← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 80

Sashe 59

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai baza idanuwa yarima yakeyi yaga Fatima Amma shiru be gantaba,haushinta ne ya lullubesa ya Gama fahintar inda yarinyar Nan ta dosa Amma zai koya Mata hankali,. Be Gama Shan mamaki ba Saida yaga ummu a wajen walima da kowa na wajen Amma babu Fatima Babu dalilinta,...dikda irin fushin da yakeyi da ita hakan besa ya daina tunaninta ba,Rabon da ya ganta tun ranan dinner dinsu shima basuyi magana ba ko a wani Hali take ciki oho....

A daidai kunnensa ummu tazo ta rada Masa "zan sanarwa da iyayen deejahmah daga Nan akai amarya dakinta kawai tunda yamma tayi sanan jamaa sun fara tafiya gidajensu"....kallo ya bita dashi Yana so ya tambayeta ita Fatima fa?Amma sai ya kasa kawai ya maida kansa kasa batare da yace komiba,

Deejahmah dake gefensa sai kallonsa takeyi ta gefen idonta,ta kasa dauke kanta daga gareshi haka kawai takasa daina kallonsa yayi Mata matukar kyau da kwarjini...

Har inda su hajiya babba suke zaune suna tsaigumin baazo da Fatima wajen walima ba gudun kunya ace Dan sarki ya auri shegiya yasa aka kulleta a gida,to sun rigada sun Dana tarko Akan daga wajen idan andau deejahmah a mota ayi can cikin gida inda akai musu gini....

Sallama hajiya zainab tayi Amma babu Wanda ya ansa Mata sai rahina....wadda itama tsoron kada Mai martaba yaji labarin halin da suke ciki takeyi yasa ta amsa,

"Nazo ne in shaida muku maganar Kai amare gidajensu inaga zai kyautu idan an tashi Nan sai muje a kaisu ko?"....yatsina fuska rahina tayi sanan tace"umm"...ummu ta juya abinta cikin jamaa suka bita da harara,

Zare jikinta ummu tayi ta koma gidanta inda dama ta Gama shirya komi tunda dama ta rigada ta kaiwa Mai martaba ita yayi Mata fada,

Can ta dibi tawagar Yan rakiya ciki harda jakadiyyar sarki da babbar kawar ummu wadda tazo Mata biki,..ummu tasa motoci sukai layi a kofar gidanta sanan bayi Suka fara fitowa sanan ummu da aminiyarta sai Fatima wadda ke tsakiyarsu suna rike da hannunta,wadda gaba daya komi ganinsa takeyi tamkar a mafarki haka ummu tasata a mota saura suka hahhau tasu akaja su zuwa gidan amarya,

Farin ciki ne ya lullube ummu ganin burinta ya cika na sharewa marainiyar Allah hawaye,....gida ne tsararre ginin zamani Mai sashi hudu a ko wanne sama da kasa ne,...gate guda daya ne na shiga gidan Wanda shine ainihin main entrance na shiga ,....rike hannunta ummu tayi suka nufi sashen gate din gidan,... maaikata da dogarawa gidan suna ganin zuwansu suka bude musu gate din gidan hade da zubewa kasa suna kawo gaisuwa,

Addua ummu tabawa Fatima umarnin yi kamar yarda al'adar malam bahaushe take anaso ko wace amarya idan ankaita gidanta tayi addua hade da Bismillah ta shiga da kafar dama..haka Fatima tayi sanan suka shiga cikin gidan Wanda harabar gidan kansa abin kallo ne tamkar baa kasar hausa ba haka ummu tayi musu jagora har sashen da ta zabawa Fatima Dan dama tazo gidan taga komi.....

Sama suka hau da ita inda Nan ne dakunan kwanan bangarenta suke,

Wani daki ummu ta bude suka shiga da ita Basu direta ko inaba sai Kan makeke hadadden gado Dan kasar waje suka direta...

"Masha Allahu" shine kawai abinda kawar ummu ke Fadi "tubar kallah Fatima lallai kinzo duniya a saa Domin samin irin wanan daular sai Wanda Allah ya zaba,saboda haka ki Zama Mai biyayya Kuma ki rike Miji Allah ya bada zaman lafiya"...

