Sashe 79
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfin Hali Fatima tayi ta dago kanta daga jikinta ta bude baki dakyar tace"mahhh"....girgiza Mata Kai zuhra tayi "umminki ce ni Fatima ga mahaifiyarki Nan zahrau"ta nuna Mata inda zahrau ke zaune ta sunkuyar da Kai hawaye na diga....
A hankali ta juya ta dubi mahaifiyarta...a hankali ta Shiga takawa har gaban mahaifiyarta ta ta dire Jakarta kasa tasa hannu ta cire gyalen dake kanta ta jefar ta tsugunna ta dafa kafafuwanta"maamah.."....kuka yaci karfin zahrau Koda ta dago suka hada Ido da yarta numfashinta ne ya tafi saboda tsananin yadda taga kamaninta da Yar Tata.....mikewa tayi tsaye bakinta na rawa...ta ambaci "bintu"....
Cikin shasshekar kuka Fatima ta amsa da "naam"....
Kawai numfashinta ne ya tafi ta Fadi.. da sauri zuhra ta rukota jikinta Tana kuka,
Halima ce ta shigo daga waje taga halin da suke ciki itama tayi joining wajen kukan farin ciki....
*********
Bayan komi ya Lafa zahrau ta farfado daga suman da tayi hannunta na cikin na Fatima take bin diyar Tata da kallo yadda Tai masifar Kama da ita Babu abinda ya Rana kamanninsu sai shekaru dikda itama zahraun Bata tsufaba tunda Bata wuce 37 ba lokacin....
Yarima na zaune a gefe Fatima ta kallesa suka hada Ido ta sakar Masa murmushi wani soyayyar mijinta ne ya lullubeta Wanda Bata tabajin irinsa ba,Anya akwai mazaje irin kabiru kuwa?tabbas ya cika Dan halak tunda ya cika Mata alkawarin da yayi Mata na sama Mata farin ciki har karshen rayuwarta....
Memakon ya maida Mata da murmushi sai ya harareta...turo Masa baki tayi Sarai ta fahimci fushi ya dauka da ita Dole ma ta lallashi mijinta Domin yarima ya Gama Mata komiba a rayuwarta....
*Muje xuwa*
SLIMZY❤
[9/9, 19:57] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
50
A Daren ranan yarima ya sanarwa da Mai martaba samun mahaifiyar Fatima Wanda yayi tsananin farin ciki da Jin hakan....Nan da Nan yasa aka sanar da akwai kwarya kwaryar liyafa washe gari ta taryar mahaifiyar Fatima zuwa masarautar barayar Zaki Kuma matar tsohon sarki Marigayi....
********
Washe gari yarima ya sanarwa da deejahmah samun mahaifiyar Fatima....saboda tsananin farin ciki har kuka tayi na Taya Fatima samun mahaifiyarta dikda Fatima a gidan kakaninta ya barota Dan zasu taho dasu zuwa masarauta...
Duban deejahmah yayi ya shafa kanta saboda tsananin tausayinta da yakeji yadda lokaci daya ta canja daga yadda take dik jikinta ya mutu tayi wani sanyi...
"Ki shirya dakyau kiyi Shiga ta alfarma saboda Mai martaba yace zaayi biki ne sosai na taryar mahaifiyar Fatima"
Kashe Masa Ido tayi hade da lallausan murmushi "yadda kace haka zaayi ranka ya dade"...rungumeta yayi Yana jujjuyata a sama Tana kyalkyala dariya...
********
Wasu tsadaddun Kaya ummu tabawa bilkisu ta Sanya masu shegen kyau tayi kwalliyarta ta alfarma tamkar ba ita ba dik inda ta gifta ummu sai ta kalleta tausayin yarinyar takeji yadda take rayuwa Babu iyaye Kuma Bata damu ba tasawa zuciyarta hakuri da dangana...
"Bilkisu Niko idan bazaki damuba zanyi Miki wata Yar tambaya"ummu taiwa bilkisu maganar cike da kulawa,
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta kasa Tana Wasa da Yan yatsunta,
"Shekaran jiya na ganku keda Dana Ahmad a jikin mota yadda kuke magana sai Naga tamkar akwai wata alaka a tsakaninku kedashi"
Murmushi kawai bilkisu takeyi batare da tace komiba,....ummu ma Yar dariya tayi "to kodai tuwona Mai na zaayi ne keda Dan nawa?Dan gaskiya Kun matukar dacewa da juna"
Mikewa bilkisu tayi tsulum batare da tacewa ummu komiba ta shige tsohon dakin Fatima na da,....
