kiftawa batayi,

Dariya sosai ummu tayi "kiyi Shiru ki share hawayenki zakaran da Allah ya nufa da cara ko Ana muzuru Ana shaho sai yayi Fatima Allah ya daukaka daarajarki burina ya cika don nayi abinda nasan harabada safiya bazata mance da wanan bakin ciki ba kedin dai kece uwar gida Kuma matar so"

Rungume hajiya zainab Fatima tayi Tana kuka Tana dariya lokaci daya,....ita kanta hajiya zainab din dariya takeyi Tana bubbuga bayan Fatima...

Dago Fatima tayi tana dubanta Tana murmushi,take kunya ta lullube Fatima ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta....

"Bude idanuwanki bakida wadda tafini nice uwarki nice ubanki Fatima sanan inaji a jikina kedin wata ce inaji a jikina iyayenki zasu bayyana kinji"

Bude idanuwa tayi sababbin hawaye na sauka a idonta "ummu nacire Rai da ganin iyayena,zuciyata tafara mantawa da zancen iyayena tunda nasameki a matsayin uwa....nayi babban dace"

Share Mata hawaye tayi ta mike tsaye ta fice dakinta,Jim kadan ta shigo da alkyabba baka Mai aikin golden colour Mai shegen kyau da tsada...ta karaso "taso kisa in kaiki fadar sarki sanan daganan mu shiga cikin gida koh"

Gabanta ne ya fadi ta shiga girgiza Kai data tunada babban bala'i dake tunkarosu baki na rawa tace "ummu muje wajen Mai martaba kawai mudawo"

"Tsoro ba naki bane Fatima dakewa zakiyi muje Mai martaba yasa Miki albarka mu shiga cikin gidan Kai tsaye gidan mijinki ne yanzun Babu shegiyar data Isa ta takaki Dan haka karki kuskura kibari suyi galaba akanki lokaci yayi da zanbaki dama ki Rama abinda dik akai Miki na karbar Miki yancinki na huce Miki takaici sauran yakin zan koma Baya ingani Yar tawa jaruma ce?"....

Dago idanuwa tayi ta saukesu Akan ummu sai ta sunkuyar da kanta kasa Tana murmushi....

Canja Kaya tayi daga kayan dake jikinta xuwa hadaddiyar Riiga baka Mai shegen khyau ummu ta Bata ita kyauta daga saudiyya ta siyota,Saida tasa Mata ita sannan ta Dora Mata alkyabba wayyoo zokuga yadda alkyabba ta fito da Fatima tamkar Yar larabawa ta ummu da kanta ta gyara Mata fuska sanan suka fito gidan direct fadar sarki suka nufa....

Saida jakadiyya tayi musu iso sanan suka shiga,....har gaban sarki ummu ta zube ta kwashi gaisuwa dubban jamaa dake cikin fadar kowa sai Allah ya sanya alheri yakeyi fuskar hajiya zainab sai faraa takeyi....

A gaban Mai martaba ta ajiye Fatima wadda ta gaidashi cike da girmamawa ya amsa fuskarsa dauke da faraa Nan ya shiga yi Mata nasiha wadda batasan lokacinda hawaye ke gudu a idanuwanta ba....yasa Mata albarka sanan cikin jamaa ya shaidawa dik wani Wanda yake fadar yabawa Fatima kujerar makka da dawakai dari da rakuma dari da shanu dari sanan da kujera uku extra ta wadanda zasu rakata aikin hajji...da kyautar motoci uku Wanda natane mallakinta Dasu zata rinka fita Kuma ya Bata bayi goma masu kulawa da ita a matsayinta na uwargidan dansa daya tilo....kabbara ce kawai jamaa keyi a wajen

Shesshekar kuka kawai Fatima takeyi Tana sauke ajiyar zuciya ganin komi takeyi tamkar a mafarki...yau itace keda wadanan niimomin gabaki daya?...godiya sosai ummu tayiwa Mai martaba harda Fatima wadda kalmomin godiya da tayi amfani dasu gani takeyi tamkar sunyi kadan....haka kawai Mai martaba ya kasa dauke idanuwansa daga gareta ya rasa dalilin dayasa yarinyar ta shiga ransa ga fuskarta da takeyi Masa gizo lokuta da dama...