Nan sukaita Mata nasiha Mai ratsa zuciya sanan ummu sukai sallama ta bi bayan kawartata suka fice.....

Bayi biyu ne ke cikin dakin Fatima ko wacce na tsaye gefe da gefe yayinda wasu ke kasa a parlornta mutum hudu Wanda dik nata ne...su zasu rinka kulawa da ita,

**********
Sai magriba aka tashi walima inda tawagar jamaa sukayi caaaa a hanyar gidan amarya wadanda sukayo wa deejahmah rakiya da kawayenta da baki wadanda suka zo biki....

Jamaa kowa sai sambarka yakeyi da wanan makeken gida Wanda yasha kayan more rayuwar duniya,

Dayan part din aka nufa da deejahmah inda sukai meta rakiya har cikin bedroom itama aka ajiyeta,..too fa Nan kawayen amarya su Sunita Suka shiga kashe selfie a bedroom din deejahmah saboda tsabar haduwarsa ....

Dai dai kunnenta hajiya babba ta rada Mata "ki kwantar da hankalinki karki nuna Masa komi Domin dakinki zai Soma zuwa tunda ke aka fara kawowa Kinga kece uwar gida sai yayi Miki kwana bakwai sanan zai koma sashenta lokacin kin mantar dashi wata halitta"....

Deejahmah ta jinjina Kai batare da tace komiba,haka suka Gama surutansu sukai Mata sallama harda Yan matan amarya wadanda dama Ahmad ya sallamensu da makudan kudi tun a wajen walima,,,,,

Sakkowa kasa hajiya babba keyi cike da Isa da mulki kawai tai Karo da bayi wadanda suna ganinta suka zube ...tabisu da kallon tuhuma Tana kallonsu daya bayan daya "ku Kuma daga Ina"

A tare suka hada baki wajen Bata amsa "mune maaikatan sarauniya Fatima wadda aka kawo Nan dazun kafin maraice".....dibbbb network din Kan hajiya babba ya dauke saita juya da sauri zuwa dayar matakalar ta shiga takawa sauri da sauri har ta shige ciki ta nufi kofar da take hangen hasken lantarki tasa hannu ta tura kofar daki,

Fatima wadda ke zaune Kan dadduma ta idar da sallah ta dago Kai da sauri,ganin ko wacece yasata sauke lallausan murmushi hade da mikewa ta nade daddumar Tana fadin "Bismillah ranki ya dade,ai ya kamata kishigo kiga yadda Allah yayi da Yar shegiya Yar kwararo"...tai maganar fuskarta dauke da murmushi,

"Bismillah ga waje Kun kawo amaryata ne?"ta jefa Mata tambaya dikda zuciyarta na tsananin bugawa....

Kallon takaici hajiya babba keyi Mata "yarinya kinyi kuskuren shigowa hurumin da ba naki ba a guje zakibar gidan Nan da kafafuwanki,idan baki fita da hankali ba Zaki fita da tsananin hauka"

"Kinyi babban kuskure hajiya wajen bani damar shigowa gidan Nan Domin kafin infita sai shegiya ta tabbatar da ta Haifa muku jikokin shegu Domin tabar muku tarihi Wanda bazaku taba mantawa ba"

Idanuwa kawai hajiya babba kebin Fatima dashi wadda take jifanta da mugayen kalamai a cikin hikima...."lallai kin dakko ruwan dafa kanki tunda daga kawoki ko cikakkun awanni goma bakiyiba kinfara Zama tantiriyar Mara kunya"

Yar dariya Fatima tayi ta dago Kai Ido cikin idon take kallon hajiya babba "hajiya dama bakisan dik Dan kwararo bashida kunya ba sai yau?....dik azabar da kikaimun dik a tunaninki biyayyr da nayi Miki tsoro ne yasa nayi Miki su?nayi Miki ne kawai don kedin uwargijiyata ce a wanan lokacin,sanan jira nakeyi insamu damar da Nima zanci nawa duniyar Domin kaf dinku saina baku mamaki,nayi matukar farin ciki da ya kasance ke da kanki kika Tako inda nake har nasamu damar amayar da abinda ke cikina a cikin sauki.... alhamdulillah Allah ya cika mun burina na Zama matar kabiru sanan wani abin farin ciki ma uwargida a wajensa wanan ne ya bani damar Zama sarauniyar sarki Mai jiran gado.....hajiya Dan Allah ga hanya Nan mijina na gab da shigowa"....Fatima ta nuna Mata hanyar Kofa Tana murmushi....