********
Da yareema da deejahmah suka tafi gidan kakannin Fatima,
Deejahmah Tasha mamakin ganin yadda suka tarbeta hannu biyu biyu tamkar Yar da suka Haifa haka mahaifiyar Fatima ta rungume deejahmah a jikinta,
Fuskar Fatima dauke da murmushi take duban deejahmah dik yadda ta sauya tamkar ba itaba da abin mamaki yake Bata da Bata yarda da deejahmah ba dik tunaninta kissa ce kawai takeso tayi Mata Amma yadda taga deejahmah na shisshigowa lamarin nata yasa ta Dan saki jiki da ita,
Wani irin kallo Mai cike da shauki da tsananin soyayya yarima ke jifan Fatima dashi ya kasa dauke idanuwansa daga gareta ya rasa dalilin da yasa Fatima ta Shiga ransa fiye da kowa a rayuwarsa....ga wani sabon sonta da yake ji a dik jijiyoyim jikinsa musamman yanzun da take dauke da gudan jininsa a jikinsa....
Wucesa tazo yi ya ruko hannunta Yana murzawa hade da sauke ajiyar zuciya Yana Shirin janyota jikinsa deejahmah tayi Dan gyaran murya "malam ka Bari dai kuje gida tukunna ni banaso kasa Yar uwata Jin kunya....Dan yanzun da zarar aka shigo aka ganta a jikinka Kai ba kunyar da zakaji itace zataji kunya"...Tai maganar cike da zolaya....
Turo baki Fatima tayi cike da shagwaba ta dubi Deejama "kina ganin ko tausayina bayaji so yakeyi yamun mugunta ma"
"Yi hakuri rabu dashi zamu Rama Bari muje gida yau ai a gidanmu zamu kwana koh?injidai Zaki bimu"
Gyada Mata Kai Fatima tayi tana murmushi,
Kallonsu yakeyi cike da shaawarsu lokaci daya ya tsunci kansa cikin tsananin farin ciki....
Motoci ne nagani na fada aka shirya zuwa gidan Mai martaba wadanda kaf dangin Fatima da mahaifiyarta zahrau suka hallara Dan zuwa gidan sarki kowa cike yake da tsananin farin ciki Mara misaltuwa....
*******
Fada ta cika tayi dankam dangi na kusa Dana waje kowa ya hallara sai Sam barka akeyi da zuwan zahrau masarautar barayar Zaki kusan kowa da yake wajen cike yake da farin ciki Banda hajiya babba wadda fuskarta kadai zaka duba kasan Tana cikin tsananin tashin hankali Mara misaltuwa....ita kuwa rahina gabaki daya yanayinta ya nuna tayi give up hukunci kawai take jira...
Shiru kowa yayi lokacin da Mai martaba yayi gyaran murya...
"Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah daya nuna Mana wanan Rana Mai cike da tarihi....ranace wadda bazamu taba mantawa da itaba a rayuwarmu kasantuwar dawowar iyalan Dan uwana sarki abdallah na biyu a masarautar barayar Zaki Marigayi....hakika lokacin da ya shude abubuwa da dama na bakin ciki sun samemu misali kamar batar matar Dan uwana da ciki Sanan kuma mutuwarsa shi Dan uwan nawa a karshe Kuma rasa Dana babba habibu da mukayi mun tsunci kanmu a cikin damuwa sai gashi Allah ya kawo Mana waraka ta sanadiyyar mutuwar habibu daya kasance Yar uwarsa ce tayi sanadiyyarsa bada son ranta ba Allah ya jikansu da rahma"
Fada ta hada baki da "ameeen"
"Abu na gaba shine lokaci yayi da ya Dace indauki mulki in mikawa masushi Amma saidai hakan bazaiyuwuba sanadiyyar abinda sarki abdallah ya Haifa din macece saidai zan dauki tamanim cikin dari na mukami a mikawa Yar marigayi wato fatima"
Murmushi yarima yayi hade da dubam inda fatima ke zaune gefen deejahmah dukkansu murmushi suka saukewa juna,
Mai martaba ya cigaba da magana"Allah ya nuna min ranan da ya Dace Inyake mummunan hukunci Wanda ya Dace da masu laifi guda biyu a cikin fadar Nan"....