Sallama Sukai da fada suka nufo hanyar cikin gida....dakyar Fatima ke taka kafafuwanta a haka har suka Isa...

*********

Da sallamarsu suka shigo cikin gidan inda kallo ya koma sama,jamaa sai tururuwar fitowa sukeyi Dan suyi kallo dik Wanda ya Dora idonsa Akan Fatima sai yace Masha Allahu saboda wani irin annuri na kyau da kwarjini dake fita a fuskarta,

Dakin hajiya karama suka nufa inda maroka Mata Suka shiga wasa Fatima suna yi Mata kirari....faraa sosai Yan uwan hajiya karama suka shigayi suna fadin "Masha Allahu tubarkalla Allah ubangiji ya bada zaman lafiya Allah yasa ace gara da akayi,lallai yarinya kin shigo gidan sarauta da kafar dama hakika kin Zama tauraruwa wadda ke haska masarautar barayar Zaki da kewaye Allah ubangiji ya sa albarka"

A gaban hajiya karama Fatima ta tsugunna ta sunkuyar da kanta kasa,...kallonta hajiya karama takeyi Tana murmushi ta dago hannunta ta Dora akanta Tana shafawa "Allah yayi Miki albarka Fatima Allah ubangiji yasa alkhairi a zamanki da danmu kinji?ikon Allah sai kallo dik abinda Allah ya kaddara mu bamu Isa mujada ikonsa ba saboda haka Ina farin ciki da kika kasance daya daga cikin surukaina"

Murmushi kawai Fatima takeyi kanta a kasa batare da ta dago ba....

Sautin muryar hajiya babba yasa dakin yin tsit tun daga parlor kafin ta karaso take zazzaga balai "ayyiriri shegiya Mara uba itace surukar Mai martaba itace matar sabon sarki Mai jiran gado,...lallai wanan Abu yayi Amma is a tarihi ban tabajin wanan kwado ba ace Dan sarki ya auri shegiya Yar kwararo...wadda akai cikinta a titi iyayenta suka wofintar da ita...to meye sunan jikokin da Zata haifawa sarki? Shegu?"ta kece da wata iriyar dariyar rashin mutunci,

Mikewa hajiya zainab tayi 'ke safiya ki Kama girmanki Domin Ina ganin mutuncinki a matsayinki na matar yayana yau da bakida wanan matsayi Dana kaskantar dake a idon duniya"

"Zainabu kenan lallai kin cika kin aiwatar da mugun nufinki sanan kin shammacemu a wanan wasan saidai ki gyarawa shegiyar yarki waje Domin sati daya kacal na baki zai sakota Dan bata Isa tazo gidan sarauta a matsayinta na shegiya tayi kishi da yar asaliba sanan Kuma shekara ta zagayo tace zata haihu baa gidan Nan ba"

Murmushin mugunta ummu tayi "burina ya cika na tabbatar da na shammaceku Dan na kulla muku abinda har ku mutu bazaku manta ba,kamar yadda Fatima ta auri kabiru cikin sauki Aka kawo muku albishir na aure haka zaa kawo muku albishir na ta Haifa muku jikoki"

"Fatima bazata taba Haifa Mana jikoki cikin gidaba Dan bazamu hada jini da shegiya ba,..Kuma min rigada munsan kece kika hada komi batare da son kabiru ba saboda haka nabaki dama wanan karon Amma Ina gargadinki da karki Bari mu hadu a wasa na gaba Dan zakisha Kashi....yaro Yana can daki tare da matarsa Yana jinyar ta"

Saida gaban Fatima ya fadi Amma saita danne kawai ta gyara zamanta a gaban mahaifiyar yarima....

Kanwar kakar yarima ce dattijuwa tayiwa ummu tsawa Akan Subar wanan fadan da sukeyi tonawa kansu asiri sukeyi cikin mutane....ummu batace komiba tai shiru yayinda hajiya babba ta shiga zazzaga balai...tagaji ta fuce a dakin...

*********
Koda deejahmah ta farfado ta ganta a dakin yarima Yana gefen gado ya zabga tagumi Ahmad na gefe shima fuskarsa dauke da alhini sai kawai ta fashe da kuka Tana fadin "ka cuceni Allah ya Isa tsakanina da Kai Kuma wallahi bazan zauna a gidanka ba matukar da wanan karuwar zaka zauna"
Chapter 57 · 0% Book details