Kalaman Fatima kawai keyi mata yawo akai tamkar a mafarki.....kallon Dan bakin Fatima kawai takeyi yadda take zaro maganganu tamkar Tana jiranta.....batasan lokacin da gumi ya jikata ba sharkaf.....a tarihin rayuwarta Babu Wanda ya taba tararta ga da ga ya mayar Mata da martanin maganganu marasa dadiba Koda kishiyarta ce balle Fatima dake matsayin surukarta.....

Jinjina Kai kawai tayi ta nuna Fatima "lallai kin Kira ruwa bakida laima kinzama kiyashi Mai jawo abinda yafi karfinsa.....lallai kin nunamin ke din cikakkiyar Yar bariki ce Amma da sannu zanyi maganinki Zaki hada kayanki da kanki ki koma gidan marayu...idan nayi Miki me sauki kenan idan baki fita gidan Nan da hauka ba"

"Yan rakiyarku suna jiranki hajiya"....

A fusace ta fice a dakin Fatima ta bita da malalacin murmushi hade da dafa kirjinta ta furta a Fili "banso na Miki hakan ba tun yanzun Amma gara in shayar dake mamaki ki kwana kina tunanina"...

Runtse idanuwanta tayi tana sauke numfashi a hankalinki a hankali harta samu natsuwa a zuciyarta.....

Jikinsa a sanyaye ya shigo gidan,direct side din dake facing dinsa ya nufa....Wanda shine na Fatima...

Babu kowa a parlorn kafa ta dauke haka ya nufi hanyar matakala Yana takawa a hankali a hankali har ya Haye sama....

A hankali ya tura kofar dakin bakinsa dauke da sallama...ya maida dakin ya rufe,

Tsaye yayi gabansa na faduwa Yana tunanin wacece a side din da akace Nan zai shiga ya kwana?....kallo yake binta dashi tun daga kasa har sama inda ya sauke idonsa Akan fuskarta dake sunkuye.....ya kafeta da idanuwansa wadanda yake Kara budesu Yana kallonta saboda gani yakeyi tamkar gizo take yi mishi ita dince kuwa?....ya Kare Mata kallo sanan ya tako a sanyaye ya karaso har inda take ya zauna a gefen gado....zuciyarsa ce ta tsananta bugawa Amma hakan be hanasa Kiran sunanta ba a sanyaye "bintu"...shine abinda ya furta a hankali....

"Allah ya cikamun burina na mallakeki a matsayin matar aurena"...besan lokacin da hawayen farin ciki suka Soma gudu a idanuwansa ba....

Ya matso daf da ita ya dago kanta ya kura Mata ido,....ita kuwa Fatima idonta a rufe suke sai zuciyarta dakeyi Mata lugude....

"Ki bude idanuwanki ki kalleni bintu yau na Zama mallakinki kema kin Zama mallakina....dare da Rana banida burin da ya wuce hakan,kullum adduata shine Allah ya cikamun burina na karshe shine aurenki,sai Allah ya dubi kyakkyawar niyyata ya mallakamin ke cikin sauki....hawayen Dadi ke diga a idonsa suna sauka a fuskarta...itama su ta shigayi suna gudu a fuskarta kawai yasa hannu ya shiga share Mata su Amma tamkar karuwa suke.....tausayinta da soyayyarta suka shiga yawo a jinin jikinsa,...ntake jikinsa ya hau rawa ta rungumeta tsammm a jikinsa da karfin gaske.....

********

Kaiwa da komowa kawai hajiya babba keyi a cikin bedroom dinta Tana tunani kala kala....kalaman Fatima kawai ke yawo a kunnuwanta sunayi Mata amsa kuwwa....."tabbas kinyi kuskure Fatima Wanda bazaki tabayin irinsa ba a rayuwa.....lallai kin dakkowa kanki dala Babu gammo Amma nidake zamuga Wanda zaici riba.....sainayi sanadiyyar zamanki a gidan yari na harabada....

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

40
Chapter 59 · 0% Book details