Gaban hajiya babba ya yanke ya fadi Nan da Nan zufa ta Shiga karyo Mata a ta ko Ina a sassan jikinta,
"Safiya kinbani mamaki ,ban taba tunanin kedin azzaluma bace Saida wanan lamari ya faru,Ashe ba tsakani da Allah kike zaune Dani ba...kina zaune danine saboda mulki da dukiya Wanda hakan ya tabbatar mun da dik ranan da na rasasu Zaki guje ni,to tunkafin hakan ya faru Ina Mai tabbatar Miki da na tanadar Miki hukunci me tsanani daga ke kuwa har Yar uwata rahina....
"Hukuncin Dana yanke Miki kuwa shine na sauwake Miki igiyar aurena guda daya.....Sanan na yanke Miki hukuncin xama a kurkukun masarautar Nan na shekara biyar sakamakon yunkurin kisan Kai da kikayi"....
Murmushi Fatima tayi lokaci daya ta dago kanta ta dubi hajiya babba idanuwansu suka hadu da juna ta sauke Mata kayataccen murmushi hade da kafeta da idanuwa.....
"Ke Kuma rahina ba wani hukunci zan yanke mikiba face na yanke dik wata alaka Taki da cikin masarautar Nan na tsameki a cikin Yan uwana har zuwa lokacin da Zaki shiryu ki tsarkake zuciyarki Sanan gidan da nabaku kuke xaune keda mijinki na dauki mukamin galadiman gari gabaki daya na kwace su daka hannunku zan mikasu ga sarkin fada a bisa namijin kokarin dayayi wajen nemawa Fatima diyata farin cikinta"
Sunkuyar da kanta Deejahmah tayi kwalla cike da idanuwanta Jin hukuncin da Mai martaba ya yakewa iyayenta....
Hannu Fatima tasa ta ruko hannun deejahmah lokaci daya ta dago kanta suka hada idanuwa,take tausayin deejahmah ya lullube Fatima Wanda hakan yasata girgiza Mata Kai alamar kada tayi kuka.....
Kuka sosai hajiya rahina takeyi me cike da danasani Wanda Bata taba tunanin zata wayi gari ta tsunci kanta a kaskantacciyar rayuwa ba,...Rana daya dik abinda take takama dashi an kwaceshi daga gareta sakamakon son zuciya da rudim shedan da tabi na zugar hajiya babba gashi ta kaita ta baro....
Itadai zahrau tunda ta sunkuyar da kanta Bata dago ba saboda kwata kwata Bata taba tunanin saboda ita Mai martaba zai iya sakin uwargidansa ba a dalilin mugun aikin da tayi na yunkurin kisan Kai....
"Fatima Allah yayi Miki albarka keda abokiyar zamanki Allah ya hada kawunanku ku zauna lafiya kunji?"
Jinjina Kai Fatima tayi "ameen ranka ya dade Ina godiya"
"Ina neman wata alfarma guda daya ranka ya dade"
Fada tayi tsit kowa na kallon Fatima yayinda zuciyoyin wasu daga ciki suka Shiga tsananin rudani...
"Bakida alfarma a masarautar barayar Zaki Fatima saboda sarautar dungurungum Taki ce da badan xuwanki a matsayin mace ba da yau sarki zaiyi mirabus ya Mika Miki sarautarki Dan haka kome kikeso umarni kawai Zaki bada ayi Miki shi"
Murmushin Jin Dadi Fatima tayi "akwai Yan uwana guda biyu a cikin gidan Nan Maryam da bilkisu wadanda suka kasance marayu babu uwa Babu uba suna Nan suna bauta inaso Mai martaba ya yantasu daga bayi zuwa cikakkun ya'ya ranka ya dade"
"Kinada damar da Zaki yanta ko wani bawa daga cikin gidan Nan Fatima Dan haka bilkisu da Maryam sun yantu Sanan nayi alkawarin rikesu a matsayin Yaya harabada"....
Wani irin farin cikine ya lullube Fatima Wanda Saida hawaye ya sakko daga idanuwanta....abinda Bata taba tunanin samuba ko a mafarki yau gashi itace a daular mulki sarautar gabaki daya tatace Dik ta sanadiyyar yarimanta kabiru Wanda ya zame Mata kyautar Allah....